Fim Babbar Hanya Ce Ta Nishaɗantar Da Al’umma -D Malam Dan Bola (2)
Published: 22nd, June 2025 GMT
Na yi shi kamar ‘series’ amma ba ‘series’ bane, ‘part-part’ ne na yi shi haka ba wani me tsayi bane ba, baya wuce minti uku zuwa biyar ya ma yi tsayi kenan.
Kai ka ke rubuta ‘comedy’ din ko kuwa bayar wa ka ke a rubuta maka?
Ni nake rubuta ‘comedy’ na da kaina, sai dai idan ana hira da abokai ana abun dariya haka da sauransu, sai in dauke shi, shi ma din ko da ban rubuta ba in yi shi akai, mu je mu yi bidiyon shi a duk lokacin da muka samu dama to, gaskiya ba a rubuta mun ‘comedy’ sai dai irin a ba ni ‘idea’ haka.
Ko akwai wani ‘comedy’ da ka taba yi wanda ya janyo maka zagi wajen mutane?
Ban taba bidiyon da ya jawo mun zagi a wajen mutane ba, sai dai kin san duk abin da ka ke dole akwai wanda ba fa burge shi ka ke yi ba, kuma mukan sanya number akan bidiyo haka nan wani zai bushi iska ya kira ka kawai ya kunduma maka zagi, ban sani ba ko shi samun nishadinsa ta nan yake samu, sai dai irin wadannan.
Wane irin nasarori ka samu game da wannan harkar ta comedy?
Nasarar dana samu nake jin dadi, nake alfahari da ita; mutane masoya ina jin dadi idan na ga yadda suke son bidiyoyi na, suke yabawa.
Ko akwai wani kalubale da ka taba fuskanta game da ‘comedy’?
An sami kalubale sosai kwanan nan ma an samu, dake mun dan tafi hutun Dan Bola, sai na ce bari na dauko wani shiri na zo na ci gaba da saka wa kafin in dawo in cigaba da Dan Bola sai na dauko shiri mai suna Ango, muka saka ranar yin aiki muka dauko jarumai, da kyamarori da ‘light-light’ aka je aka fara wannan aiki ana tsaka da aiki kawai dai Aljanun Jarumar da take tsaka da yin aikin ya tashi, ba mu gama aikin ba aikin ya tashi, hankali kowa ya daga, darakta ya dan fara rukiya, a takaice dai sai da muka hakura da wannan aikin, aka kwashe aiki daga ‘computer’ washegari aka zo za a duba ‘sound’ babu kin ga ba aiki kenan, duk wata wahala da muka yi kama daga kan tattara jarumai, abincinsu, kudin sallamarsu, sannan kudin kayan aiki da muka dauko dukka haka muka yi asarar wannan aikin.
Na ji ka yi maganar jarumai, shin kana amfani da jaruman kannywood ne cikin ‘comedy’ ko kuwa Jaruman social media ne wadanda su ma suke baje hajarsu a kananun bidiyo?
Eh, na kan sanya jaruman kannywood a ‘comedy’ na, nayi comedy da Ali Nuhu, Na kowa, Bosho, Daushe.
Wacce hanya ka bi wajen ganin ka samu lokacin Ali Nuhu domin yin ‘comedy’, kuma ta ya ka sanar masa?
Muna da alaka da yallabai, dan shi yallabai maigida na ne a kannywood, saboda yana bibiyar lamura na akan abubuwan da na ke yi tun ma bamu taba haduwa da shi ba ya fara yi min ‘reposting’ a instagram, kuma yakan bani shawarwari idan ya ga ina yin wani abu da wanda bai kamata ba da kuma abun da ya kamata in yi. Allah cikin ikon sa har ya neme ni na je nayi fim din alaka, tun da har ya sa ni a alaka kin ga ai akwai alaka kenan, masha Allahu. Akwai lokacin da Arewa 24 suka gaiyace ni zasu yi interbiew da ni, suna gayyata na ke sanar masa Arewa24 za su yi hira da ni ya ce masha Allah Allah ya taimaka. Lokacin yayi naje su kayi interbiew da ni, bayan sunyi interbiew da ni, sai na kirawo yallabai na gaya masa na zo mun yi hira daArewa24 mun gama, sai nace sir kana office in kawo ziyara? ya ce yana ofis
Idan za ka yi ‘comedy’ kana kashe kudi kamar naira nawa wajen hada aikin?
Ya danganta da yanayin ‘comedy’ din da za ka yi, idan na tashi zan yi aiki bana fita nayi daya ko biyu, na kan rubuta kamar guda goma sai na fita nayi su, to kuma guda goman nan a kalla indai ina so na dan yi shi ‘normal-normal’ zan iya kashe talatin, arba’in haka, tunda kayan aikin na rana daya zan dauka.
A yanzu kana da mutanen da suke karkashinka za su yi kamar guda nawa?
