Aminiya:
2025-08-09@05:15:22 GMT

Trump ya zargi Isra’ila da Iran da saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta

Published: 24th, June 2025 GMT

Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya zargi Iran da Isra’ila da saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta.

Da yake jawabi kafin tafiyar Babban Taron Ƙungiyar NATO, da zai gudana a birnin Hague, Trump, ya bayyana takaicinsa bisa yadda kasashen biyu game da saɓa yarjejeniyar, sa’o’i kaɗan bayan sun amince da ita.

Tun da farko sai da ya buƙaci Isra’ila ta janye shirinta na kai wa Iran hari.

A safiyar Litinin bayan sanarwar Trump cewa ɓangarorin sun amince su tsagaita wuta ne, Ministan Tsaron Isra’ila ya yi barazanar kai wa Iran hari mai tsanani bayan zargin ta da harbo wa ƙasarsa rokoki.

Iran ta musanta zargin tare da cewa Isra’ila za ta yaba wa aya zaƙi idan kuskura ta kawo mata hari.

Daga bisani Trump ya ce wa Isra’ilar, “Kada ki kai harin bom a Iran, yin kika babban saɓawa ne. Ki umarci matuƙa jiragenkinki su koma gida.”

Buƙatar tasa bayan fara tsagaita wuta da Iran ta yi, na da alaƙa da sabon tayar da jijiyoyin wuts tsakanin Iran da Isra’ila.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Iran Isra ila yarjejeniyar tsagaita wuta

এছাড়াও পড়ুন:

Sojojin Sama Sun Yi Lugudan Wuta, Sun Kashe Ƴan Ta’adda A Borno

Rundunar Sojin Sama ta ƙasa (NAF) ta daƙile harin da ’yan ta’adda suka shirya kai wa sansanin Sojoji a Rann, jihar Borno, tare da kashe da dama daga cikinsu yayin da suke tserewa.

Mai magana da yawun NAF, Ehimen Ejodame, ya bayyana cewa dakarun saman ƙarƙashin Operation Haɗin Kai (OPHK) sun hana harin ne da safiyar 8 ga Agusta, 2025, ta hanyar samun bayanan leƙen asiri da kai farmaki daga sama.

Tashin Gurneti Ya Hallaka Yara Uku A Borno Sojoji Sun Kama Mai Yi Wa Boko Haram Safarar Man Fetur A Borno

An gano tarin ƴan ta’adda da ke gudu bayan samun bayanan sirri, sannan aka fatattake su da makamai na musamman, inda aka hallaka da dama daga cikinsu.

Ejodame ya ce wannan matakin gaggawar da aka ɗauka ya dawo da zaman lafiya a yankin, yana kuma nuna jajircewar NAF wajen kare Sojoji da shawo kan barazanar ƴan ta’adda cikin hanzari.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran da Masar sun jaddada wajabcin daukar matakan kawo karshen kisan kiyashi a Gaza
  • Sojojin Sama Sun Yi Lugudan Wuta, Sun Kashe Ƴan Ta’adda A Borno
  • Sojoji sun yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta a Borno
  • Araqchi: Hari Kan Cibiyoyin Makamashin Nukiliyar Kasar Iran Ba Zai Taba Canza Matsayinta Ba
  • Yadda sabbin takunkuman Trump za su shafi tattalin arziƙin duniya
  • Gaza: Fararen hula 22 sun yi shahada a hare-haren Isra’ila a daren jiya
  • Sin Ya Yi Kira Ga Isra’ila Da Ta Dakatar Da Aiwatar Da Mataki Mai Hadari A Zirin Gaza
  • Malaman Jami’o’in Isra’ila Sun Nemi Jamus Ta Tilasta Dakatar Da Yakin Gaza
  • IRGC: Bayan yakin Kwanaki 12 Yanayi Ya Sauya Zuwa Ga Amfani Ga Iran
  • Iran tana Goyon Bayan Zaman Lafiya Tsakanun Kasashen Yankin