Minista Ya Yaba Wa Hafsoshin Soji Kan Cigaban Da Aka Samu A Fannin Tsaron Ƙasa
Published: 21st, June 2025 GMT
Idris, wanda shi ne ya jagoranci zaman, ya bayyana irin nasarorin da aka samu a ƙarƙashin jagorancin Babban Hafsan Tsaro da sauran Hafsoshin Sojin a matsayin mai tabbataccen tasiri da gamsasshen sakamako.
Ya ce: “Abin da muka gani ba wai kawai daƙile waɗannan barazanar ba ne, sai dai ma sake karɓe sararin ƙasar mu, da tunanin jama’a, da kuma a matakin aiki.
Ya lissafa nasarorin da rundunonin sojin Nijeriya suka samu a sassa daban-daban na ƙasar nan, ciki har da yankin Arewa-maso-gabas da gaɓar teku.
“Daga nasarar ragargaza sansanonin Boko Haram da ISWAP a Arewa-maso-Gabas, zuwa irin gagarumin farmakin da aka kai kan maɓoyar ‘yan bindiga a Arewa-maso-Yamma da Arewa-ta-Tsakiya; daga ingantaccen sintirin da sojin ruwa ke yi wanda ya rage yawan satar ɗanyen mai da rushe haramtattun matatun mai; zuwa luguden wutar sama da ba ya ƙarewa wanda ya tarwatsa hanyoyin sufuri da ɗaukar kaya na miyagun mutane — sakamakon da aka samu ba kawai abin burgewa ba ne, har ma abin kwantar da hankali ne.”
Ministan ya kuma jaddada muhimmancin rawar da kafafen yaɗa labarai suke takawa wajen gina ƙasa, yana mai roƙon su da su tallafa wa ƙoƙarin da rundunonin tsaro suke yi ta hanyar yaɗa nasarorin da suke samu.
Ya ce: “Ya kamata kafafen yaɗa labarai su riƙa bada rahoto ba kawai kan abin da ya zama ba daidai ba, har ma da abin da ake yi daidai. Ku riƙa hasko irin sadaukarwar da dakarun mu suke yi. Ku bada labaran cigaba da ake samu. Ku daidaita suka da cikakken bayani. Wannan shi ne ainihin aikin jarida bisa ƙwarewa.”
Ya bada tabbacin cewa gwamnatin Tinubu za ta ci gaba da tallafa wa rundunar soji ba kawai da kayan aiki kaɗai ba har ma da tsare-tsaren dabarun da za su inganta tattara bayanan sirri, haɗin gwiwar hukumomi, da walwalar ma’aikata.
Ya yaba wa Hafsoshin Sojin bisa shugabancin su na kishin ƙasa da samar da sakamako mai tasiri.
“Kun dawo da fata, kun ceci rayuka, kun kare martabar ƙasar mu, kuma fiye da komai ma, kun tunatar da mu ma’anar yi wa ƙasa hidima,” inji shi.
Ya kuma buƙaci kafafen watsa labarai da sauran masu ruwa da tsaki da su riƙa haska irin nasarorin da ake samu, yana mai cewa hakan yana da matuƙar muhimmanci wajen ƙarfafa gwiwar jami’an tsaro.
“Ku lura da cigaban da ake samu kuma ku faɗaɗa yaɗuwar sa. Wannan na da matuƙar amfani ga ɗimbin dakarun mu da ke aiki dare da rana don kare ƙasar nan da samar da yanayin da duk ‘yan Nijeriya za su iya rayuwa, su yi aiki, su bunƙasa.”
Taron ya samu halartar Ministan Tsaro, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda Manjo Janar A.T. Jibrin (ritaya) ya wakilta; da Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa; da Manajan Daraktan Kamfanin Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN), Malam Ali M. Ali; da Babban Daraktan Hukumar Gidajen Rediyon Nijeriya (FRCN), Dakta Mohammed Bulama; da Babban Daraktan Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; da Shugaban da Shugaban Majalisar Ƙungiyar Masana Harkokin Yaɗa Labarai ta Nijeriya (NIPR), Dakta Ike Neliaku; da wakilan Hafsoshin Soji, da manyan shugabannin kafafen yaɗa labarai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: yaɗa labarai nasarorin da
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Ɗantsoho Ya Mayar Da Hankali Wajen Farafaɗo Da Martaba Da Ƙimar NPA
Daga baya an ƙara nata wani nauyin kula da Tashoshin Warri, Koko, Burutu da kuma ta Sapele, waɗanda kamfanonin ƴ an kasuwa masu zaman kansu ne, ke tafiyar da su, amma har zuwa yau, mahukunta a NPA ne, ke tafiyar da duk wata ragamar hukumar baki ɗaya.
A shekaru da dama da suka gabata, matsaloli da dama, sun dabaibaye NPA da suka haɗa da, cin hanci da rashawa da rashin ingantattun kayan aiki, musamman na zamani da sauransu, inda waɗannan matsalolin suka haifar wa da NPA koma baya matuƙa, musamman na wajen zama a kan gaba wajen gudanar da harkar hada-hadar kasuwanci a nahiyar Afirka.
Amma, za mu iya cewa, Allah san barka da naɗa Dakota Abubakar Ɗantsoho, a matsayin zaƙaurin shugaban hukumar kuma mai hangen nesa, wanda ya a baje ƙwarewarsa da kuma hazaƙarsa da su yi daidai da ƙugurin shugaba Bola Ahmed Tinubu na sake farfaɗo da fatan ga ƴ an ƙasar da kuma ita ƙasar Kant’s, wato Renewed Hope Agenda.
