Harin Amurka A Wurare 3 Na Nukiliyar Iran: Babu Wani Lahani A Harin Bama-baman – Iran
Published: 22nd, June 2025 GMT
Trump ya ce hare-haren da Amurka ta kai kan cibiyoyin nukiliyar Iran guda uku, lallai zai kara rura wutar rikici a ci gaba da yakin da ake yi tsakanin Iran da Isra’ila.
Sai dai ministan harkokin wajen Iran Seyed Abbas Araghchi ya yi Allah wadai da harin da Amurka ta kai da cewa “abin takaici ne” sannan ya ce Iran ta tanadi “dukkan zabin kare ‘yancinta”, yana mai jaddada cewa Amurka za ta fuskanci “tsauraran sakamako”.
Araghchi ya kara da cewa, Amurka ta keta kundin tsarin mulkin Majalisar Dinkin Duniya a matsayinta na mamba a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.
Bugu da kari, wani dan Majalisar kasar Iran, ya kara da cewa, “babu wani mummunan lahani a wuraren, kuma dama tun kafin harin, an riga an kwashe duk wasu abubuwa masu muhimmanci na tashoshin nukiliyar”.
Tun da farko, Tehran ta yi gargadin cewa za ta kai hari kan muradun Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya domin daukar fansa kan duk wani hari da Amurka ta kai, kuma ya zuwa yanzu ta harba makamai masu linzami kan Isra’ila, inda aka ji karar fashewar wasu abubuwa a birnin Kudus.
A halin da ake ciki, kawunan ‘yan majalisar dokokin Amurka ya rabu dangane da shigar kasar, inda ‘yan jam’iyyar Republican suka yabawa Trump, yayin da ‘yan jam’iyyar Democrat suka yi gargadin cewa an jefa Amurka cikin wani yakin da ba nata ba.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
’Yan kwangila sun hana zaman majalisa kan rashin biyan haƙƙoƙinsu
Majalisar Wakilai ta dakatar da zamanta na tsawon mako guda, sakamakon zanga-zangar da wasu ’yan kwangila suka gudanar a ƙofar shiga ginin majalisar dokoki ta ƙasa da ke Abuja, saboda rashin biyan kuɗaɗen ayyukan da suka kammala tun shekarar 2024.
Rahotanni sun ce ’yan kwangilar sun yi dandazo ne a ƙofar shiga majalisar a ranar Talata, domin nuna rashin jin daɗinsu kan yadda gwamnati ta gaza biyansu haƙƙoƙinsu duk da cewa sun kammala ayyukan da aka ba su.
China ta yi martani kan barazanar Trump ta kai hari Najeriya Kotu ta sahale wa PDP gudanar da babban taronta a IbadanBayanai sun ce masu zanga-zangar sun rufe hanyoyin shiga da fita na majalisar, abin da ya tilasta shugaban majalisar da sauran ’yan majalisa jinkirta zaman da aka shirya gudanarwa.
Wasu daga cikin ’yan kwangilar sun shaida wa manema labarai cewa sun gaji da alkawuran da gwamnati ke ci gaba da yi ba tare da cika su ba, inda suka yi kira da a gaggauta biyansu haƙƙoƙinsu kafin su sake komawa bakin aiki.
Majalisar ƙarƙashin jagorancin mataimakin kakakinta, Benjamin Okezie Kalu, ta ce an dakatar da zaman ne domin ba wa hukumomin da abin ya shafa damar tattaunawa da ’yan kwangilar, da nufin warware matsalar cikin lumana.
Matakin da majalisar ta ɗauka na zuwa ne bayan wani taƙaitaccen ƙudiri na gaggawa da shugaban marasa rinjaye a majalisar, Kingsley Chinda ya gabatar.
Chinda ya jawo hankalin majalisa kan “matsanancin halin da ’yan kwangila ke ciki” saboda rashin biyan su haƙƙoƙinsu duk da alƙawarin gwamnati.
A cewar Chinda, zanga-zangar ta samo asali ne a dalilin gazawar gwamnati wajen aiwatar da umarnin da Shugaba Bola Tinubu ya bai wa Ministocin Kuɗi da Tsara Tattalin Arziki da su biya ’yan kwangilar cikin gaggawa.
Bayan muhawara kan wannan ƙudiri ne majalisar ta amince da buƙatar bai wa Ministan Kuɗi, Wale Edun; da Ministan Tsara Tattalin Arziki, Atiku Bagudu; da Akanta Janar na Ƙasa wa’adin kwanaki bakwai domin su biya dukkan kuɗaɗen kwangilar da aka biyo gwamnati.
Daga bisani ne ɗan majalisa daga Jihar Zamfara, Kabiru Ahmadu Mai-Palace, ya gabatar da wani ƙarin ƙudiri da ya nemi majalisar ta dakatar da zamanta na mako guda har sai an ga matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka.
Da yake nasa tsokacin, Shugaban Kwamitin Majalisar kan Ka’idoji da Hanyoyin Gudanarwa, Francis Waive, ya mara masa baya, inda ya ce hakan ne ya fi dacewa ganin cewa masu zanga-zangar sun yi barazanar ci gaba da rufe hanyoyin majalisar har na tsawon mako guda.
Dangane da hakan ne majalisar ta yanke shawarar dakatar da dukkan ayyukanta har zuwa Talata mai zuwa, yayin da ake jiran sakamakon tattaunawa tsakanin shugabannin majalisar da ɓangaren zartarwa.
Majalisar ta kuma umurci shugabanninta da su tabbatar da kiyaye wannan matsaya, tare da bayar da rahoto nan da mako guda domin ɗaukar matakai masu tsanani idan gwamnati ta gaza yin abin da ya dace.