Aminiya:
2025-09-24@11:22:16 GMT

Amurka ta roƙi China ta sa baki kada Iran ta rufe mashigar tekun Hormuz

Published: 23rd, June 2025 GMT

Gwamnatin Amurka ta buƙaci ƙasar Sin da ta hana Iran rufe mashigar tekun Hormuz, ɗaya daga cikin muhimman hanyoyin jigilar kayayyaki a duniya.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya yi kiran ne bayan da kafar yada labarai ta Iran, Press TV ta ruwaito cewa majalisar dokokin ƙasar ta amince da shirin rufe mashigar.

Duk wani cikas ga samar da man fetur zai yi tasiri mai tsanani ga tattalin arzikin duniya.

Ƙasar Sin ce babbar mai sayen mai daga Iran kuma tana da kyakkyawar alaka da Tehran.

Harin Iran: Amurka ta ɗebo ruwan dafa kanta Koriya ta Arewa za ta taimaka da gyara tashoshin nukiliyan Iran —Masani NAJERIYA A YAU: Matakan daƙile kisan matafiya a hanyoyin Najeriya

Farashin man fetur ya tashi bayan harin da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran, inda farashin man Brent crude ya kai matsayinsa mafi girma cikin watanni biyar.

Matakin rufe mashigar tekun Hormuz wadda kusan kashi 20 cikin ɗari na man fetur da iskar gas na duniya ke bi ta cikinta, zai iya jefa duniya cikin bala’in rashin mai.

Masani kan harkokin kasuwanci Gerrit Heinemann ya shaida wa kafar yaɗa labarai ta Daily Mail ta ƙasar Birtaniya, cewa idan Iran ta zaɓi rufe mashigar, sakamakon zai zama “bala’i.”

Mashigar hanya ce ta kasuwanci mai mahimmanci ga duniya, inda kusan kashi ɗaya cikin biyar na man fetur na duniya ke bi ta mashigar teku. Kazalika adadi mai yawa na iskar Gas Mai Ruwa (LNG), na bi ta mashigar,  wanda hakan ya sa ta zama “mafi muhimmancin mashigar isar da man fetur a duniya.”

Kwamandan Rundunar Juyi Juya Halin Musulunci na Iran kuma ɗan majalisar dokokin ƙasar, Esmail Kosari ya bayyana cewa wannan matakin yana cikin ajandarsu kuma “za a yi shi duk lokacin da ya zama dole.”

A ƙarshen makon jiya Kowsari ya sanar cewa rufe mashigar tekun Hormuz “yana cikin matakan da gwamnatin ƙasar ke duba yiwuwar ɗauka, kuma Iran za ta yanke shawara da ya fi dacewa.”

Press TV ya ruwaito cewa matakin rufe mashigar tekun Hormuz bai kammala ba, har yanzu Majalisar Koli ta Tsaro ta Kasa ta Iran ce ke da hurumin yanke shawara ta ƙarshe kan lamarin.

Amma Kowsari ya bayyana cewa Iran ba ta iyakance iya matakin da za ta ɗauka a kan Isra’ila ba, kuma, “martanin soji wani yanki ne kawai na martaninmu gaba ɗaya.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Iran rufe mashigar tekun Hormuz

এছাড়াও পড়ুন:

Lokaci Yayi Da Shugabannin Arewa Za Su Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Yankin –  ACI

Ya gargadi cewa, tarihi ba zai gafarta wa shugabannin Arewa ba idan suka kasa daukar matakin gaggawa wajen dakile kashe-kashe, garkuwa da mutane da rikice-rikicen da ke addabar yankin. Ya ce shiru da fifita wasu akan wasu daga cikin shugabanni suna kara ta’azzara matsalar tsaro a jihohin Zamfara, Kaduna, Katsina, Filato da Benuwe.

 

Ya bayyana cewa akwai damuwa matuka yayin da ‘yan bindiga ke ci gaba da addabar al’umma, wasu daga cikin manyan mutane na fifita shirya shagulgula masu tsada maimakon kiraye-kirayen tarurrukan neman mafita na gaske don kawo karshen wannan rikici.

 

“Lokacin yin shiru ya wuce, yanzu ne lokacin daukar mataki. Tarihi ba zai gafarta wa halin ko-in-kula ba a lokacin da ake bukatar mataki fiye da kowane lokaci.”

 

Idris ya ce kungiyarsu na cikin damuwa matuka bisa abin da ya kira “ƙin ɗaukar mataki na gaggawa daga hukumomin tsaro duk da bayanan sirri da ke hannunsu, lamarin da ya bar gwamnonin jihohi cikin wahala da kuma barin ‘yan kasa cikin hali na shakku da rashin tsaro:.

 

Ya kuma bukaci ‘yan Arewa da su kaurace wa rarrabuwar kawuna, yana mai jaddada cewa tsawon ƙarnuka mutane masu bambancin addinai da kabilu sun zauna tare cikin zaman lafiya.

 

Har ila yau, dole ne a fahimci zaman lafiya ba wai kawai rashin rikici ba ne, har da nufin kasancewar adalci, da mutunci ga kowa.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Larijani: Iran na kare tsaron kasa da azama
  • Kuri’ar Jin Ra’ayoyi Ta CGTN: Guguwar Amincewa Da Kasar Falasdinu Ta Nuna Yadda Amurka Da Isra’ila Suka Zama Saniyar Waren Da Ba A Taba Gani Ba
  • Kotu ta hana NUPENG rufe Matatar Ɗangote
  • He Lifeng: Ya Kamata Sin Da Amurka Su Karfafa Dangantakar Tattalin Arziki Da Cinikayya Mai Dorewa Cikin Lumana
  • An rufe sansanin NYSC da kasuwanni saboda rashin tsaro a Kwara
  • Li Qiang Ya Gana Da Tawagar Membobin Majalisar Wakilai Ta Amurka
  • Lokaci Yayi Da Shugabannin Arewa Za Su Kawo Ƙarshen Matsalar Tsaro A Yankin –  ACI
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Hau Turbar Hadin Gwiwa Da Samun Moriyar Juna A Sabon Lokaci
  • SERAP, Amnesty Sun Bukaci Tinubu Ya Janye Ƙarar Da Ya Shigar Kan Sowore, X Da Facebook
  • Arakci Ya Kore Cewa Ya Zanta Da Steven Witkoff Na Amurka