Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila
Published: 21st, June 2025 GMT
Iran ta lalata cibiyar binciken kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila, wato cibiyar kimiyya ta Weizmann Institute of Science da ke birnin Tel Aviv.
Cibiyar, wadda ke da alaƙa da binciken harkokin sojin Isra’ila, ta sanar da cewa harin da Iran ta kawo ɗin ya yi sanadiyar ɓarnar da ta kai kimanin Dala miliyan 500.
Makaman Iran sun lalata gine-gine da dama a cibiyar, lamarin da ya sanya masu bincike faɗi-tashi don ceto samfurin bincike a cikin ɓaraguzan gini, a yayin da gobarar ke ci.
Wani makami mai linzami ya tarwatsa wani gini mai ɗauke da ɗakunan gwaje-gwaje na zamani da dama, a yayin harin na ramuwar gayya, bayan da Isra’ila ta kashe masana kimiyyar nukiliya na Iran.
2027: Manyan ’Yan adawa na neman rajistar sabuwar jam’iyya Wani ya kashe mahaifiyarsa mai shekara 71 a Akwa IbomMakamin ya faɗo kan cibiyar ne kafin wayewar garin ranar Lahadi, amma babu wanda ya ji rauni domin cibiyar ba kowa a cikinta a lokacin.
Fira Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya ziyarci wurin, inda ya ce, “wannan harin ne dalilin da ya sa Isra’ila ba za a taɓa barin Iran ta mallaki makaman nukiliya ba.”
Idan ba a manta ba, Isra’ila ce ta fara kai hari kan Iran a ranar 13 ga Yuni, bisa hujjar cewa abokiyar gabar tata tana dab da ƙera makaman nukiliya.
Iran, wadda ta dage cewa shirin nukiliyarta don dalilai na zaman lafiya ne kawai, ta mayar da martani da hare-haren makamai masu linzami da na jirage marasa matuƙa a kan Isra’ila.
Hare-haren Isra’ila sun yi sanadiyar mutuwar wasu manyan masana kimiyyar nukiliya na Iran, da manyan shugabannin sojojin Iran, da fararen hula tare da lalata gidaje da tashoshin nukiliya da ababen more rayuwa.
Duk da cewa yawancin binciken cibiyar Weizmann sun danganci fannin gas magunguna da ilimin kimiyya ne, amma tana kuma da alaka da tsaro.
A watan Oktoba na 2024, ta sanar da haɗin gwiwa da babban kamfanin tsaro na Isra’ila, Elbit, kan “kayayyakin da aka samo daga halittu don aikace-aikacen tsaro.”
Cibiyar binciken kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ila, tana da ƙungiyoyin bincike 286, masana kimiyya ma’aikata 191, da daruruwan dalibai.
Iran ta sanar a ranar Juma’a cewa ba za ta tattauna makomar shirin nukiliyarta ba yayin da take fama da hare-hare daga Isra’ila.
Duk ƙoƙarin ƙasashen Turai na jan hankalin Tehran zuwa tattaunawa bai nuna alamun nasara ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Iran Isra ila nukiliya
এছাড়াও পড়ুন:
Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan buƙatar MDD ta tsagaita wuta a Gaza
Ƙasar Amurka ta hau kujerar-na-ƙi kan wani ƙudurin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ke neman a dakatar da yaki a Gaza nan take kuma ba tare da sharaɗi ba.
Daftarin kudurin na majalisar ya kuma buƙaci Isra’ila ta cire duk wani takunkumi kan kai agaji ga yankin na Falasɗinawa.
Wani ya sace munduwar Fir’auna a gidan tarihin Masar Kasar Albania ta nada mutum-mutumi a matsayin ministaKudurin, wanda ƙasashe 10 da aka zaɓa daga cikin mambobi 15 na majalisar suka tsara, ya kuma buƙaci a saki dukkan fursunonin aka yi garkuwa da su daga hannun Hamas da sauran kungiyoyi ba tare da sharadi ba, cikin mutunci da girmamawa.
Kudurin dai ya samu goyon bayan ƙasashe 14, sai dai Amurka ta yi amfani da karfin tuwo wajen kin amincewa da shi.
Wannan shi ne karo na shida da Amurka ke hawa kujerar-na-ki kan batun yaki tsakanin Isra’ila da Hamas tun kusan shekaru biyu da suka gabata.
Jakadiyar Denmark a Majalisar Dinkin Duniya, Christina Markus Lassen, kafin ta kada kuri’arta, ta ce, “An tabbatar da yunwa a Gaza, ba hasashe ba ne, ba jita-jita ba, an tabbatar da ita.”
Ta ƙara da cewa: “Isra’ila ta faɗaɗa hare-haren soji a birnin Gaza, lamarin da ke ƙara jefa fararen hula cikin wahala. Wannan mummunan yanayi da gazawar jin kai ne ya tilasta mu daukar mataki a yau.”
Wani rahoto daga hukumar da ke sa ido kan yunwa a duniya ya tabbatar da cewa birnin Gaza da kewaye na fama da yunwa, kuma akwai yiwuwar ta yadu.
Amurka na da al’adar kare Isra’ila a Majalisar Dinkin Duniya. Sai dai a makon da ya gabata, a wani mataki da ba kasafai ake gani ba, ta goyi bayan wata sanarwa daga majalisar da ke sukar hare-haren da aka kai Qatar, duk da cewa ba a ambaci Isra’ila a cikin rubutun ba.
Wannan mataki ya nuna goyon bayan Shugaban Amurka Donald Trump ga umarnin da Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya bayar.
Sai dai hawa kujerar-na-kin da Amurka ta yi a ranar Alhamis ya sake tabbatar da cewa Washington na ci gaba da ba Isra’ila kariya ta diflomasiyya.