A yanzu haka, fasahar kwaikwayon tunanin dan Adam ta AI na sauya zaman rayuwar dan Adam. Ga misalin, motoci mara matuki na saukaka tafiye-tafiye na dan Adam, samfurin binciken yanayi na iya hasashen hanyar guguwa a cikin dakika 10 kawai… Amma, fasaha ta zama kamar “takobi mai kaifi biyu”, wadda a lokaci daya take kuma kara haifar da matsaloli, kamar su fallasar sirri, yaudara ta hanyar amfani da AI, da hadarin rashin aikin yi.

Bisa wannan yanayin da ake ciki na kasancewar alfanu‌ da ‌matsaloli tare, ‌’dan Adam na bukatar hadin gwiwa cikin gaggawa don daidaita ci gaban fasahar AI, da kafa tsarin gudanar da harkokin fasahar AI na duniya, da nemo daidaito tsakanin kirkire-kirkire da tsaro, da nufin tabbatar da ganin an inganta ci gaban wayewar kai ta hanyar amfani da fasaha. Wannan shi ne dalilin da ya sa aka kaddamar da “shawarar gudanar da harkokin AI ta duniya”.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Xi Ya Bukaci A Yi Dukkan Mai Yiwuwa Wajen Gudanar Da Ayyukan Bincike Da Ceto Bayan Aukuwar Ambaliya A Lardin Gansu

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bukaci a yi dukkan kokarin bincike da ceto da tunkarar ambaliya da ayyukan agaji, bayan aukuwar ambaliya a yankin tsaunika tun daga jiya Alhamis, a lardin Gansu na arewa maso yammcin kasar Sin. Zuwa karfe 3 na rana a yau Juma’a, ibtila’in ya yi sanadin mutuwar mutane 10 da batan wasu 33.

Shugaba Xi Jinping na bada muhimmanci sosai ga yanayin ibtila’i da mamakon ruwan sama ya haifar a wasu yankuna ciki har da gundumar Yuzhong na Lanzhou, babban birnin lardin Gansu.

Cikin umarnin da ya bayar, Xi Jinping ya ce aiki na gaggawa shi ne yin dukkan mai yuwuwa wajen bincike da ceton mutanen da suka bata da ganowa da sake tsugunar da wadanda ke cikin hadari da rage hadari da dawo da hanyoyin sadarwa da na sufuri nan bada jimawa ba.

Ya ce la’akari da tsanantar yanayi a baya baya nan, ya zama wajibi hukumomin yankuna da sassan gwamnati masu ruwa da tsaki su karfafa aikin hasashen barazana da gargadin wuri, da nema da gano hadduran dake boye da karfafa ayyukan agaji da tsare-tsaren shirin ko-ta-kwana da karfafa daukan matakan takaita aukuwar ambaliya da na bayar da agaji, ta yadda za a tabbatar da tsaron rayukan jama’a a lokaci na damina. (Fa’iza Mustapha)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Ina Fatan Taka Inda Yayana Ya Taka A Fagen Ƙwallon Ƙafa A Duniya -Jobe Bellingham
  • Shin Amurka Ta Manta Da Azabar “Babban Koma-Baya” Tare Da Haraji Mafi Yawa a Lokacin Na Tsawon Kusan Karni?
  • An Bude Taron Mutum-Mutumin Inji Na Duniya Na 2025 A Yau Juma’a
  • Sin Ta Gabatar Da Korafi Da Babbar Murya Dangane Da Kalaman Jagoran Philippines 
  • Xi Ya Bukaci A Yi Dukkan Mai Yiwuwa Wajen Gudanar Da Ayyukan Bincike Da Ceto Bayan Aukuwar Ambaliya A Lardin Gansu
  • Mu Tuna Da Jinin Da Aka Zubar Don Kiyaye Hasken Da Muke Da Shi Yanzu
  • Amurka Ta Fara Girbar Sakamakon Kare-Karen Haraji
  • Nazarin CGTN: Alummar Duniya Na Adawa Da Fadada Mamaya A Gaza
  • An Bude Gasar Wasannin Ta Duniya Ta 2025 A Chengdu
  • Yadda sabbin takunkuman Trump za su shafi tattalin arziƙin duniya