‘Harin da Iran ta kai wa sansanin sojin Amurka keta haddin Qatar ne’
Published: 24th, June 2025 GMT
Gwamnatin Qatar ta yi Allah-wadai da harin da Iran ta kai kan sansanin sojin saman Amurka da ke yankin al-Udeid na kasar.
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen ƙasar, Majed al-Ansari, ya wallafa a shafinsa na X cewa: “Mun ɗauki wannan a matsayin keta haddin Qatar da sararin samaniyarta da dokokin duniya da kuma yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya.
Ya ce na’urorin kakkaɓo makamai na ƙasar sun “samu nasarar daƙile hare-haren na makamai masu linzami” kuma tuni aka janye dakarun Amurka daga sansanin tun kafin harin.
Ya ƙara da cewa “an ɗauki duka matakan da suka dace wajen tabbatar da tsaron lafiyar dakarun a sansanin, ciki har da sojojin Qatar, da dakarun ƙawance da sauransu.
“Mun tabbatar da cewa babu wanda ya rasa rai ko jikkata a harin.”
Kakakin ya ce Qatar na da damar mayar da martani “domin rama daidai da abin da aka yi mata.”
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Nato Na Yin Taron Tattaunawa Keta Hurumin Samaniyar Kasar Estonia Da Rasha Ta Yi
A yau Talata ne dai kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato, ta bude wani zama na musamman a birnin Brussels domin tattauna zargin da ta yi wa kasar Rasha da keta hurumin sararin samaniyar kasar Istonia.
Taron na kungiyar yarjejeniyar tsaro ta Nato, yana a karkashin aiki da doka ta 4 ne na tsarin aikin kungiyar wacce ta yi kira da a rika yin tarukan gaggawa domin yin shawara a duk lokacin da wata memba ta fuskanci barazana.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Estonia ce dai ta bayyana cewa jiragen yakin Rasha, samfurin Meg-31 guda 3 su ka keta hurumin sararin samaniyarta a ranar juma’ar da ta gabata, sun kuma dauki tsawon mintuna 12 suna karakaina a samaniya.
Ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Estonia ta bayyana abinda ya faru da cewa, keta hurumin kasar ne a fili, wanda kuma ya sa kungiyar ta Nato ta yi kakkausar suka, tare da bayyan shi a matsayin tsokana daga Rasha.
Rasha dai tana zaman tsami da kungiyar Nato saboda yakin kasar Ukrainiya wanda ya shiga cikin shekaru na 3 ana yi.
A gefe daya Nato tana ci gaba da aike wa da sojojinta zuwa kasar Poland wacce take makwabtaka da Ukiraniya, bayan da ita ma ta zargi Rashan da cewa ta keta hurumin sararin samaniyarta.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Dembele Ya Lashe Kyautar Ballon d’Or Ta Shekara Ta 2025. September 23, 2025 Hindi: Amurka Da Kasashen Yamma Ba Sa Son A Dakatar Da Bude Wuta A Gaza. September 23, 2025 Tattalin Arzikin Najeriya Ya HaBaka A Rubu’i Na Biyu Na 2025 September 23, 2025 Kashi 80 Cikin Dari Na MDD Sun Amince Da Falasdinu A Matsayin Kasa. September 23, 2025 Iran Da Rasha Zasu Rattaba Hannun Kan Batun Gina Wasu Tashoshin Nukiliya. September 23, 2025 Hamas ta bukaci kasashen duniya da MDD su mayar da Isra’ila saniyar ware September 22, 2025 Iran : Dakatar da kisan kiyashi a Gaza, ‘’zakaran gwajin dafi ‘’ne ga MDD” September 22, 2025 Italiya: An yi gagarimar zanga-zangar tir da kisan kiyashi da ake yi a Gaza September 22, 2025 Iran ta la’anci harin da aka kai kan wani masallaci a Sudan September 22, 2025 Ana Ci Gaba Da Kidayar Kuri’aun Zaben Shugaban Kasa A Guinea September 22, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci