Yin sulhu da ’yan bindiga dabara ce ba gazawa ba — Gwamnatin Sakkwato
Published: 20th, June 2025 GMT
Gwamnatin Jihar Sakkwato ta ce ba gazawa ba ce ta sa ta yanke shawarar tattaunawa da ’yan bindigar da suka yanke hukuncin ajiye makamansu ba.
Ta ce wannan hanya ce mafi kyau da za ta kawo zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
Katolika ta horar da shugabannin al’umma da na addini kan zaman lafiya Kotu ta daure mutumin da yake yada bidiyon tsiraici shekara 76 a kurkukuWani mai amfani da kafar sada zumunta, Basharu Altine Guyawa, ya soki wannan mataki na gwamnatin.
Amma Mai Bai Wa Gwamnan Jihar Shawara kan Tsaro, Kanal Ahmed Usman (mai ritaya), ya ce manufar gwamnati ita ce ta kawo zaman lafiya, ba don ta kasa ba.
Ya ce, “Mun san kowa na da ‘yancin faɗin albarkacin bakinsa. Amma dole ne mu fayyace dalilin da ya sa Gwamna Ahmed Aliyu ke amfani da hanyoyi daban-daban wajen magance matsalar rashin tsaro, ciki har da tattaunawa da ‘yan bindigar da suka tuba.”
Ya ƙara da cewa abin mamaki ne yadda Guyawa ke sukar wannan yunƙuri.
Ya ce shi ma ya taɓa buƙatar shirin shiga tsakanin gwamnati da ‘yan bindiga domin yin sulhu.
Kanal Usman ya bayyana cewa gwamnati tana amfani da dukkanin matakai biyu; na ƙarfi da na sulhu.
A cewarsa, mutane da yawa a Rabah, Goronyo, Isa, Sabon Birni da wasu yankuna na ta yin hijira.
Manoma sun bar gonakinsu, amfanin gona ya ragu, kuma kasuwanci ya tsaya cak.
Wannan ya jawo ƙarancin abinci da tsadar rayuwa a faɗin jihar.
“Burinmu shi ne mu dawo da zaman lafiya, mu dawo da mutane gidajensu, sannan a sake farfaɗo da harkokin noma da kasuwanci,” in ji shi.
Ya ce har yanzu gwamnati na aike jami’an tsaro inda ya dace.
Amma waɗanda suka tuba da gaske za a karɓe su bisa kulawa da tsari na gyaran hali.
“Wannan ba gajiyawa ba ce ko jin tsoro, wannan dabara ce ta sulhu domin ɗorewar zaman lafiya.”
Amma ya roƙi masu sukar gwamnati da su yi magana cikin hankali.
“Jihar Sakkwato na buƙatar haɗin kai da mafita, ba rabuwar kai da zargi ba. Gwamna Ahmed Aliyu na aiki tuƙuru don kawo zaman lafiya.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga Gwamnatin Sakkwato martani Tsaro zaman lafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Jami’ar Yobe sun tsunduma yajin aiki
Ƙungiyar Malaman Jami’a ta Ƙasa (ASUU), reshen Jami’ar Jihar Yobe (YSU), ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani saboda gwamnati ta kasa cika alƙawuran da ta ɗaukar musu.
Waɗannan alƙawura sun haɗa da ƙarin albashi, biyan bashin da suke bi, da kuma barin jami’ar ta riƙa gudanar da harkokinta da ƙashin kanta.
Lakurawa sun kashe ’yan sanda 3 a Kebbi Yadda aka kama ɗan bindiga ɗauke da N13m a hanyar JosShugaban ASUU na Jami’ar Yobe, Dokta Ahmed Karage, ya bayyana hakan bayan kammala wani taro da suka gudanar.
Ya ce sun fara yajin aikin ne bayan dogon lokaci da suka ɗauka suna tattaunawa da gwamnati, amma ba su cimma matsaya ba.
“Mun kwashe watanni muna magana da gwamnati, amma abin takaici shi ne dole ne yanzu mu tafi yajin aiki saboda gwamnati ta ƙi cika alƙawuran da ta ɗauka,” in ji Dokta Karage.
Daga cikin buƙatunsu akwai aiwatar da sabon mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000, biyan bashin albashin da ya fara tun daga shekarar 2019, da kuma wasu haƙƙoƙinsu.
Ya ce jami’o’i su riƙa tafiyar da al’amuran su da kansu shi ne mafita don warware matsalolin da ake fama da su a fannin ilimi.
ASUU ta ce ba za su koma aiki ba har sai gwamnati ta magance matsalolin da suka gabatar.
Sun gargaɗi gwamnatin jihar kan ɗaukar matakin gaggawa don kaucewa kawo cikas ga kalandar karatu.
Har ila yau, ƙungiyar ta roƙi dalibai da su yi haƙuri, inda ta ce ta fara yajin aikin ba don cutar da su ba, illa dai domin neman haƙƙinsu da ya wajaba gwamnati ta biya.