Sanarwar ta ƙara da cewa, aikin Sahara ba wai kawai aikin jaridar bogi ba ne; ya samo asali ne zuwa da suna ‘Gonzo’, wanda ke da alaƙa da ƙarairayi wajen bayar da rahoto.

 

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “An ja hankalinmu kan labaran ƙarya da Sahara Reporters ke yaɗawa, shafin da ya shahara wajen yaɗa labaran ƙarya domin tayar da ƙura a intanet.

 

“A yayin tattaunawa da manema labarai kai tsaye a makon da ya gabata, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana ƙudirinsa na ɗaukar nauyin kasafin kuɗi, inda ya tabbatar da cewa bai karbi lamuni na cikin gida ko na ƙasashen waje ba tsawon shekaru biyu da ya yi yana mulki.

 

“Amma abin ya ba mu mamaki, manyan jami’an yaɗa labaran ƙarya, Sahara Reporters, sun wallafa abin da suka sanya a matsayin wani rahoto na musamman na yadda aka karbi rancen Naira Biliyan 34 a ƙarƙashin kulawar Gwamna Lawal.

 

“Rahoton na Sahara ya bayyana ƙarara irin gazawar su wajen neman ƙwararan bayanai tare da yin nazari kan takardar kasafin kuɗin jihar Zamfara.

 

“Rahoton lamuni na naira biliyan 34 da Sahara Reporters ta yaɗa na buƙatar ƙarin haske domin tabbatar da cewa jama’a sun fahimci gaskiyar lamarin.

 

“An shirya Kasafin Kuɗi na 2023 ne a zamanin gwamnatin Bello Matawalle, wanda a yanzu shi ne Ƙaramin Ministan Tsaro, daga cikin kasafin kuɗin, an ware biliyan 53.2 domin kula da lamuni da gwamnatin jihar ta karbo.

 

“Duk da cewa ba a samu lamuni a wannan adadi na sama ba, gwamnatin jihar Zamfara ta kashe biliyan 34 wajen biyan kuɗin ruwa na rance daban-daban da gwamnatocin baya suka karba, hakan ya nuna yadda Dauda Lawal ya jajirce wajen rage yawan bashin da ake bin Zamfara da kuma hana karbar ƙarin lamuni.

 

“Duk dandali da ya ƙuduri aniyar yin aikin jarida na gaskiya zai gudanar da cikakken bincike don tabbatar da hasashensa da kuma tabbatar da sahihancin sa, amma Sahara Reporters ta zabi wata hanya ta daban, ta tsaya kan tsarin aikin jaridar bogi.

 

“Ya kamata Sahara Reporters ta tambayi tsohon Gwamna Bello Matawalle kan yadda ya yi amfani da lamunin da ya karba a zamaninsa, wanda hakan bai haifar da wani ci gaba ba, rancen da muke biya kenan.

 

“Gwamna Dauda Lawal bai karbi rance ba tsawon shekaru biyu da ya yi yana Gwamnan jihar Zamfara.

 

“Muna ƙalubalantar Sahara Reporters da su samar da duk wasu takardun da ke nuna gwamnatin Zamfara mai ci na neman lamuni, ko a cikin gida ko kuma a waje.”

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Sahara Reporters tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Shugabannin DSS Sun Gana A Kaduna, Sun Tattauna Matsalar Tsaron Arewa Maso Yamma November 7, 2025 Manyan Labarai Hajjin 2026: NAHCON Ta Kammala Tantance Masaukai Da Ɗakunan Dafa Abincin Alhazai A Madinah November 7, 2025 Manyan Labarai Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump November 7, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Karramawar LEADERSHIP Gare Ni, Zaburantarwa Ce Ga Ci Gaba Da Kyawawan Manufofin Mu – Gwamna Lawal
  • Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Ta Tabbatar Da Hannun Amurka Wajen Kaddamar Da Yaki Kanta
  • Majalisa Ta Ƙaryata Karɓar Dala Miliyan 10 Don Daƙile Tantance Shugaban NERC
  • Gwamnatin tarayya ki amince damu a matakin ƙasa – Bijilanti
  • An gano gawar wata mai shekara 96 a cikin masai
  • Mun fara tattaunawa da Amurka kan barazanar Trump – Gwamnatin Tarayya
  • Cin zarafin Wakilin NTA ya tada ƙura a Yobe
  • Gwamnatin Tarayya ta fara shirin sayar da matatun manta ga ’yan kasuwa
  • NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir
  • Yadda Gwamna Lawal Ya Aiwatar Da Ayyukan Gina Zamfara Na Naira Biliyan 140