An Nemi A Kafa Dokar Ta-ɓaci Kan Masu Ƙwacen Waya
Published: 20th, June 2025 GMT
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS) ce ta bayyana hakan a rahoton ayyukan ta’addanci na watanni 12. Rahoton ya bayyana ayyukan ta’addanci miliyan 51.89 da suka shafi iyalai, satar waya ce mafi yawa a ciki da kaso 13.8 da rahoton satar waya miliyan 25.
Rahoton ya nuna akwai layukan waya da ke aiki a wayoyin hannu miliyan 216.
A yayin da duniya ke kara komawa a duniyar fasaha, wayoyin hannu na yi wa al’umma amfani fiye da sadarwa domin suna amfani a matsayin wajen neman ilimi, kasuwanci, karamin banki da biyan bukatun yau da kullum, kuma hanyar rayuwar al’umma da dama wanda hakan ya sa kwacen waya ya zama abin damuwa.
Nazarin ya nuna, a lokacin NBS ta bayar da rahoton mutane miliyan 17.97 ne suka fada tarkon masu kwacen waya. Daga ciki akwai Dorcas Oluwaseyi wadda aka sace wayar ta a cikin mota. “Sun kwace jaka ta, suka dauki karamar jaka ta, suka dauke waya, da katukan ATM di na.”
A yau bata gari suna farautar wayoyin hannu a al’ummar da kunci da tsadar rayuwa ta yi wa katutu, a yayin da raunanan hukumomin tsaro suka bar ta’addancin na ci gaba da faruwa a kullum.
Hukumomin tsaro a lokuta daban-daban kan bayyana kokarin da suke yi wajen kawar da ta’addancin kwacen waya sai dai al’umma na kukan kokarin jami’an ba wani abin rubutawa ba ne a bisa ga yadda matsalar karuwa take yi maimakon raguwa.
Jihar Kano ce kan gaba a Arewacin Nijeriya inda kwacen waya ya yanke cibi ta yadda barayin ba sani ba sabo suka mayar da ‘ya’ya da yawa marayu, suka mayar da mata zawarawa suka raba dimbin al’umma da mahaifan su, duka a dalilin kwace wayoyin wadanda ba su ji ba ba su gani ba.
Kisan gillar da wani mai kwacen waya ya yi wa matashin jami’in sojin ruwan Nijeriya a Kaduna a kan ya ki aminta ya bashi wayarsa ya kara daga hankalin al’umma a kan girman matsalar wadda har za a iya cakawa soja wuka har lahira.
Sojan Laftanar Kwamanda M. Buba ya tsaya ne a bakin gadar Kawo, Kaduna domin ya yi facin tayar motarsa a inda barawon ya samu sa’a ya caka masa wuka lamarin da duk da jama’a sun kawo dauki sun yi wa barawon kisan gilla, tuni hukumar kwalejin horas da hafsoshin soji da ke Jaji in da sojan ke karbar horo suka kama mutane 27 a maboyar su.
A Gombe matashin magidanci, Ahmad Kasiran ne masu kwacen waya suka raba da duniya a kan wayarsa lamarin ya daga hankalin jama’a tare da girgiza su.
A yayin hada wannan rahoton wakilin mu ya samu rahoton yadda masu kwacen waya suka cakawa wani malamin jami’a wuka a Kano suka bar shi a cikin jini.
Gagarumar matsalar kwacen waya ta ta’azzara ne a dalilin rashin madafa a halin tsadar rayuwa. Rashin aikin yi ya mamaye ko’ina ta yadda jama’a ba su samun ayyukan yi. Hauhawar farashin kaya da karyewar darajar naira ya kara girman wannan matsalar wadda ta jefa miliyoyin ‘yan Nijeriya a cikin fatara da bude kofar ta’addanci da rashin tsaro.
A bisa ga wannan a yau jama’a da dama sun zabi kwacen waya a matsayin hanya mafi sauki ta samun kudi a bisa ga bukatar da ake da ita ta wayoyin da ba sababbi ba.
A haka wasu na ganin mafita ita ce dokar agajin gaggawa, gyaran dokoki, karfafa hanyoyin fasahar bin diddigin gano waya, zartas da hukunci mai tsauri da aiwatar da shiraruwan rage matsalar rashin ayyukan yi.
Inganta dokokin hukumomin tsaro ya zama wajibi kuma hanya ta farko a fafutukar kawar da wannan matsalar. Hobbasar Rundunar ‘Yan Sanda ba mai yawa ba ce domin rahoton hukumar kididdiga ya nuna kashi 90% na wadanda aka yi wa kwacen waya sun kai rahoton faruwar lamarin, amma kashi 11.7% ne kawai aka gano.
A mabambantan ra’ayoyin jama’a da LEADERSHIP Hausa ta tattaro sun bayyana wajibcin gwamnati da musamman hukumomin tsaro da su kaddamar da dokar daukin gaggawa, tare da hukunci mai tsauri kan masu kwacen waya da ke addabar al’umma tun kafin lamarin ya kara tabarbarewar da zai fi karfin hukuma.
