Bam ya kashe mutum 5, 15 sun jikkata a Kano
Published: 21st, June 2025 GMT
Aƙalla mutum biyar ne aka tabbatar da rasuwarsu, yayin da wasu 15 suka jikkata sakamakon fashewar wani bam a Jihar Kano.
Aminiya ta gano yadda fashewar bam ɗin ya haddasa firgici a yankin da lamarin ya faru, inda jami’an tsaro da na agajin gaggawa suka garzaya wajen don kai ɗauki.
An yi wa ma’aikatan ƙananan hukumomin Gombe ƙarin albashin N5,000 Mahara sun kashe ’yan ɗaurin aure 12 daga Zariya a FilatoKwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ya ce fashewar na iya kasancewa bam ɗin da sojoji suke yin jigilar ne wanda aka yi sakaci ya fashe.
“Na samu kiran gaggawa cewa wani abu mai tayar da hankali ya faru. Da na isa wajen, sai na ga abin kamar bama-baman sojoji ne suka fashe.
“Mutane 15 sun jikkata, kuma abin takaici, guda biyar sun rasu,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibitocin da ke kusa yankin domin samun kulawa ta gaggawa.
Ya ce binciken farko ya nuna cewa wata babbar mota ce ɗauke da kayan fashewar, wadda ta ke kan hanyar zuwa Jihar Yobe.
Har yanzu jami’an tsaro ba su tabbatar da ko motar sojoji ce ke ɗauke da kayan fashewar ba.
Rundunar na ci gaba da da bincike domin gano musabbabin faruwar lamarin da kuma abin da ya haddasa fashewar abun.
“Za mu samu cikakken bayani bayan kammala bincike,” in ji Kwamishinan.
Ya kuma roƙi jama’a da su kwantar da hankalinsu.
Ga hotunan yadda jami’an tsaro ke bincike kan lamarin:
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar Da Hankali Kan Dakatar Da Gidan Rediyon Badeggi FM
Minista Idris ya bayyana damuwa da irin martanin da al’umma da masu ruwa da tsaki a harkar yaɗa labarai suka nuna dangane da lamarin. Amma ya jaddada cewa hukumar da ke da hurumin dakatar da lasisin gidajen rediyo da talabijin ita ce Hukumar Kula da Gidajen Radiyo da Talabijin ta Ƙasa (NBC), kamar yadda doka ta tanada.
Sanarwar da Gwamnatin Tarayya ta bayar kan lamarin ta ce: “Saboda haka, ministan yana maraba da matakin da Gwamnatin Jihar Neja ta ɗauka na kai koken da ta ke da shi kan zargin rashin ɗabi’a da Badeggi FM ta yi a hukumance zuwa ga NBC domin a warware batun.”
Idris ya roƙi dukkan ɓangarori da su kwantar da hankalin su, yana mai tabbatar da cewa NBC tana da tsarin da ya dace na warware irin waɗannan matsaloli cikin gaskiya da adalci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp