Jakadan Sin Dake Amurka Ya Yi Jawabi A Gun Liyafar Da Kwamitin Kasa Mai Lura Da Kasuwancin Amurka Da Sin Ya Shirya
Published: 20th, June 2025 GMT
Kwamitin kasa mai lura da kasuwancin Amurka da Sin ko USCBC, ya gudanar da liyafar murna ta shekarar 2025, a ranar Laraba 18 ga wata a birnin Washington na Amurka, liyafar da jakadan kasar Sin a Amurka Xie Feng ya halarta tare da gabatar da jawabi.
Cikin jawabin nasa jakada Xie ya ce cimma moriya da nasara tare, muhimman ginshikai ne na ci gaba mai dorewa na hadin-gwiwar Sin da Amurka ta fuskar raya tattalin arziki da kasuwanci, inda dukkan bangarorin biyu gami da duniya ke cin gajiya.
Jakadan ya kara da cewa, dangantakar Sin da Amurka na cikin wani muhimmin lokaci, kana, neman hada kai don cimma moriya tare, ko kuma nuna wa juna kiyayya, hanyoyi ne mabambanta dake gabansu. Don haka ya dace kasashen biyu su tsaya bisa jagorancin shugabanninsu kan manyan tsare-tsare, da aiwatar da muhimman ra’ayoyi iri daya da suka cimma a zahiri. Har kullum kasar Sin na nuna sahihanci amma mai kunshe da sharadi, wato kiyaye cikakken yankin kasa, gami da muradun neman ci gaba, tamkar jan layi ne da ba za a iya tsallakewa ba, yayin da girmama juna, da kiyaye zaman lafiya da samun moriya tare cikin hadin-gwiwa, suka zamo babbar ka’ida da dole a mutunta ta. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare
A ranar 30 ga wata ne shugabannin kasashen Sin da Amurka suka gana da juna a birnin Busan na kasar Koriya ta Kudu, lamarin da ya jawo hankulan kasa da kasa, inda shugabannin 2 suka yi musayar ra’ayoyi dangane da huldar da ke tsakanin kasashen 2 da al’amuran da suka jawo hankulansu. Sun amince da inganta hadin gwiwar kasashen 2 a fannonin tattalin arziki da cinikayya da makamashi da kyautata mu’amalar al’adu.
A yayin ganawar, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jaddada cewa, yana son hada kai da shugaba Donald Trump na Amurka wajen aza harsashi mai kyau na raya huldar da ke tsakanin kasashen 2, tare da samar wa juna kyakkyawan yanayin samun ci gaba. A nasa bangaren, shugaba Trump ya ce, kasar Sin, abokiyar Amurka ce mafi girma. Kasashen 2 za su hada kansu wajen samun nasarar gudanar da manyan ayyuka da dama a duniya. Nan gaba Amurka da Sin za su kara samun nasara a hadin gwiwarsu. Shugabannin 2 sun amince su rika yin mu’amala da juna. Shugaba Trump yana sa ran kai ziyara a kasar Sin a farkon shekara mai zuwa, ya kuma gayyaci shugaba Xi ya ziyarci Amurka.
Masharhanta sun yi nuni da cewa, ganawar shugabannin 2 ta sanya tagomashi kan kyautatuwar huldar da ke tsakanin Sin da Amurka, ta kuma tsara manufar raya huldar kasashen 2 a nan gaba, tare da kwantar da hankulan kasashen duniya.
Abubuwan tarihi da kuma hakikanin abubuwa sun nuna cewa, wajibi ne Sin da Amurka su zama abokan juna. A wannan muhimmin lokaci, ganawar da shugabannin kasashen 2 suka yi ta sake tsara manufar kyautata da raya huldar da ke tsakanin kasashen 2. Muddin kasashen 2 suka aiwatar da muhimman daidaito da shugabannin 2 suka cimma, da mutunta ruhin adalci, tare da martaba juna da samun moriyar juna, to, za a raya huldar da ke tsakanin kasashen 2 ba tare da wata matsala ba, da kuma kara samar da kwanciyar hankali da tabbaci a duniya. (Tasallah Yuan)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA