Shugaban Ƙasar Amurka Donald Trump ya ce an ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta gaba daya a yaƙin da ya ɓarke tsakanin Iran da Isra’ila.

Kafar yaɗa labarai ta the Guardian ta ƙasar Birtaniya ta ruwaito cewa Trump ya sanar da haka ne a shafinsa na sadar da zamunta, ’yan sa’o’i bayan hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kai a sansanin sojin Amurka da ke ƙasar Qatar da Iran bayan hare-haren da Amirkan ta kai wa Iran.

Ya sanar cewa cikin awa shida na farko Iran za ta fara dakatar da kai hare-hare, daga bisani Isra’ila ta dakatar, wanda hakan zai kawo ƙarshen yaƙin ɗungurungum.

Sanarwar tasa na zuwa ne bayan tsohon Fira Ministan Rasha, babbar ƙawar Iran, Dimitry Medvedev na cewa ƙasashe masu ƙarfin makaman nukiliya na yi wa Iran tayin makaman nasu a yayin da yaƙin ke ƙara ƙamari.

Babu dalilin kai wa Iran farmaki — Putin Akwai ƙasashen da ke shirin bai wa Iran makaman nukiliya — Rasha

Kazalika akwai yiwuwar babbar abokiyar gaban Amurka, wato Koriya ta Kudu na shirin taimaka wa Iran gyara tashoshin nukiliyan da hare-haren Amurka da Isra’ila suka shafa, da kuma gina sababbin masana’antun ƙera makamai masu linzami masu gudun walƙilya.

Hakan na zuwa ne kuma bayan Majalisar Dokokin Iran ta amince da ƙudirin rufe mashigar tekun Hormuz, matakin da Amurka ta buƙaci China ta sa baki Iran ɗin ta janye.

A gefe guda kuma Iran ta ci gaba da ruwan rokoki a kan Isara’ila, wadda ta fara kai wa cibiyoyin nukiliyar da na harkokin soji da fararen hula hari a ranar 13 ga watan nan na Yuni.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: hare hare Iran Isra ila nukiliya

এছাড়াও পড়ুন:

IRGC: Bayan yakin Kwanaki 12 Yanayi Ya Sauya Zuwa Ga Amfani Ga Iran

Kakakin dakarun juyin juya halin musulun a nan Iran ya bayyana cewa nasarar da JMI ta samu na tunkude hare-harenda HKI ta kawowa kasar ya saya abubuwa da dama a bangaren siyasa da wasu al-amura a yankin da kuma duniya gaba daya.

Kamfanin dillancin labaran Tasnim na kasar Iran ya nakalto General Ali Mohammad Naeini yana fadar haka a wani wani taro na tunawa da daya daga cikin shahidan yakin kwanaki 12 wanda HKI da Amurka suka kallafawa kasar. Ya kara da cewa duniya ta sauya sabada nasarar sannan musamman a fagen diblomasiyya da kuma kafofin yada labarai a duniya, wanda ya bar tasiri mai kyau ga kasar.

Labarin ya kara da cewa, akalla kasha 60 % na mutanen duniya sun yi amini kan cewa JMI ta sami nasara a yakin, amma a fagen yankin kuma wannan adadin ya kai kasha 80%. Don haka bayan wannan yakin, batun Iran mai rauni kuma ya tashi daga, aiki sai dai Iran mai karfi. Banda haka ganin kasashen duniya 120 ne suka yi alla wadai da hare-haren wannan adadin ya nusa cewa matsayin Iran a duniya ta sauya, sauyi mai amfani a gareta, sauyin da kuma ya bada daraja da kuma kimar maganarta. Daga karshe Janar Naini ya kammala da cewa, wannan sauyin ba karamin al-amari ne a yankin da kuma duniya ba. Kuma zai shafi al-amura a yankin da kuma duniya gaba daya.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka ‘Yansanda A Iran Suna Amfani Da Kayakin Tsaro Na Zamani A Lokacin 40 August 6, 2025 Iran tana Goyon Bayan Zaman Lafiya Tsakanun Kasashen Yankin August 6, 2025 Iran Ta Ce Babu Wani Da Zai Kusanci Cibiyoyin Tashe Makamashin Uranim Na Kasar Iran August 6, 2025 Iran: Yakin Kwanaki 12 Ya Bayyana Inganci Da Karfin Yakin Yanar Gizo Na Kasar August 6, 2025 Iran: An nada Larijani a matsayin sakataren kwamitin koli na tsaron kasa August 6, 2025 Sheikh Qassem: Tsaron Isra’ila zai rushe cikin sa’a 1 idan ta shelanta yaki a kan Lebanon   August 6, 2025 Kwamitin Sulhu na MDD ya yi zaman gaggawa kan batun Gaza August 6, 2025 Kamaru: An haramta wa babban dan hamayya tsayawa takara a zaben Oktoba August 6, 2025 Yunkurin Netanyahu na mamaye Gaza ya tayar da balli a Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 6, 2025 Araqch: Hadin Kai Tsakanin Cibiyoyi  Na Tabbatar Da Karfi Da Ci Gaba August 5, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Axios: Majalisar ministocin Isra’ila ta amince da sabon shiri na mamaye birnin Gaza
  • Zamfarawa sun yi zanga-zanga kan hare-haren ’yan bindiga
  • Hare-Haren Sojojin Mamayar Isra’ila Kan Gaza Sun Janyo Shahadan Falasdinawa Masu Yawa
  • Human Rights Watch Ta Ce: Sojojin Mamayar Isra’ila Sun Rusa Makarantu Fiye Da 500 A Gaza
  • Yadda sabbin takunkuman Trump za su shafi tattalin arziƙin duniya
  • Gaza: Fararen hula 22 sun yi shahada a hare-haren Isra’ila a daren jiya
  • An Fara Gudanar Da Juyayin Cikan Shekaru 80 Da Harin Amurka Da Makamin Nukiliya Kan Hiroshima Na Kasar Japan
  • Sin Ya Yi Kira Ga Isra’ila Da Ta Dakatar Da Aiwatar Da Mataki Mai Hadari A Zirin Gaza
  • IRGC: Bayan yakin Kwanaki 12 Yanayi Ya Sauya Zuwa Ga Amfani Ga Iran
  • Hare-haren Boko Haram Da ‘Yan Bindiga Ya Ragu A Cikin Shekaru Biyu – Ribadu