Fararen hula sun yi garkuwa da sojoji 57 a Columbia
Published: 23rd, June 2025 GMT
Rundunar Sojin ƙasar Columbia ta tabbatar da cewa fararen hula sun yi garkuwa da dakarunta guda 57.
Janar Federico Alberto Mejía na Rundunar ya sanar a ranar Lahadi cewa mutane kimanin 200 sun yi garkuwa da sojojin ne bisa umarnin ’yan tawayen FARC da suka addabi ƙasar.
Ta bayyana cewa al’ummar ƙasar suna fuskantar matsin lamba daga ’yan tawayen masu ɗauke da makamai.
Sanarwar ta ƙara da cewa an sace sojoji 31 a ranar Asabar, ragowar kuma ranar Lahadi.
Erik Rodríguez ya bayyana cewa sace sojojin na da alaƙa da kama wani jagoran ’yan tawayen kungiyar EMC da sojojin suka yi.
Ya ce a yayin da suke ƙoƙarin daukar sa a jirgi ne mutanen suka yi musu ƙawanya suka yi awon gaba su a yankin Kudu maso Yammacin Micay Canyon mai tsaunuka.
Ƙungiyar ’yan tawayen FARC ta addabi yankin Kudu maso Yammacin ƙasar, wanda ya yi ƙaurin suna wajen safarar miyagun ƙwayoyi a kusa da Lardin El Plateado.
Yankin ya yi fice wajen sarrafawa da safarar horar iblis, kuma yana cikin yana daga cikin wuraren da suka fi dama da tashin-tsahina a ƙasar ta Columbia.
A baya kungiyar ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin kasar a shekarar 2016.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: yan tawayen
এছাড়াও পড়ুন:
Ministan tsaron Ghana da wasu sun rasu a hatsarin jirgin sama
Wasu manyan jami’an gwamnati biyu a Ƙasar Ghana, sun rasu tare da wasu mutum shida a wani hatsarin jirgin sama da ya auku a ranar Laraba.
Hatsarin ya faru ne a yankin Ashanti da ke Kudancin ƙasar.
Gwamnan Kano ya gargaɗi muƙarrabansa bayan murabus ɗin Kwamishina Manoma sun koka kan rabon takin gwamnati a SakkwatoMinistan Tsaro, Edward Omane Boamah, da Ministan Muhalli, Ibrahim Murtala Mohammed, na cikin jirgin soja tare da wasu fasinjoji uku da ma’aikatan jirgin guda uku.
Jirgin ya tashi daga birnin Accra, babban birnin Ghana, zuwa garin Obuasi lokacin da aka daina jin ɗuriyarsa.
Rundunar Sojin Ghana ta ce sun daina samun saƙo daga jirgin yayin da yake cikin tafiya.
Julius Debrah, shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasar, ya bayyana a cikin wani saƙon bidiyo cewa wannan hatsarin babban rashin ne ga ƙasar.
Ya kuma ce dukkanin tutocin ƙasar za a yi ƙasa da su har sai an bayar da sanarwa domin girmama wadanda suka rasu.
Sauran waɗanda suka rasu sun haɗa da Alhaji Mohammed Muniru Limuna (muƙaddashin mai kula da harkokin tsaron ƙasar), Samuel Sarpong (mataimakin shugaban jam’iyyar National Democratic Congress), da Samuel Aboagye (tsohon ɗan takarar majalisa).
Sunan ma’aikatan jirgin da suka mutu su ne Squadron Leader Peter Bafemi Anala, Flying Officer Malin Twum-Ampadu, da Sergeant Ernest Addo Mensah.