Gwamnonin Arewa sun yi Allah-wadai da kisan ’yan ɗaurin aure a Filato
Published: 22nd, June 2025 GMT
Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya nuna baƙin cikinsa kan kisan wasu matafiya daga Jihar Kaduna da aka yi a Ƙaramar Hukumar Mangu ta Jihar Filato.
Matafiyan sun fito ne daga Zariya suna kan hanyarsu ta zuwa ɗaurin aure, yayin da wasu ɓata-gari suka farmake su.
Gwamnan ya ce wannan kisa abin takaici ne kuma rashin imani ne da ya saɓa wa doka.
Ya buƙaci a yi adalci cikin gaggawa.
Haka kuma ya miƙa ta’aziyyarsa ga Gwamnatin Jihar Kaduna, iyalan mamatan, da sauran waɗanda abin ya shafa.
A cewar sanarwar da Daraktan Yaɗa Labaran Gwamnatin Jihar Gombe, Isma’ila Uba Misilli, ya fitar, Gwamna Yahaya ya yaba wa gwamnati da ‘yan sanda a Jihar Filato bisa kamo wasu da ake zargi da hannu a kisan.
Gwamnan ya buƙaci a yi bincike na gaskiya, a gurfanar da waɗanda ke da hannu domin a hukunta su, sannan a hana irin hakan faruwa a gaba.
Haka kuma, ya roƙi al’ummar Filato da Kaduna da sauran maƙwabta da su zauna lafiya, su guji ɗaukar fansa.
Ya ce Gwamnonin Arewa za su ci gaba da haɗa kai domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
“Ina tabbatar muku cewa kare rayuka da dukiyoyin al’umma shi ne babban burinmu. Za mu yi aiki tare har sai an kawo ƙarshen wannan matsala,” in ji Gwamnan.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Ɗaurin Aure Gwamnonin Arewa
এছাড়াও পড়ুন:
Gidauniyar Tunawa Da Sardauna Ta Jinjinawa Gwamna Namadi Bisa Ayyukan Cigaban Jihar Jigawa
Daga Usman Muhammad Zaria
Gidauniyar Tunawa da Marigayi Sir Ahmadu Bello (ABMF) ta yaba wa Gwamna Umar Namadi bisa sauƙin kai, tawali’u da jajircewarsa wajen ci gaban Jihar Jigawa.
Shugaban Kwamitin Amintattu na Gidauniyar kuma tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dr. Mu’azu Babangida Aliyu ne ya yi wannan yabon yayin da ya jagoranci tawaga zuwa gaisuwar ban girma a fadar gwamnatin jihar da ke Dutse.
Ya ce salon jagoranci na Gwamna Namadi na ɗauke da ƙima da marigayi Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, ya shahara da su, musamman tsari, girmama jama’a da shugabanci na gaskiya da rikon amana.
Dr. Aliyu ya yi kira ga shugabannin Arewa su rungumi jagoranci da ke maida hankali kan al’umma, tare da fifita ilimi a matsayin tubalin cigaba.
Ya kuma sanar da cewa Jihar Jigawa ce za ta karbi bakuncin taron gidauniyar na shekarar 2026, wanda zai ƙunshi laccoci, shirye-shiryen wayar da kan jama’a da bada lambar yabo.
A jawabinsa, Gwamna Namadi ya gode wa Gidauniyar bisa wannan yabo da kuma zaɓar Jigawa don karɓar taron na 2026.
Ya kuma jaddada aniyar gwamnatinsa na ci gaba da bin sawun Sardauna ta hanyar shugabanci na gaskiya, tsare-tsaren jin daɗin jama’a da kuma zuba jari a fannin ilimi.
Ya tabbatar da cikakken goyon baya wajen shirya taron 2026 cikin nasara.
Tawagar ta haɗa da Madakin Zazzau, Malam Muhammad Munir Ja’afaru, da wasu jami’an Gidauniyar.