2027: ‘Sai bayan babban taron APC Tinubu zai bayyana wanda za su yi takara tare’
Published: 20th, June 2025 GMT
Fadar Shugaban Kasa ta ce shugaba Bola Tinubu zai zabi wanda zai yi masa takarar mataimaki a zaben 2027 a hukumance ne kawai bayan a kammala babban taron jam’iyyar APC a 2026.
Kakakin shugaban, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawarsa da jaridar Daily Trust a ranar Alhamis.
Da yake martani kan dalilin da ya sa fadar shugaban ta yi shiru kan zargin cewa Tinubu na son canza mataimaki a 2027 musamman la’akari da yadda ’yan jam’iyyar ke ta nuna goyon bayansu ga shugaban shi kadai, Onanuga ya ce hakan ba gaskiya ba ne.
A cewarsa, “Lokacin da na karanta labarin, na karyata shi saboda ba shi da tushe. A tsarin shugaba mai cikakken iko da Najeriya ke bi, dan takarar shugaban kasa ake fara zaba, shi kuma sai ya zabi wanda zai yi masa mataimaki. Abin da ya faru ke nan a lokacin Buhari – an fara zabensa, sai daga baya shi kuma ya dauki mataimaki. Ba a yin duka biyun a lokaci daya.
“Da zarar INEC ta fitar da jadawalin zabuka, jam’iyya za ta shirya babban taronta, idan aka sake tsayar da shugaban kasa, shi kuma zai zabi mataimakinsa,” in ji Onanuga.
Kazalika, ya kuma yi fatali da tarihin da ake daukowa cewa sau biyu tinubu yana canza mataimaka lokacin da ya yi Gwamna a jihar Legas daga 1999 zuwa 2007, cewa irin haka za ta faru da Kashim Shettima a 2027.
Ya kuma ce jita-jitar da ake yadawa a kan yiwuwar canza Shettima tun ma kafin a fara nuna amincewa da sake takarar Tinubu ba ta da tushe.
Ya ce, “Ba ni da masaniya a kan duk wani sabani tsakanin shugaban kasa da mataimakinsa. Iya abin da na sani shi ne akwai kyakkyawar fahimtar juna da alakar aiki mai kyau a tsakaninsu. Duk maganganun da ake yadawa ba su da maraba da na teburin mai shayi. Mutane na ta fadara maganganun rashin kan gado cewa wai Seyi Tinubu ne ma mataimakin shugaban kasa. Wannan shashanci ne.
“A wannan kasar, mukamin mataimaka ko na gwamna ko na shugaban kasa ba a raba su da ’yan tsegungumin mutane. Ko da ana zaune lafiya babu wata matsala, makunsantansu sai sun kirkiri husuma da labaran karya. Amma iya abin da na sani shi ne babu matsala tsakanin Tinubu da Shettima.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Dan Wasan Gaban Chelsea, Murdyk Ka Iya Shafe Shekaru 4 Ba Tare Da Ya Buga Wasa Ba
Murdyk ya halarci wasan karshe na gasar cin kofin Uefa Conference League da Chelsea ta doke Real Betis a watan da ya gabata, amma kuma ba a cikin tawagar Chelsea ba, a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, FA ta ce “Za mu iya tabbatar da cewa an tuhumi Mykhailo Mudryk da laifin keta dokar hana kara kuzari, ta hanyar amfani da wani abu da aka haramta, wanda kuma ya sabawa doka ta 3 da 4 a kundin dokokin FA na hana kara kuzari.
Zuwa yanzu Chelsea ba ta ce komai ba dangane da tuhumar da akeyiwa Murdyk amma a watan Disamba ta ce, ta na fatan dan wasan nata yayi nasara duba da cewa “Mykhailo ya tabbatar da cewa bai taba yin amfani da haramtattun abubuwa da gangan ba” tace a cikin sanarwar, a karkashin dokokin FA, yan wasa sunada yancin bukatar ayi masu gwaji na biyu bayan an samu tabbacin amfani da kwayoyi masu kara kuzari a gwajin farko, amma idan gwajin na biyu ya zo daidai da na farko to za a yanke masu hukunci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp