Shugaba Tinubu Ya Nada Jega Mai Ba Shi Shawara Na Musamman Kan Harkokin Kiwon Dabbobi
Published: 8th, March 2025 GMT
Shugaba Bola Tinubu ya nada tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Attahiru Muhammadu Jega a matsayin mai ba da shawara na musamman kan sake fasalin kiwon dabbobi.
Shugaban ya yi fatan nadin Farfesa Jega zai haifar da ci gaba mai ma’ana a fannin kiwo, da kuma kara karfafa ayyukan ci gaban kasa.
Tsohon Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Jega ne ya jagoranci Kwamitin Kiwo na Shugaban Kasa tare da Shugaba Tinubu.
Wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce kwamitin ya bayar da cikakkun shawarwarin da suka tabbatar da sauye-sauyen da aka samu a fannin kiwon dabbobi, daya daga cikinsu shi ne samar da ma’aikatar kiwo.
Jega, mai shekaru 68, mamba ne a Majalisar Ba da Shawarar Zabe ta Duniya, kuma Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Jihar Kano.
Ya rike mukamin shugaban hukumar ta INEC tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015.
Sanarwar ta ce nadin nasa zai karfafa nasarorin da kwamitin shugaban kasa ya samu, tare da tabbatar da ci gaba da sauye-sauyen da aka fara gudanarwa.
Daga Bello Wakili
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
Shugaban ‘Yan Bindiga A Zamfara, Bello Turji, Ya Ajiye Makamai, Ya Saki Mutane 32
Rahotanni sun bayyana cewa, fitaccen kwamandan ‘yan ta’adda Bello Turji ya mika wuya tare da sako wasu mutane 32 da aka yi garkuwa da su, biyo bayan wani shirin zaman lafiya da malaman addinin musulunci suka yi a jihar Zamfara. Wani fitaccen malamin addinin Musuluncin nan, Musa Yusuf, wanda aka fi sani da Asadus-Sunnah ne ya bayyana hakan yayin wani taron addini da aka yi a ranar Litinin a Kaduna.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp