DAGA LARABA: Ko Najeriya Na Da Kudin Renon Sabbin Jihohi?
Published: 25th, June 2025 GMT
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Da za a kirkiri sabuwar jiha a Najeriya a yanzu, to da dole a samar da karin gwamna daya da sabuwar majalisar dokoki, da sababbin ma’aikatun gwamnati, da sauransu.
Samar da wadannan kuwa abu ne da yake bukatar makudan kudi – akalla Naira biliyan 30 duk shekara.
Ko da jihar za ta iya sama wa kanta kudin shiga kuma, za ta bukaci tallafi daga Gwamnatin Tarayya kafin ta tsaya da kafafunta.
Shin a halin matsin tattalin arzkin da take fuskanta yanzu, Najeriya tana da kudin da za ta reni sababbin jihohi kuwa? NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu DAGA LARABA: Ko Kare Kai Daga Harin ‘Yan Ta’adda Zai Kawo Karshen Matsalar Tsaro?
Shirin Najeriya a Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne a kan abin da kirkirar sababbin jihohi a Najeriya yake nufi ta fuskar tattalin arziki.
Domin sauke shirin, latsa nan
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Kirkirar sabbin jihohi
এছাড়াও পড়ুন:
Mu Tuna Da Jinin Da Aka Zubar Don Kiyaye Hasken Da Muke Da Shi Yanzu
A cikin fim din “Dead to Rights”, an ce, “Mu tuna da jinin da aka zubar a yakin, don mu kiyaye hasken da muke da shi yanzu.” Abin haka yake, yau mun waiwayi abubuwan da suka faru a tarihi, ba don neman ci gaba da kiyaya da juna ba, a maimakon hakan, muna son kira ga al’ummomin duniya da su tsaya tsayin daka a kan kiyaye zaman lafiya da magance yaki a tsakaninsu.
Yakin duniya na biyu babbar masifa ce ga dan Adam, kuma irin ra’ayi da ake rike da shi game da tarihin yakin, ya zama wata jarrabawa ga dan Adam. A bana ake cika shekaru 80 da al’ummar Sinawa suka samu nasarar yaki da mahara Japanawa, da ma kasashen duniya suka samu nasarar yaki da ‘yan Fascist, kuma rike ra’ayi madaidaici game da tarihin yakin duniya na biyu a daidai wannan lokaci, yana da ma’ana ta musamman ga kasashen duniya, musamman a yayin da ake fuskantar rikice-rikice da zaman dar dar a duniya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp