Atiku Da Wasu Sun Kafa Sabuwar Jam’iyya, Sun Nemi INEC Ta Musu Rajista
Published: 21st, June 2025 GMT
A cikin takardar, ƙungiyar ta bayyana cewa ta yanke shawarar kafa sabuwar jam’iyya maimakon haɗaka da wasu.
Sun bayyana cewa sun zaɓi suna All Democratic Alliance (ADA) kuma taken jam’iyyar shi ne “Justice for All” wato “Adalci ga Kowa.”
Sun kuma haɗa da adireshin babban ofishin jam’iyyar a cikin takardar.
Sun gabatar da wasu muhimman takardu da suka haɗa da tambarin jam’iyya, tsarin kundin mulki, tutar jam’iyyar, da manufofinta.
Tambarin jam’iyyar ya ƙunshi kayan hatsi irin su masara da launuka masu ma’ana.
Kundin tsarin mulki kuma ya ƙunshi manufofi, tsari da dokokin jam’iyyar, bisa ga tsarin dokokin Najeriya da ƙa’idar dimokuraɗiyya ta duniya.
Takardar ta ƙare da girmamawa, inda ta ke roƙon INEC da ta ɗauki mataki na gaba wajen kammala rijistar jam’iyyar.
Sauran manyan ‘yan siyasa da ke cikin wannan haɗaka sun haɗa da Tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Rotimi Amaechi, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa David Mark, da Dakta Umar Ardo, wanda ya kafa ƙungiyar League of Northern Democrats.
A baya, ƙungiyar ta yi la’akari da shiga wata jam’iyya, kamar African Democratic Congress (ADC) da Social Democratic Party (SDP).
Sai dai daga sun fasa bayan sun lura da rikice-rikicen cikin gida da shari’o’i da waɗannan jam’iyyu ke fuskanta.
Saboda haka, suka zaɓi kafa sabuwar jam’iyya da za su fara daga tushe tare da daidaita tsakanin mambobinta.
Yanzu suna jiran matakin da INEC za ta ɗauka yayin da suke shirin tunkarar zaɓen 2027.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Adawa Haɗaka Manyan Yan Siyasa Sabuwar Jam iyya
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe ’yan ta’addan IPOB da yawa a Imo — ’Yan Sanda
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, ta ce jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, sojoji da DSS sun kashe ’yan ta’addan ƙungiyar IPOB da yawa.
Kakakin rundunar, DSP Henry Okoye, ya ce tawagar ta lalata sansanonin IPOB a yankin Ezioha da ke Ƙaramar Hukumar Mbaitoli, da kuma a Umuele, Ubuakpu, da Amakor a Ƙaramar Hukumar Njaba.
’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m NAJERIYA A YAU: Wadanne Kalubale Gwamna Fubara Zai Fuskanta Bayan Dawowa Mulkin Ribas?Ya ce da yawa daga cikin mambobin ƙungiyar sun mutu yayin samamen, wasu kuma an kama su, yayin da wasu suka tsere da raunuka.
Okoye, ya ƙara da cewa an gano bindigogi da harsasai da dama a sansanonin, haka kuma ƙwararru sun lalata abubuwan fashewa da aka samu wuraren.
Rundunar ta jadadda ƙudirinta na wanzar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa tare da roƙon jama’a su yi aiki tare da jami’an tsaro.