Aminiya:
2025-06-21@10:39:12 GMT

Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi daraja a Isra’ila

Published: 21st, June 2025 GMT

Iran ta lalata cibiyar binciken kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila, wato cibiyar kimiyya ta Weizmann Institute of Science da ke birnin Tel Aviv.

Cibiyar, wadda ke da alaƙa da binciken harkokin sojin Isra’ila, ta sanar da cewa harin da Iran ta kawo ɗin ya yi sanadiyar ɓarnar da ta kai kimanin Dala miliyan 500.

Makaman Iran sun lalata gine-gine da dama a cibiyar, lamarin da ya sanya masu bincike faɗi-tashi don ceto samfurin bincike a cikin ɓaraguzan gini, a yayin da gobarar ke ci.

Wani makami mai linzami ya tarwatsa wani gini mai ɗauke da ɗakunan gwaje-gwaje na zamani da dama, a yayin harin na ramuwar gayya, bayan da Isra’ila ta kashe masana kimiyyar nukiliya na Iran.

Makamin ya faɗo kan cibiyar ne kafin wayewar garin ranar Lahadi, amma babu wanda ya ji rauni domin cibiyar ba kowa a cikinta a lokacin.

Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ziyarci wurin, inda ya ce, “wannan harin ne dalilin da ya sa Isra’ila ba za a taɓa barin Iran ta mallaki makaman nukiliya ba.”

Idan ba a manta ba, Isra’ila ce ta fara kai hari kan Iran a ranar 13 ga Yuni, bisa hujjar cewa abokiyar gabar tata tana dab da ƙera makaman nukiliya.

Iran, wadda ta dage cewa shirin nukiliyarta don dalilai na zaman lafiya ne kawai, ta mayar da martani da hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa a kan Isra’ila.

Hare-haren Isra’ila sun yi sanadiyar mutuwar wasu manyan masana kimiyyar nukiliya na Iran, da manyan shugabannin sojojin Iran, da fararen hula tare da lalata gidaje da tashoshin nukiliya da ababen more rayuwa.

Duk da cewa yawancin binciken cibiyar Weizmann sun danganci fannin gas magunguna da ilimin kimiyya ne, amma tana kuma da alaka da tsaro.

A watan Oktoba na 2024, ta sanar da haɗin gwiwa da babban kamfanin tsaro na Isra’ila, Elbit, kan “kayayyakin da aka samo daga halittu don aikace-aikacen tsaro.”

Cibiyar binciken kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila, tana da ƙungiyoyin bincike 286, masana kimiyya ma’aikata 191, da daruruwan dalibai.

Iran ta sanar a ranar Juma’a cewa ba za ta tattauna makomar shirin nukiliyarta ba yayin da take fama da hare-hare daga Isra’ila.

Duk ƙoƙarin ƙasashen Turai na jan hankalin Tehran zuwa tattaunawa bai nuna alamun nasara ba.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Iran Isra ila nukiliya

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisa Na Binciken Yadda Aka Kashe Naira Tiriliyan 1.12 Na Tallafin Manoma

Sanarwar ta ce: “Ma’aikatar Harkokin Waje na sanar da jama’a cewa, sakamakon rikicin da ke kara kamari tsakanin Isra’ila da Iran, Gwamnatin Tarayya tana shirin karshe na kwaso ‘yan Nijeriya da suka maƙale a wadannan kasashe.

“Saboda haka, ana shawartar dukkanin ‘yan Nijeriya da abin ya shafa da su kiyaye matakan tsaro da kuma tuntubar ofishin jakadanci mafi kusa domin yin rijista da samun karin umarni.”

Baya ga haka, Gwamnatin Tarayya ta sake kira da a dakatar da fada tsakanin Isra’ila da Iran, tare da bukatar bangarorin su rungumi tattaunawa, su mutunta dokokin kare hakkin dan Adam na duniya, kuma su bai wa rayuwar fararen hula muhimmanci.

Ma’aikatar ta jaddada cewa Nijeriya na goyon bayan hanyoyin warware rikici ta hanyar lumana da kuma tallafa wa zaman lafiya a yankuna da duniya baki daya.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila
  • Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila
  • Iran Ta Bayyana Sharaɗin Sasantawa Da Isra’ila – Ministan Harkokin Waje
  • Majalisa Na Binciken Yadda Aka Kashe Naira Tiriliyan 1.12 Na Tallafin Manoma
  • Za mu iya galaba kan Iran ko babu Amurka — Isra’ila
  • Nan da mako biyu za mu yanke shawara kan shigar wa Isra’ila yaƙi — Trump
  • An Kashe ‘Yan Ta’adda 6,260, An Ceto Mutane 5,365 Acikin Shekaru Biyu – Hedikwatar Tsaro 
  • Gwamnonin APC Sun Nemi Tinubu Ya Ƙirkiri ‘Yansandan Jihohi Don Yaƙar Matsalar Tsaro
  • Kar a kuskura a shiga cikin yaƙin Iran da Isra’ila — MDD