Aminiya:
2025-09-18@16:10:39 GMT

Hisbah ta lalata katan 243 na barasa da wasu kayan maye a Yobe

Published: 19th, June 2025 GMT

A ci gaba da ƙoƙarinta na tabbatar da kyawawan halaye da kuma samar da zaman lafiya a tsakanin al’umma, Hukumar Hisbah ta Jihar Yobe ta lalata katan 243 na barasa da galan 100 na barasa da aka haɗa a gida, da aka fi sani da sukudaye.

A wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na Hukumar, Adamu Muhammad ya sanya wa hannu, ta ce an lalata barasa a Damaturu, a wani mataki na aiwatar da dokar hana sha da kayan rarraba barasa a jihar.

Guguwar ruwan sama ta yi ɓarna a Kwalejin Kimiyya da Fasaha a Kogi Tinubu na ƙaddamar da wasu ayyuka a Jihar Kaduna

Shugaban Hukumar Hisbah na jihar, Dokta Yahuza Hamza Abubakar ne ya bayyana cewa aikin ya yi dai-dai da aikin hukumar na aiwatar da dokokin da ke inganta nagarta da kare martabar al’umma.

“Shaye-shaye na haifar da barazana ga lafiyar jama’a da zamantakewar jama’a wadda akan hakan ne aka haramta sha da rarraba ta a cikin jihar a ƙarƙashin dokokin da ake da su,” in ji shi.

Dokta Yahuza ya nanata ƙudurin hukumar na samar da zaman lafiya, adalci da gyara al’umma, inda ya ce Hisbah ta kuma sasanta tare da warware wasu matsaloli a ayyukan da suka yi a baya-bayan nan.

Ya buƙaci mazauna jihar da su ci gaba da marawa ƙoƙarin hukumar baya wajen tabbatar da kyawawan ɗabi’u da mutuncin jama’a.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta

Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Alhaji Salim Hashim Idris Gwangwazo, ya kaddamar da shirin kula da ido kyauta domin tallafawa jama’a da ke fama da ‘Glaucoma’ da ke lalata rijiyoyin ido, da ‘Cataract’ wato yanar ido da sauran cututtukan ido.

An gudanar da shirin ne a Asibitin Kwalli tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar, ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf, da Hukumar Lafiyar Farko ta Jiha, da ƙaramar hukumar da masu bada tallafi daga kasashen waje.

Shirin ya haɗa da gwaje-gwajen lafiyar ido, da bayar da magunguna da kuma rarraba tabarau kyauta, musamman ga marasa ƙarfi a cikin al’umma.

Shugaban ƙaramar hukumar, ta bakin Kwamishinan Lafiya Alhaji Mustapha Darma, ya bukaci jama’a da su ci gaba da tallafawa gwamnati wajen samar da ingantaccen kulawa.

A baya-bayan nan, gwamnatin jihar ta dauki nauyin kula da lafiyar ido ga mutum  sama da 500 daga Birnin Kano da sauran kananan hukumomi.

Shugaban kula da lafiya am matakin farko na ƙaramar hukumar, Alhaji Lawan Jafar, ya ce wadanda lalurar su ba ta tsananta ba za a ba su shawarwarin kula da lafiyar su, da magunguna, wa su ma har da tabarau, yayin da wadanda ta su ta  tsananta kuma za a musu tiyata.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana sun nuna godiya tare da yi wa gwamnati addu’a don samun nasara.

Shugaban tawagar likitocin, Dr. Kamal Saleh, ya tabbatar da cewa shirin ya samu nasara sosai.

 

Daga Khadijah Aliyu 

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Hukumar Alhazai Ta Jigawa Za Ta Shirya Taron Bita Na Musamman Ga Jami’anta
  • Hukumar Bunkasa Ilimin Manyan Makarantu Ta Shirya Taro Na Musamman Ga Jami’anta
  • An kashe ’yan ta’addan IPOB da yawa a Imo — ’Yan Sanda
  • UNICEF Ya Ba Da Tallafin Kayayyakin Aiki Ga Cibiyoyin Lafiya A Kirikasamma
  • Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Ta Kammala Ziyarar Yini 3 A Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar
  • Karamar Hukumar Birnin Kano Ta Kaddamar Da Kula Da Lafiyar Ido Kyauta
  • ALGON ta karrama Gwamna Buni da lambar yabo kan kawo ci gaba a Yobe
  • Gwamnatin Kano ta gayyaci Mai Dubun Isa da Shehi Tajul-Izzi kan shirya muƙabala
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • Gwamnatin Neja Ta Musanta Rahoton Hana Da’awa A Jihar