A halin yanzu ban da wanda suke karkashi na sai dai abokaina, wanda tare ake tashi ayi gwagwarmaya.
Su waye abokanan aikin?
Abokanan ‘comedy’ na yawanci mata ne akwai wata yarinya mai suna Salma, akwai wani abokina yana nan shi ma muna fafata bidiyoyin shi Sani Mijin Biza, cikin sabon salon ‘comedy’ karya Da Gaskiya, da dai sauransu.
Wane abu ne ya fi baka wahala wajen yin ‘comedy’ ?
Abin da yake ban wahala shi ne; yarinya da za ka yi ‘comedy’ da ita babu abun a tattare da ita, ko ba ta rike ‘dialogue’ ko tana da saurin dariya, ina shan wahala da wannan abun.
Wane bidiyo ne ya fi burge ka cikin wanda ka yi?
Bidiyon da ya fi burge ni shi ne bidiyon Dan Bola, bidiyo na farko, wanda shi ne ya sa aka fara gani na, wanda na tawo ina tura bola ina cewa; “Za a kwashe bola?” kawai sai na ga budurwa ta, na duke na ce “Kai ina! karya ne ke wallahi Bebi ni ne” ina son wannan ‘comedy’ sosai.
Idan aka ce ka dauki daya ‘comedy’ ko fim wanne za ka dauka?
Fim zan zaba, ai fim baban ‘comedy’ ne, shi ya haifi ‘comedy’, na fara ‘comedy’ ne sakamakon ina son na kai ga fim.
Bayan wannan harkar taka da ka ke yi kana yin wata sana’ar ne?
Eh! Ina yin harkar ‘Gold’ kamar su zoben zinare, da Agogon zinare, sannan kuma da sauran ma’adanai, kamar su; ‘Blackstone’, ‘Tender stone’, da su jigida na ‘gold’ da sauransu.
Mene ne burinka a nan gaba game da bidiyon da ka ke yi da kuma harkar fim?
Burina shi ne na shahara nayi sunan da duk duniya za ta sanni kuma ta yi alfahari da ni, kuma na bada gudunmawa a addini na addinin musulunci
Wacce shawara za ka bawa masu irin sana’arka ta ‘comedy’?
Shawarar da zan ba su su tsaya su lura su yi abu mai kyau, kar su tsaya iya nishadi koyaya ne su rika sanya abu mai ma’ana tare da sako, domin an ce in yau kai ne- gobe ba kai bane, sabida haka a guji sanya kalaman batsa domin hakan ba shi da kyau.
Ko kana da wadanda za ka gaisar?
Ina gaishe da baban ogana wanda nake alfahari da shi a masana’antar kannywood wato Isma’il Maigana, darakto dan shi yake ba ni umarni akan bidiyoyi na, sannan ga abokina abokin gwagwarmaya Sani Mijin Biza, sannan akwai Adam A Beach, kuma akwai abokina wato Shafi’u Nadir Dan So.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Jami’an Alhazai Sun Karrama DG Labbo Bisa Nasarar Hajjin 2025
Jami’an Alhazai na shiyya-shiyya sun karrama Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa Alhaji Ahmed Umar Labbo bisa nasarorin da aka samu a aikin hajjin shekarar 2025.
Shugaban jami’an alhazai na shiyya-shiyya, Alhaji Sale Haruna Kafin Hausa ya tabbatar da hakan a wani kwarya-kwaryan biki da aka gudanar a shelkwatar hukumar dake Dutse Babban Birnin jihar.
Ya ce karrama Ahmed Labbo, na da nasaba da gudunmawar da ya bayar da kuma samun nasarar aikin hajjin bana a gida da kuma kasar Saudi Arabia.
Yace wadannan nasarorin sun sanya hukumar ta samu lambobin yabo da kyautuka da dama a kasa mai tsarki.
Alhaji Sale Haruna Kafin Hausa, yana mai cewar jami’an alhazai na shiyya-shiyya suna alfahari da Alhaji Ahmed Umar Labbo bisa yadda yake kula da su da kuma tafiya da kowa wajen gudanar da aikin hajji.
Da yake maida jawabi, Darakta janar na hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ya yaba ma jami’an bisa wannan karamci da kuma gode musu bisa kokarin su wajen kula da alhazai a aikin hajjin bana.
Shima a nasa tsokacin, Mai bai wa Gwamna Umar Namadi shawara akan aikin hajji, Alhaji Isa Idris Gwaram ya bayyana Alhaji Ahmed Umar Labbo a matsayin Shugaba abun koyi da hukumar alhazai ta jihar take alfahari da shi.
Wakilinmu, ya shaida mana cewar, a yayin bikin an kuma karrama Daraktan kudi da mulki na hukumar, Alhaji Jamilu Ilu Kazaure wanda ya yi ritaya daga aiki.
Usman Mohammed Zaria