Dangane da sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta bayar na cewa za ta maido da yin tambayoyi ga dalibai kafin a ba su biza kuwa, Guo Jiakun ya ce, kasar Sin ta lura da batun, kuma tana fatan Amurka za ta aiwatar da kalaman shugaba Trump na maraba da daliban kasar Sin da su zo Amurka don yin karatu.

Dangane da wani rahoto da wata cibiyar bincike ta kasar Switzerland ta fitar, inda ta bayyana cewa, matsayin karfin yin takara na yankin Hong Kong na Sin ya karu zuwa matsayi na uku a duk fadin duniya, Guo Jiakun ya bayyana cewa, wannan na nuni da matsayin Hong Kong na musamman da kuma alfanun da ake da shi, da kuma tabbatar da ci gaban manufar “Kasa daya, mai tsarin mulki biyu”.(Safiyah Ma)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Sin Ta Samu Bunkasar Tafiye-Tafiye Cikin Gida Da Kashi 20.6% A Rabin Farko Na Bana

An yi balaguro na cikin gida sama da biliyan 3.28 a kasar Sin a rabin farko na shekarar 2025, adadin da ya karu da kashi 20.6 cikin dari a mizanin duk shekara, bisa bayanan da ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta fitar a yau Jumma’a.

Masu yawon bude ido na cikin gida sun kashe jimillar yuan tiriliyan 3.15 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 441 a cikin wadannan watanni shida, inda adadin ya karu da kaso 15.2 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar 2024.

Bugu da kari, musamman an lura da yadda yawan tafiye-tafiyen cikin gida da mazauna yankunan karkara ke yi suka karu da kashi 30.6 cikin dari a mizanin duk shekara, inda aka samu karin kashi 30.1 cikin dari idan aka kwatanta da na rabin farkon bara. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Son Zai Bar Tottenham Zuwa Amurka Bayan Shafe Shekaru 10 A Ingila
  • Amurka Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Zuwa Ƙasarta Domin Haihuwa
  • Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar Da Hankali Kan Dakatar Da Gidan Rediyon Badeggi FM
  • Sauya Sheƙa: Sanatoci Biyu APC Ke Buƙata Wajen Samun Kashi Biyu Cikin Uku A Majalisar Dattawa
  • Kwamitin Tantance Makarantun Gaba da Sakandire Na Bogi Ya Yi Wa Yankin Funtua Dirar Mikiya
  • Kasar Sin Ta Yi Watsi Da Zargin Amurka Dangane Da Batun Ukraine
  • 2027: APC Da ADC Na Gwagwarmayar Neman Samun Goyon Bayan Mutanen Arewa
  • Sin Ta Kadu Da Takunkumin Da Amurka Ta Kakaba Wa Hukumomi Da Jami’an Falasdinu
  • Har yanzu ana fama da cutar kwalara a Najeriya – UNICEF
  • Sin Ta Samu Bunkasar Tafiye-Tafiye Cikin Gida Da Kashi 20.6% A Rabin Farko Na Bana