Babu dalilin kai wa Iran farmaki — Putin
Published: 23rd, June 2025 GMT
Shugaban Ƙasar Rasha, Vladimir Putin, ya ce babu wata hujja ko dalilin kai wa Iran hari.
Putin ya yi wannan furuci ne yayin wata tattaunawa da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Agarachi a fadar Kremlin da ke birnin Moscow.
Akwai ƙasashen da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya — Rasha Fararen hula sun yi garkuwa da sojoji 57 a ColumbiaA jawabin da ya gabatar a farkon tattaunawar wanda aka yada a gidan talabijin na gwamnatin Rasha, shugaba Putin ya ce: “Babu wata hujja ko dalili da zai sa a kai wa Iran farmaki.
Ya ƙara da cewa “na ji daɗin zuwan ka [Agarachi] Moscow a yau. Wannan zai ba mu damar tattauna waɗannan batutuwa masu wahala da kuma hanyar shawo kan lamarin.”
A nasa jawabin, Ministan Harkokin Wajen na Iran ya ce ƙasarsa na da “ƙawance ta ƙut da ƙut” da Rasha.
Ya ce hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai wa Iran “sun saɓa wa dokoki da ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.”
A farkon shekarar nan Iran da Rasha sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna.
Sai da ba ta haɗa da ƙawancen soji ba kuma ba ta buƙaci Rasha ta kai wa Iran ɗaukin kariya ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Iran Isra ila kai wa Iran
এছাড়াও পড়ুন:
An Gano Gawar Wata Tsohuwa Mai Shekaru 96 Bayan Faɗawa Shadda A Kano
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump November 7, 2025
Manyan Labarai Barazanar Amurka Na Kawo Wa Nijeriya Hari November 7, 2025
Manyan Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Amince da Gina Sabbin Gidaje Ga Alƙalai, Da Samar Da Ruwa A FCT November 6, 2025