Gwamnatin Hong Kong Ta Gudanar Da Bikin Cika Shekaru Biyar Da Kafuwar Dokar Tsaron Kasa Ta Yankin
Published: 22nd, June 2025 GMT
Gwamnatin yankin musamman na Hong Kong, ta gudanar da bikin murnar cika shekaru biyar da kafawa, da kaddamar da dokar tsaron kasa ta yankin. Yayin bikin da ya gudana a jiya Asabar, Xia Baolong, wanda shi ne shugaban ofishi mai lura da al’amuran yankunan Hong Kong da Macao a kwamitin kolin JKS, da ofishi mai lura da al’amuran yankunan Hong Kong da Macao a majalisar gudanarwa ta kasar Sin, ya ce dokar tsaron kasa ta yankin Hong Kong da aka kaddamar a ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2020, ta samarwa yankin damar fita daga hargitsi zuwa yanayi na daidaito, tare da shigar da yankin sabon zamani na gudanar da tsarin “kasa daya tsarin mulki biyu”.
Xia Baolong, ya ce dokar ta taka rawar gani wajen kare ’yancin kai, da tsaro da moriyar ci gaban kasa. Kazalika, ta haifar da daidaito da walwala a yankin na Hong Kong, tare da samar da kariya ga moriyar al’ummun Hong Kong, da baki masu zuba jari.
A nasa jawabin kuwa, kantoman yankin na Hong Kong, John Lee, cewa ya yi salon “kasa daya tsarin mulki biyu”, da dokar tsaron kasa ta Hong Kong, da dokar tabbatar da kare tsaron kasa sun dunkule tare da haifar da daidaito, ta yadda yankin Hong Kong zai iya samun ci gaba, da sauye-sauye, tare da bada karin gudummawa ga muhimman ginshikai na gina kasa da ingiza farfadowarta. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: dokar tsaron kasa ta
এছাড়াও পড়ুন:
Sin Tana Maraba Da Kwararru Daga Bangarori Daban Daban Na Kasa Da Kasa Su Zo Kasar
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau 22 ga wannan wata cewa, a yayin da ake raya duniya bisa tsarin bai daya, musayar kwararru a tsakanin kasa da kasa ta sa kaimi ga raya fasahohi da tattalin arzikin kasashen duniya. Kasar Sin tana maraba da kwararru daga bangarori da sana’o’i daban daban na kasa da kasa su zo kasar ta Sin su gudanar da harkokinsu don sa kaimi ga raya zamantakewar al’ummar dan Adam da kuma samun ci gaban sha’aninsu baki daya. (Zainab Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp