Aminiya:
2025-09-19@19:25:13 GMT

Jami’an tsaro sun ƙwato makamai da kama mutane 398 a Kaduna

Published: 20th, June 2025 GMT

Tawagar jami’an tsaron  haɗin gwaiwa ta musamman da Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani ya kafa domin yaƙi da ayyukan ’yan daba da sace-sacen waya a jihar, ta samu nasarar ƙwato makamai tare da cafke mutane 398 da ake zargi a wurare daban-daban.

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sanda (PPRO), DSP Hassan Mansir ne ya fitar, na bayyana cewa, an kai samamen ne  cikin gaggawa tare da wasu sahihan bayanan sirri.

Wani ya kashe mahaifiyarsa mai shekara 71 a Akwa Ibom Yin sulhu da ’yan bindiga dabara ce ba gazawa ba — Gwamnatin Sakkwato

Samamen ya sanya wasu da dama daga cikin masu aikata laifuka tserewa daga Jihar Kaduna saboda fargabar kama su.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, a cikin kwanaki tara na farko da rundunar take gudanar ayyukanta, ta kama wani mutum mai suna Mathew Adamu, wanda ya shahara wajen aikata ta’addancin cikin al’umma.

Sanarwar ta ce, rundunar ta ƙunshi rundunar ’yan sandan Najeriya ne a matsayin hukumar da ke jagorantar hukumar, tare da sojoji da Jami’an tsaron farin kaya DSS da Sibil defens da jami’an shige da fice na Najeriya da hukumar gyaran hali da hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi (NDLEA) da hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC) da Hukumar Kwastam ta Najeriya, ciki har da hukumar ’yan banga ta Jihar Kaduna (KADVIS).

DSP Hassan ya bayyana cewa, an samu wata ƙaramar bindiga ƙirar gida daga hannun wani mutum mai suna Adamu Umar, wani fitaccen mai sayar da miyagun ƙwayoyi, wanda za a miƙa ƙararsa ga Hukumar NDLEA mai yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Najeriya domin ci gaba da bincike da gurfanar da shi.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Kwastam

এছাড়াও পড়ুন:

An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe

Hukumar Sibil Difens (NSCDC) a Jihar Gombe, ta kama mutum shida bisa zargin tono gawar wani mutum a kabari tare da cire sassan jikinta domin yin asiri.

Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama, Kawuji Sarki, mai shekaru 39, ya amsa laifin.

Wata mata ta ƙona al’aurar ’yarta da wuta kan zargin maita a Bauchi Janye Dokar Ta-ɓaci: Fubara ya koma Ribas

Ya bayyana cewa wani mutum mai suna Aliyu Chindo ne, ya ba su aikin cire idanun mamacin, tare da yi wa kowannensu alƙawarin Naira 500,000.

Sai dai ya ce bayan kai masa sassan jikin, Chindo ya gudu ba tare da ya biya su ba.

Nan take jami’an tsaro suka cafke su.

An gano cewa sun tono kabarin wani tsoho mai shekaru 85, Mallam Manu Wanzam, wanda aka binne a ranar 9 ga watan Satumba a maƙabartar Gadam Arewa da ke Ƙaramar Hukumar Kwami.

Kakakin NSCDC a jihar, SC Buhari Sa’ad, ya bayyana sunayen sauran da aka kama: Adamu Umar (22), Umar Jibrin Aboki (21), Abdullahi Umar Dauda (17), Muhammed Isa Chindo (28), da Manu Sale (23).

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da neman Aliyu Chindo da ya tsere.

Kwamandan hukumar a jihar, Jibrin Idris, ya bayyana lamarin a matsayin “rashin imani,” tare da tabbatar da cewa za su gurfanar da waɗanda suka kama a kotu bayan kammala bincike.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Babu wani hari da aka kai sakatariyar NUJ a Yobe — ’Yan Sanda
  • An cafke mutum 6 kan tono gawa a kabari don yin asiri a Gombe
  • NAJERIYA A YAU: Ayyukan Da Fasahar AI Za Ta Raba Mutane Da Su Nan Ba Da Jimawa Ba
  • Sojoji Sun Tarwatsa Wata Haramtacciyar Masana’antar Ƙera Makamai A Filato
  • Hukumar Alhazai Ta Jigawa Za Ta Shirya Taron Bita Na Musamman Ga Jami’anta
  • Fasahar AI ta gano cutar da za ta kama mutane a shekara 10 masu zuwa
  • Gobara ta kashe manyan jami’an hukumar FIRS 4 a Legas
  • Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Aka Yi Wa Sharrin Safarar Ƙwayoyi
  • Saudiyya Ta Saki ‘Yan Nijeriya 3 Da Ta Kama Bisa Kuskuren Safarar Ƙwayoyi