Za mu sake gina kasuwar waya ta Farm Center — Abba
Published: 22nd, June 2025 GMT
Gwamnan Kano Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi alƙawarin sake gina kasuwar waya ta Farm Center da ta yi gobara a kwanakin baya.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Asabar.
Amurka ta ƙaddamar da hare-hare kan Iran Za mu ci gaba da yi wa Isra’ila luguden wuta — Shugaban IranSanarwar ta ce bayan ziyarar gani da ido da gwamnan ya yi a ranar Juma’a, ya ɗauki matakin sake gina kasuwar tare da sabunta ta da zamanantar da ita, aikin da da ya ce “gwamnan zai kashe naira biliyan 2.
“Wannan yunƙuri ba kawai saboda gobarar ba ce, za mu yi amfani da wannan damar ne domin inganta tattalin arzikin jihar, da samar da ayyukan yi,” kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin jihar za ta saya ƙarin fili domin faɗaɗa kasuwar, inda za ta samu damar gina abubuwan da ake buƙata a kasuwa na zamani, ciki har da gina sashen masu kashe gobara domin jiran kar-ta-kwana.
“Ba kasuwa kawai za mu gina ba, cibiyar kasuwanci za mu gina domin jawo ’yan kasuwa daga ƙasashen duniya,”in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Farm Center Gobara Jihar Kano
এছাড়াও পড়ুন:
Ta’addanci Ba Zai Yi Nasara Ba A Ƙasarmu — Tinubu
“Duk da matsalolin siyasa da muke fuskanta, mun ci gaba da hadin gwiwa da abokan huldarmu ta hanyar diflomasiyya.
“Ina tabbatar muku da cewa, ta’addanci ba zai yi nasara ba. Aikin da ke gabanmu shi ne, mu ci gaba da ajandar Sabunta Fata don gina Nijeriya mai arziki da wadata,” in ji Tinubu.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA