Wakilin Sin Ya Yi Kira A Yayyafa Ruwa Ga Rikicin Isra’ila Da Iran
Published: 21st, June 2025 GMT
Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD ya yi kiran hada karfi da karfe a bangaren kasa da kasa don karfafa tattaunawa domin ganin an yayyafa ruwa ga rikicin Isra’ila da Iran.
Wakilin, Fu Cong ya ce, yayin da rikicin yake-yaken sojoji na Isra’ila da Iran ya shiga kwana na takwas, abin bakin ciki ne ganin yadda lamarin yake janyo asarar rayukan fararen hula da dama tare da lalata kayayyakin aiki a dukkan bangarorin biyu.
Ya kara da cewa, idan har wutar rikicin ta ci gaba da ruruwa, ba kawai bangarorin biyu ne za su tafka babbar asara ba, hatta sauran kasashen yankin lamarin zai yi musu mummunar illa.
Fu Cong, ya fada wa wani taron gaggawa na kwamitin sulhun MDD cewa, matakin da Isra’ila ta dauka ya saba wa dokokin duniya da ka’idojin huldar kasa da kasa, yana kuma kawo cikas ga ‘yancin kai da tsaron kasar Iran, tare da yin kafar ungulu ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Kuma ba tare da wata shakka ba, kasar Sin ta yi Allah wadai da hakan. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ya Ce: Maso Goyon Bayan Isra’ila Suna Da Hannu A Laifukanta
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Gwamnatin mamayar Isra’ila na aikata kisan kiyashi a Gaza, kuma magoya bayanta suna da hannu a ciki
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Rahoton kwamitin binciken gaskiya na Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da cewa, laifukan da haramtacciyar kasar Isra’ila ta aikata a Gaza sun kai na “kisan kare dangi”, inda ya yi kira ga masu kare gwamnatin ta Isra’ila da su daina shiga da hada baki wajen aikata wadannan laifuka kan al’ummar Falastinu.
Baqa’i ya bayyana cewa: Kwamitin bincike mai zaman kansa na kwamitin kare hakkin bil’adama na Majalisar Dinkin Duniya kan laifukan da ake aikatawa a Falasdinu da aka mamaye karkashin jagorancin fitacciyar marubuciya Navi Pillay, ba ta da wata shakka game da irin laifukan da kuma irin zaluncin da ake yi a Gaza. Ya yi nuni da cewa, hukumar ta tabbatar a cikin wani bincike na shari’a mai shafuka 72 na gaskiya da alkaluma, cewa haramtacciyar kasar Isra’ila na aikata kisan kiyashi a Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Cika Kwanaki 713 Suna Kisan Kiyashi A Zirin Gaza September 18, 2025 Harin Makami Mai Linzami Yemen Ya Tilastawa Jirgin Fira Ministan Gwamnatin Isra’ila Saukar Gaggawa September 18, 2025 Eslami: Dole ne IAEA ta zama mai cikakken ‘yancin cin gashin kai September 18, 2025 Rahoto: An yi tattaunawa mai tsawo tsakanin Syria da Isra’ila a Landan September 18, 2025 Sheikh Qassem: Harin Pager jarabawa ce wadda ta kara wa masu gwagwarmaya kwarin gwiwa September 18, 2025 Pezeshkian: Iran da Masar suna da tsohon tarihi a duniya September 18, 2025 Iran ta samu Zinariya, Azurfa, da Tagulla a Gasar Kokawa ta Duniya September 18, 2025 Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam Da Zai Samar Da “Internet” Ga Yankunan Karkara September 17, 2025 Za A Kada Kuri’ar Raba Gardama Akan Sabon Tsarin Mulki A Kasar Guinea September 17, 2025 Larijani: Iran Da Saudiyya Za Su Bunkasa Aiki Tare A Fagagen Kasuwanci Da Tsaro September 17, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci