Daga Xi’an Zuwa Astana: Me Muka Koya Daga Taron Kolin Sin Da Kasashen Tsakiyar Asiya
Published: 19th, June 2025 GMT
A shekaru biyu da suka wuce, shugaban kasar Sin da takwarorinsa na kasashen nan biyar sun dasa wasu bishiyoyin ruman guda shida a birnin Xi’an, wadanda yanzu haka cike suke da furanni tare da alamanta hadin gwiwar kasashen mai cike da kyawawan nasarori, wadanda kuma suka shaida cewa, “hannu daya ba ya daukar jinka”, hada karfi da karfe ne zai kai ga inda aka dosa, kuma ba wanda ke iya cin nasara daga faduwar wasu, kuma za a iya tabbatar da nasara ga juna ne kurum idan aka zama tsintsiya madaurinki guda.
Yanzu haka, duniyarmu na fama da rikice-rikice da kariyar ciniki da ra’ayi na kashin kai da kuma siyasar nuna fin karfi. Amma bai kamata a mai da hannun agogon baya ba, kuma ba za a yarda da rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummomin duniya ba, kana ‘yan Adam bai kamata su koma irin rayuwar da masu karfi ke cin zalin masu karamin karfi kamar yadda aka yi a baya ba.
Daga birnin Xi’an zuwa Astana, Sin da kasashen tsakiyar Asiya sun samar da ruhin da ya amsa tambayar da zamaninmu ya aza mana, wato “me ya faru a duniyarmu, kuma me ya kamata mu yi”, wanda kuma ya karfafa mana niyyar kiyaye adalci da cin moriyar juna da samun nasara tare, don kiyaye zaman lafiyar duniya da tabbatar da ci gaban kasa da kasa baki daya. (Lubabatu Lei)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Baje Kolin Sin Da ASEAN Ya Fadada Matsayar Bai Daya Ta Cudanyar Sassa Daban Daban
A yau Laraba ne aka bude bikin baje koli karo na 22, na Sin da kasashe membobin kungiyar ASEAN ko (CAEXPO), da kuma taron dandalin kasuwanci da juba jari na Sin da ASEAN ko CABIS, a birnin Nanning na jihar Guangxi ta kabilar Zhuang mai cin gashin kai dake kudancin kasar Sin.
A shekarun baya bayan nan, Sin da kungiyar ASEAN, sun ci gaba da cimma manyan nasarori tare a fannin bunkasa dunkulewar tattalin arzikin shiyyarsu, da fadada damar bai daya ta cudanyar mabambantan sassa, a gabar da ake fuskantar yanayin tangal-tangal a duniya.
Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a da kafar CGTN ta kasar Sin ta gudanar, ta shaida yadda kaso 92.8 bisa dari na masu bayyana ra’ayoyi suka amince cewa, baje kolin CAEXPO ya bayyana yadda Sin da kungiyar ASEAN suka himmatu wajen bunkasa bude kofa bisa matsayin koli, da kare tsarin cinikayya cikin ’yanci da kasancewar mabambantan sassa.
Kafar CGTN ta gabatar da kuri’ar ne da harsunan Turanci, da Sifaniyanci, da Faransanci, da Larabci, da yaren Rasha, inda kuma mutane 6,260 suka bayyana ra’ayoyinsu cikin sa’ao’i 24. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp