Aminiya:
2025-09-24@14:16:57 GMT

Barau ya nesanta kansa daga masu nema masa kujerar mataimakin Tinubu a 2027

Published: 25th, June 2025 GMT

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya nesanta kansa daga wata kungiya da take fafutukar ganin Shugaban Kasa Bola Tinubu ya dauke shi a matsayin mataimakinsa a 2027.

Mai magana da yawun Sanatan, Isma’il Mudashir ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Talata, inda ya ce a maimakon haka, kamata ya yi kungiyar ta fi mayar da hankali wajen mara wa Tinubu baya ya samu nasarar yunkurinsa na bunkasa Najeriya.

A kwanan nan ne dai wata kungiya mai suna Zauren Matasan APC na Arewacin Najeriya (NNPYA) ta ayyana goyon bayanta ga Tinubu ya dauki Sanatan a matsayin wanda za su yi takara tare.

Gwamnatin Nijeriya ta yi wa Amurka martani kan barazanar tsaro a Abuja Mali ta ƙulla yarjejeniyar nukiliya da Rasha

Hakan dai ya biyo bayan jita-jitar da ake ta yadawa a ’yan kwanakin nan cewa ba lallai ne Tinubun ya sake yin takara tare da Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa a 2027 din ba.

A cewar Sanata Barau, “An jawo hankalina kan wasu rubuc-rubuce a shafukan sada zumunta da ma wasu jaridu na wasu kungiyoyi, cikinsu har da NNPYA, inda suke kiran jagoranmu, Shugaba Bola Tinubu, da ya dauke ni a matsayin mataimaki a 2027. Wannan ba da yawuna ba ne kuma ba shi ne abu mafi muhimmanci ba a yanzu.

“Ina kira ga NNPYA da ma sauran kungiyoyin da ke wannan fafutukar da su daina daga yanzu, sannan su mayar da hankalinsu wajen goyon bayan yunkurin Shugaba Tinubu na magance matsalolin da ke addabar kasarmu.

“Kamata ya yi mu hada karfi da karfe wajen goyon bayan Tinubu har ya samu ya kai Najeriya tudun mun tsira.

“Yanzu ba lokaci ne da za mu rika wannan kiraye-kirayen ba, lokaci ne na tabbatar da cewa Tinubu ya samu nasarar sauke nauyin da ke wuyansa.

“Ya damu kwarai da gaske wajen ganin Najeriya ta samu ci gaba. Saboda haka nake kira da kowa ya goya masa baya kan kudurorinsa da tuni aka fara ganin amfaninsu a kasa,” in ji Sanata Barau.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Barau

এছাড়াও পড়ুন:

He Lifeng: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Karfafa Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Mai Dorewa Cikin Lumana

Mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya gana da tawagar ‘yan majalisar wakilan Amurka karkashin jagorancin Adam Smith a yinin yau Litinin 22 ga wata a birnin Beijing.

He Lifeng ya ce, a ranar 19 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping da shugaba Donald Trump sun yi wata tattaunawa ta wayar tarho, kuma sun cimma muhimmiyar matsaya, tare da samar da jagoranci bisa manyan tsare-tsare don tabbatar da daidaiton dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka a mataki na gaba. Kasashen Sin da Amurka na da sararin yin hadin gwiwa da kuma samun moriyar juna.

Ana sa ran Amurka za ta sa kaimi wajen yin magana da kasar Sin bisa ka’idojin mutunta juna, da zaman lafiya da samun nasara ga ko wane bangare, da kara amincewa da juna, da kawar da shakku, da sa kaimi ga habaka dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Sin da Amurka. Ana fatan mambobin majalisar wakilan Amurka za su himmatu wajen samar da hanyoyin zantawa, da inganta tattaunawa da mu’amala, da kuma taka rawar gani wajen ci gaban kasashen biyu. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • UNGA: Yau Shettima zai gabatar da jawabin Najeriya a MDD
  • DSS ta yi wa Malami tambayoyi kan harin da aka kai masa a Kebbi
  • He Lifeng: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Karfafa Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Mai Dorewa Cikin Lumana
  • Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara haɓaka — NBS
  • Kasar Sin Na Matukar Goyon Bayan Tabbatar Da Adalci Ga Falasdinawa Wajen Maido Da Hakkinsu Na Kasa
  • Dalilin da muke goyon bayan Tinubu kan karɓo bashi — Majalisar Wakilai
  • Dalilin da muke goyon bayan tsare-tsaren Tinubu na karɓo bashi — Majalisar Wakilai
  • Mataimakin Shugaban BUK Ya Buƙaci ‘Yan Siyasa Da Su Yi Koyi Da Tallafin Karatu Na Barau
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wata Bakuwar Cuta Take Cin Naman Jikin Mutanen Malabu
  • APC Da PDP Na Zargin Juna Kan Amfani Da Addini Wajen Neman Nasara A 2027