Bom ya kashe mutum 5 a Kano — ’Yan sanda
Published: 21st, June 2025 GMT
Ana fargabar mutum biyar sun mutu a sakamakon tashin bom a Jihar Kano a ranar Asabar.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori, ba bayyana cewa bom ɗin soja ne ya tashi.
Kwamishinan ya ce akwai yiwuwar kuskure wurin safara ko kuma wurin kula da abin fashewan.
Ya bayyana haka ne a yayin ziyarar gani da ido da ya kai wurin da abin ta tashi.                
      
				
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An kashe ’yan bindiga 19 yayin daƙile wani hari a Kano
Dakarun Rundunar Sojin Najeriya sun daƙile wani harin ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Shanono da ke Jihar Kano, inda suka yi nasarar hallaka 19 daga cikin ’yan ta’addan.
Bayanai sun ce sojojin ƙarƙashin rundunar haɗin gwiwa ta Operation MESA sun fafata da ‘yan bindigar ne da yammacin ranar Asabar bayan samun bayanan sirri kan motsinsu a yankunan Unguwar Tudu da Unguwar Tsamiya da Goron Dutse.
’Yan Sandan Legas sun ayyana neman Sowore ruwa a jallo Kano Pillars ta koma ƙarshen teburin Gasar Firimiyar NijeriyaA sanarwar da kakakin rundunar, Kyaftin Babatunde Zubairu, ya fitar, sojojin sun gaggauta kai samame yankin bayan samun rahoto, inda suka yi musayar wuta da ’yan bindigar.
“A yayin arangamar, an hallaka ’yan bindiga 19, kuma an ƙwato babura da dama da wayoyin salula guda biyu daga hannunsu,” in ji Kyaftin Zubairu.
Sai dai ya tabbatar da cewa sojoji biyu da ɗan sa-kai guda ɗaya sun rasu yayin fafatawar.
Kyaftin Zubairu ya ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da sintiri a yankin don kare al’ummomin da ke cikin haɗarin hare-haren masu satar shanu da sauran laifuka.
Rundunar ta kuma shawarci jama’a su kasance cikin shiri da lura, tare da kai rahoton duk wani motsi da ake zargin ba na halas ba ga jami’an tsaro mafi kusa.
A cewar kwamandan rundunar, Birgediya Janar Ahmed Tukur, Rundunar Sojin Najeriya na ƙoƙari wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a Kano, tare da haɗin gwiwar sauran hukumomin tsaro.
An bayyana wannan aikin a matsayin wani ɓangare na ci gaba da kare yankunan karkara domin bai wa mazauna ƙwarin gwiwa a wuraren da ake fama da hare-haren ’yan bindiga.