An Fara Kiraye-Kirayen Tinubu Ya Zaɓi Barau Jibrin A Mataimakinsa Na 2027
Published: 24th, June 2025 GMT
2. Haɗin kai da shugabanni daga ko’ina
3. Rashin ta’asar da ya yi wa kowa
Bayannan ƙuri’un INEC na 2023 daga jihohin Arewa maso Gabas sun nuna cewa Atiku Abubakar ya samu ƙuri’u fiye da Tinubu a dukkan jihohin yankin.
Ƙungiyar ta kammala da cewa: “Lokaci ya yi da Shugaba Tinubu ya kamata ya yi la’akari da wannan batu yayin shirye-shiryen zaɓen 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Barau
এছাড়াও পড়ুন:
CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AI
Hukumar da ke kula da yi wa Kamfanoni Rajista ta Najeriya (CAC) ta ƙaddamar da sabon shafin intanet mai amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira wato AI domin sauƙaƙa rajistar harkokin kasuwanci da kamfanoni a Najeriya.
Shugaban Hukumar, Hussaini Ishaq Magaji (SAN), ne ya bayyana a yayin taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a Kano ranar Litinin.
Dalilin da muke goyon bayan tsare-tsaren Tinubu na karɓo bashi — Majalisar Wakilai Sarkin Ruman Katsina ya rasuYa kuma ce hukumar ta kawo sabbin sauye-sauye da za su inganta ayyukanta da kuma sauƙaƙa wa ’yan kasuwa yin rajista da ita.
Magaji ya ce, “Ko ina kake, daga dakinka, ba tare da ka san kowa a CAC ba, kuma ba tare da biyan kowa komai ba, za ka iya yin rajistar sunan kasuwancinka ka samu takardar shaidarka cikin ƙasa da minti 10.”
“Adadin bayanan da shafinmu na intanet ke ɗauka ya tashi daga 3.5TB zuwa kusan 12TB cikin watanni uku da fara jagorancin hukumar,” in ji shi.
Shugaban ya kuma ce hukumar na karɓar saƙon imel sama da 3,000 a kullum, yayin da ma’aikata ƙasa da 100 ke kula da su da kuma bayar da amsa.
Sai dai ya ce sabon shafin da aka ƙaddamar, zai karanta kuma ya rarraba tare da bayar da amsa ga dubban sakonnin na imel cikin daƙiƙa daya.
Ya kuma ce karfin aikin shafin wanda aka fara amfani da shi a watan Yuni ba shi da iyaka.
Hussaini ya ce, “Babu inda a duniya ake yin rajistar sunan kasuwanci cikin ƙasa da minti 10. Mu ne muka fara, sauran su biyo baya.
“A yau kaɗai, akwai aƙalla kamfanoni 7,000 da ke buƙatar a yi musu rijista, yayin da ma’aikata 63 ne kawai ke aikin. Wannan ne ya sa dole mu fara amfani da wannan fasahar domin inganta ayyukanmu,” in ji shi.
Ana sa ran shugaban hukumar zai gabatar da jawabi kan nasarorin da hukumar ta samu a fasahar a yayin taron hukumomin da ke kula da yi wa kamfanoni rajista na duniya da za a yi a ƙasar Tunisia wata mai zuwa.