Aminiya:
2025-09-24@11:15:59 GMT

An kashe uban ango da ɗan uwansa a harin Filato

Published: 21st, June 2025 GMT

Mahaifin ango da ƙanin ango na daga cikin mutanen da aka kashe lokacin da wasu suka kai musu hari a Jihar Filato.

Rahotanni sun nuna cewa mutum 31 ne ke cikin wata babbar mota mai ɗaukar fasinja 18 daga Jami’ar Ahmadu Bello Zariya (ABU), yayin da aka kai musu hari.

Ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum 10 da bam a Borno An yi wa ma’aikatan ƙananan hukumomin Gombe ƙarin albashin N5,000

Mutanen sun fito ne daga unguwar Basawa da ke Ƙaramar Hukumar Zariya a Jihar Kaduna, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa garin Pau da ke Jihar Filato domin ɗaurin aure.

Mutum 12 sun rasu a sakamakon harin, yayin da 19 suka jikkata kuma ana kula da su a Asibitin Gwamnati na Mangu.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira, Ibrahim Umar, ya ce: “Mahaifi da ƙanin ango duk sun rasu a harin.

“Angon daga Zariya yake, amma yana aiki a matsayin malami a wata makaranta a yankin. A nan ne ya haɗu da matar da zai aura.

“Muna ɗauke da goro da sauran kayayyakin da ake kai wa wajen aure. Mun shaida wa waɗanda suka tare mu cewa ba ‘yan yankin ba ne, kuma mu ba ma faɗa, sai dai ba su saurare mu ba,” in ji shi.

Ya yaba da yadda sojojin da ke kusa da wajen suka kai musu ɗauki.

“Sojojin sun taimaka mana sosai. Da ba su zo ba, da abin ya fi haka muni,” in ji shi.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Ɗan Uwan Ango Ɗaurin Aure hari Matafiya

এছাড়াও পড়ুন:

Mahara sun kashe ’yan sanda a shingen bincike a Kogi

’Yan bindiga sun kai hari shingen bincike na ’yan sanda a Jihar Kogi, inda suka kashe jami’ai da wani mutum.

Harin farko ya faru da misalin ƙarfe 10:30 na safe a ƙauyen Abugi da ke Ƙaramar Hukumar Lokoja.

Mata 400 sun amfana da kayan haihuwa a Gombe Bayan biyan N50m an sako ma’aurata da ’yarsu su da aka sace a Katsina

Maharan, sun kai harin ne a kan babur, inda suka buɗe wa ’yan sandan da ke bakin aiki wuce.

Wani matashi da ya zo wucewa ta wajen ya rasa ransa.

Bayan haka, maharan sun kwashe bindigogin jami’an sannan suka tsere.

Daga baya, da misalin ƙarfe 11 na safe, suka sake kai wani hari a shingen da ke kan hanyar Ilafin, Isanlu a Ƙaramar Hukumar Yagba ta Gabas, inda suka kashe wasu ’yan sanda biyu na rundunar MOPOL 70.

Mutanen yankin sun ce wannan hari ya jefa su cikin tsoro, suna ganin cewa maharan na neman bindigogi ne domin su ci gaba da kai hare-hare.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Yagba ta Gabas, Dokta Joshua Dare, ya yi Allah-wadai da hare-haren.

Ya bayyana harin a matsayin barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.

Ba wannan ne karo na farko da irin wannan hari ya auku ba.

A ranar 9 ga watan Satumba, an kashe jami’an tsaro guda biyar; ciki har da ’yan sanda uku da ’yan banga biyu, a wani hari  kwanton ɓauna da aka kai musu a yankin Egbe da ke Ƙaramar Hukumar Yagba ta Yamma.

Gwamnatin Jihar Kogi, a baya-bayan nan ta zargi wasu matasa da taimaka wa ’yan bindiga a yankin, inda ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauke su a matsayin ’yan ta’adda.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP William Aya, bai ce komai game da sabon harin ba, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Jihar Kogi Na Cikin Fargaba Yayin Da Kogin Neja Da Benuwe Suka Tumfatsa
  • Sojoji Sun Daƙile Hare-haren ISWAP, Sun Bai Wa Magidanta 10,000 Kariya A Borno
  • Mahara sun kashe ɗan sanda, sun ɗauke bindigarsa a Taraba
  • An yi garkuwa da ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato
  • ‘Yan Bindiga Sun Sace Ɗan Majalisar Dokokin Jihar Filato
  • DSS ta yi wa Malami tambayoyi kan harin da aka kai masa a Kebbi
  • Jariri ya mutu a bayan uwarsa yayin tsere wa ’yan bindiga a Neja
  • Hisbah ta kama masu safarar mata zuwa Saudiyya a Kano
  • Karin ƙananan hukumomi 2 sun yi sulhu da ’yan bindiga a Katsina
  • Mahara sun kashe ’yan sanda a shingen bincike a Kogi