“Wajibi ne hukumomin tsaro su kara daura damarar yaki da barayin waya domin matsalar ta wuce duk yadda ake tunani haka ma gwamnatoci su ba da cikakken goyon baya musamman a kafa dokar ta baci domin duk matsalar da ake yi wa jama’a kisan gilla to gagaruma ce haka ma a yaki matsalar shaye- shaye wadda ita sila.” In ji Kallamu Abubakar.
Abba Fadi ya bayyana nasa ra’ayin yana cewar “Inna lillahi wa Inna ilaihi Raji’un. Wannan masifa ni wallahi har na gaji da jin labarin kashe- kashen all’umar Annabi da masu kwacen waya ke yi. A gakiya ya kamata gwamnati ta tashi tsaye a kan lamarin nan tun kafin barayin waya su ci mu da yaki a kasar nan. Idan an kama barayin waya a rika zartar musu da hukuncin kisa a bainar jama’a don ya zama izina ga masu aikatawa.”
A ra’ayin Abdulkadir Aminu ya na ganin domin magance wannan matsalar shine “A dauki matakin kafa dokar ta baci ta hanyar ba- sani ba- sabo a kan barayin waya a kuma tsaurara hukunci ga duk wanda aka kama da kwacen da kuma sayen wayoyin sata.”
Shi kuwa Umar Albashir cewa ya yi “Tabbatar da hukunci ga duk wadanda aka kama da satar waya shine zai magance matsalar da sauran matsalolin da ake fuskanta. Wani babban abin dubawa shine matsalar shaye- shaye ita ce ta haddasa matsalar daba wadda kuma ta haifar da ta’addanci wanda shi kuma ya haifar da sace- sace da kwace- kwace wanda matukar ba a kawar da hanyar shaye-shaye ba to ba a dauki hanyar magance matsalolin ba.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Waya masu kwacen waya hukumomin tsaro
এছাড়াও পড়ুন:
Makon Kiwon Lafiyar Uwa da Ɗa ya Samu Gagarumar Nasara a Karamar Hukumar Gwarzo
Shirin Makon Kiwon Lafiyar Uwa da Ɗa (MNCH) a Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ya samu gagarumar nasara, inda mata da yara da dama suka amfana da ayyukan kiwon lafiya kyauta iri-iri.
Wannan kamfen na mako guda, wanda Gwamnatin Jihar Kano tare da haɗin gwiwar UNICEF da sauran abokan hulɗa suka tallafa masa, na da nufin inganta lafiyar mata da yara tare da rage mace-macen da za a iya kauce wa ta hanyar samar da dama ga ayyukan kiwon lafiya.
Cibiyoyin lafiya a fadin karamar hukumar, ciki har da Asibitin Gwamnati na Gwarzo da Asibitin ‘Yar Kasuwa, sun bayar da rigakafi kyauta, shawarwari kan abinci mai gina jiki, kulawar haihuwa da sauran muhimman ayyuka na kiwon lafiya.
Jami’in Lafiya a matakin farko na karamar hukumar Gwarzo, Alhaji Sulaiman Abdulqadir Karaye, ya bayyana cewa gwamnatin jiha ta tabbatar da samuwar ingantattun magunguna da kayan aiki.
Ya shawarci mata da masu kula da yara su rika amfana da irin waɗannan damar ta hanyar ziyartar cibiyar kiwon lafiya mafi kusa domin samun ayyuka kyauta.
“Gwamnatin Kano ta bai wa fannin kiwon lafiya muhimmanci ta hanyar tallafi na baya-bayan nan da suka haɗa da na’urar sanyaya allurar rigakafi, janareto da sauran kayan aiki masu muhimmanci,” in ji shi.
Shugaban Asibitin ‘Yar Kasuwa kuma wakilin al’umma a Gwarzo, Salisu Ibrahim, ya bayyana jin daɗinsa kan yawan halartar jama’a.
Ya ce mazauna yankin sun fito sosai domin amfana da ayyukan da aka tanada.
A nata jawabin, jami’ar da ke kula da shirye-shiryen MNCH a karamar hukumar, Hajiya Amina Ado, ta bayyana cewa an gudanar da shirin lafiya cikin nasara a manyan cibiyoyin lafiya tare da wadatattun ma’aikata da kayan aiki.
Ta tabbatar da cewa mata da dama sun halarta, kuma ta yabawa haɗin gwiwar da ke tsakanin masu ruwa da tsaki.
Ɗaya daga cikin masu amfana a Asibitin ‘Yar Kasuwa, Shamsiyya Abubakar, ta yaba wa gwamnatin jiha da ta ƙaramar hukuma bisa samar da magunguna kyauta, inda ta bayyana shirin a matsayin ceton rai ga mata da dama a yankin.
Makon Kiwon Lafiyar Uwa da Ɗa a Jihar Kano na da nufin kai ayyukan lafiya zuwa yankunan da ke da karancin samun kulawa, tare da rage gibin da ke tsakanin mata da yara wajen samun ingantacciyar kulawa.
Khadijah Aliyu