Firaministan Singapore: Jama’ar Sin Suna Da Kwarewar Kirkire-Kirkiren Fasahohi
Published: 22nd, June 2025 GMT
Firaministan kasar Singapore, Lawrence Wong, ya yi hira da wata wakiliyar CMG a kwanan baya, inda ya ce, yana da cikakken imani kan kasar Sin, saboda jama’ar kasar suna da kwarewar kirkire-kirkiren sabbin fasahohi da hikimar daidaita al’amura. A cewarsa, kokarin neman ci gaban harkoki da jajircewa na al’ummar Sin sun sa shi dakon ganin makomar kasar Sin mai cike da haske.
Wong ya kara da cewa, ya taba cudanya da jami’an gwamnatin kasar Sin na matakai daban daban a shekarun baya, wadanda suka nuna kwarewar aiki da hazaka a fannin fahimtar ayyuka. Ban da haka, Wong ya ce, jami’an kasar Sin suna son sauraron ra’ayoyi na bangarori daban daban, da kokarin neman dabara mafi dacewa wajen daidaita matsala. A cewarsa, nagartaccen tsarin gudanar da mulki ya shafi tantance ayyukan da ake gudanar da su, da koyon sabon ilimi don inganta harkoki a-kai-a-kai, kana dukkan wadannan abubuwa ana iya ganinsu cikin tsarin gudanar da mulki na kasar Sin.
Bayan haka, dangane da matakin karbar karin harajin fito kan kayayyakin sauran kasashe da kasar Amurka take yi, mista Lawrence Wong ya ce, idan Amurka za ta iya nuna sanin ya kamata, da saukin kai wajen duba ma’anar manufar kare moriyar kanta, to, za ta ga damar samun dimbin alfanu na hakika, ta hanyar kasancewa cikin tsarin cinikin duniya da ake amfani da shi yanzu. (Bello Wang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sashen Lafiya Zai Fara Amfani Da Sabuwar Fasahar AI Don Inganta Lafiya
Kwalejin Kiwon Lafiya ta Najeriya ta fara taron shekara-shekara karo na 19 na kimiyya da nufin yin amfani da sabbin fasahohi da kirkire-kirkire wajen kawo sauyi a fannin likitanci a kasar.
Da yake yiwa manema labarai jawabi gabanin taron a Sokoto, shugaban kwalejin na kasa, Dokta Peter Ebeigbe ya ce taron zai tattauna hanyoyin da za a bi domin tunkarar manufofi aiwatarwa mai inganci da shigar da kamfanoni masu zaman kansu a fannin ilimin likitanci na gaba da digiri na biyu.
Gidan Rediyon Najeriya dake Sokoto ya ruwaito cewa, ana sa ran taron zai kuma tattauna kan ingancin aikace-aikacen kirkirariyar fasaha ta Artificial Intelligence (AI) da illolinsa na isar da sahihanci mai inganci.
Shugaban na kasa ya kara da cewa ana sa ran masu hannu da shuni hudu ne zasu jagoranci taron.
Nasir Malali