’Yan bindiga sun sace babban alƙali a Bayelsa
Published: 22nd, June 2025 GMT
Wasu mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Alƙalin Babbar Kotun Jihar Bayelsa, Ebiyerin Omukoro.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 7 na daren ranar Asabar a unguwar Ekeki, kusa da babban titin Melford Okilo a Yenagoa, babban birnin jihar.
Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da kisan ’yan ɗaurin aure a Filato HOTUNA: Yadda aka yi jana’izar ’yan ɗaurin auren da aka kashe a FilatoRahotanni sun bayyana cewa, mutanen sun isa a cikin mota ƙirar Hilux, sanye da baƙaƙen kaya.
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa, maharsn sun kutsa kai gidan cin abincin da alƙalin ke ciki kuma suka tilasta masa shiga motarsu.
Har zuwa yanzu, ba a san inda suka kai shi ba, kuma babu wani saƙo ko buƙatar kuɗin fansa daga masu garkuwar.
Hakazalika ba a san dalilin da ya sa suka sace shi ba.
Wannan ba shi ne karon farko da aka sace mutum a yankin ba, domin an je har gida an sace wani ɗan jarida mai suna Oyins Egrenbido.
Wasu hotuna da bidiyo da suka karaɗe shafukan sada zumunta sun nuna yadda aka kama alƙalin tare da jefa shi cikin motar ƙirar Hilux.
Har yanzu Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bayelsa, ba ta fitar da wata sanarwa ba dangane da sace alƙalin.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Al’ummar Zamfara: ’Yan bindiga sun karɓi N56m domin izinin yin noma
Manoman gundumar Ɗan Isa da ke Ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara sun ce ’yan bindiga sun yi musu barazana a wannan damina ta bana.
Da yake tabbatar da hakan ga Daily Trust a wata tattaunawa ta wayar tarho, Hakimin unguwar Malam Hassan Yarima, ya ce kowane ƙauyuka 35 da ke ƙarkashin gundumarsa ya biya Naira dubu 800 kafin a bar mazauna yankin su yi noma.
NAHCON ta ƙayyade N8.5m kafin alƙalami na kujerar Hajjin 2026 ’Yan sanda sun ƙwato jariri da aka sace a asibitin Ekiti“Kowanne ƙauye kuma zai sake biyan Naira dubu 800, don bai wa mazauna yankin damar girbe amfanin gonakinsu, wannan ita ce yarjejeniya da muka cimma da shugaban ’yan bindiga da ke kula da wannan yanki, Ɗan Sadiya.”
“Ina magana ne game da gundumata kawai, ban san abin da mazauna wasu gundumomi suka biya wa ’yan bindigar ba a wannan shekara. Amma wani abu da nake da tabbacin shi ne mazauna yankin su biya kafin a barsu su yi noma.
“Ba mu da wani zaɓi illa mu bi umarninsa, in ba haka ba, ’yan bindiga ba za su barmu mu yi noman gonakinmu ba, a ƙalla idan muka yi noma, za mu iya samun wani abu ga iyalanmu,” in ji shi.
Sai dai Yarima ya koka da cewa, duk da biyan kuɗin noma, har yanzu ’yan bindiga sun mamaye ƙauyukansu suna sace dabbobi tare da kwashe kayan abinci.
Ya yi nadama kan yadda mazauna unguwannin da abin ya shafa suke yin amfani da duk abin da suke da shi a ƙoƙarin samun zaman lafiya da ’yan bindigar.
“Muna so mu zauna lafiya da ’yan bindigar, amma gaskiya sun karɓe mana komai, sun yi awon gaba da dabbobinmu sun kwashe kuɗinmu, amfanin noma da sauran kayayyaki.