Ɗantsoho, da shigarsa ofis, bai wani ɓata lokaci ba, ya fara da ƙaddamar da gagarumin bincke domin gano inda ake da giɓi kan gudanar da ayyukan a NPA wanda hakan ya ba shi damar, yin garanbawul baki ɗaya a hukumar, musamman domin ya sake ɗora ta, a kan turba, mai ɗorewa.
Domin tabbatar da ya daƙile ƙalubalen cunkoson musamman na Jiragen Ruwa da ke sauka, Ɗantsoho ya yi ƙoƙari wajen ganin, an yi nesa da hanyoyin Tashar Jiragen Ruwa ta jihar Legas da Tashoshin Jiragen Ruwa na Fatakwal da ta Onne da ta Warri da kuma ta Kalaba musamman duba da cewa, rashin ɗaukar wannnan matakin tun da farko a baya, ya haifar da cunkoso da ya kai kaso 90
Kazalika, baya ga magance wannan matsalar ta cunkoso da shugaban ya yi,hakan ya kuma sanya hada-hadar kasuwanci a yankunan da ke a nahiyar Afirka, ƙara tunbatsa.
Ɗantsoho, bai tsaya a nan ba,misali saboda tsaikon da ake samu a Kogin Riba Neja, ya ƙirƙiro da aikin yashe hanyoyin ruwan, musamman domin a rage cunkoso da ake samu a Tashar Jiragen Ruwa ta Onitsha, wanda hakan ya taimaka wajen ci gaba amfana da albarkatun tattalin arziki.
Bugu da ƙari, saboda burin da ya ke da shi, musamman na zamantar ƙufurin ƙara ciyar da hukumar gaba, Ɗantsho ya tabbatar da an ware dala biliyan ɗaya domin a yiwa ginin Tashar Jiragen Ruwa ta Tincan Island da ta Apapa da ta, Riɓers da ta Onne ta ta Warri da kuma ta garin Kalaba.
Asusun Bunƙasa Ayyuka wato RHIDF ne, ke tallawa wajen gudanar da waɗannan ayyukan wanda hakan ɗai ƙara taimaka wa wajen ƙara bunƙasa ɗuba hannun jari a fannin.
Hakazalika, a ƙarƙashin iya salon shugabanci na gari na Dakta Ɗantsoho ke ci gaba da gudanarwa, an samu raguwa cunkson Jiragen Ruwa da sauka a Tashshin da suka kai kaso 45.1 da kuma samun ƙaruwar shigo da Kwantainoni, da suka kai kaso 9.7 wanda hakan, ya ƙara haɓaka hada-hadar kasuwanci natuƙa.
Ɗantso ya kuma ƙirƙiro da tsarin yin amfani da na’urar Electronic truck call-up wanda hakan, ya ƙara zamantar da ayyuka a Tashohin Jiragen Ruwan tare da kuma rage cunkoso, Jiragen Ruwa.
Ɗaukacin waɗannan ayyukan da Ɗantsoho ke gudanawar, sun zo ne, daidai da manufar gwamnatin shuigaba Bola Tinubu.
Shugaban na NPA ya kuma kasance a kan gaba wajen ganin an ƙaddamar da Tashin Tsayawar Jiragen Ruwa na kan tudu, kamar dai, na gain Funtuwa, da ke a jihar Katsina, wnada an yi hakan ne, domin ƙara haɓaka fitar da kana da ba su shafi fannin Mai ba da kuma ƙara haɓaka hada-hadar kasuwanci.
Shirin aikin kashe dala biliyan ɗaya a Tashar Snake Island wanda za a ƙara faɗaɗa kadada 85 a cikin Tashar, an yi ne, bisa nufin gudanar da harkar hada-hadar kasuwanci a Tashar, wanda hakan zai kuma ƙara ɗaga darajar Nijeriya a fagne kasuwanci.
Ayyukan ci gaba da Ɗantsho ke ci gaba da samarwa a NPA, ba wai kawai nan ya tsaya ba, domin kuwa, a kwanan baya, an zaɓe shi ya zama shugaban ƙungiyar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa ta Gabas da yankin Afirka ta Tsakiya wato PMAWCA.
Wannan zaɓar ta sa, ta nuna a zahiri, irin tunbatsar da ficen da ƙasar nan ta yi a fagen na harkar sufurin Jiragen Ruwa, musamman a nahiyar Afirka
Har ila yau, Ɗantsho shugaba ne, da bai yin wasa da kula da walwalar da haƙƙoƙin ma’aiakatasa, musamman domin ya tabbatar da yaƙi cin hanci da rasahawa.
Duk dai a ci gaba da marawa tsarin shugaba Tinubu na ci gaba da ƙara tarawa ƙasar kuɗaɗen shiga, Ɗantsoho ya amince da kafa tsarin tara kuɗaɗe shiga na kai tsaye, a NPA ta hanyar yin haɗaka da hukumar kula da harkokin sufurin jiragen ruwa ta ta ƙasa wato NIMAS da kuma hukumar Kwastam.
Wannan manufar, an yi ta ne, domin a tabbatar da ana bin diddigin tara kuɗaɗen shigar da kuma kula da su.
Ɗantsoho, ya kuma tabbatar da ana ƙara ƙarafafawa masu hada-hdar Jiragen Ruwa na ƙasar guiwa wanda kuma ya yi daidai da manufar gwamnatin ƙasar.
Burin da har zuwa yau Ɗantsoho ya sanya a gaba shi ne, ganin NPA ta tsarewa tsara, wajen ƙara samar da ci gaba ba wai kawai a tsakanin nahiyar Afirka ba, har a ma faɗin duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp