Tottenham Da West Ham Sun Nuna Sha’awar Daukar Dan Wasan Nijeriya Raphael Onyedika
Published: 21st, June 2025 GMT
Manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai Tottenham Hotspur da West Ham United na fafatawa wajen ganin sun dauki tauraron dan wasan Nijeriya dake buga kwallo a Club Brugge, Raphael Onyedika, ana alakanta Onyedika da barin kungiyar Club Brugge sakamakon rawar gani da ya taka a bana.
Dan wasan na Nijeriya ya samu dimbin masu sha’awar raba shi da Brugge saboda bajintar da ya nuna a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai ta bara, a cewar Transferfeed, kungiyoyin biyu na son siyan dan wasan tsakiyar a wannan bazarar, West Ham na son ya maye gurbin Tomas Soucek dan kasar Czech, wanda ke kan hanyarsa ta barin kungiyar.
A daya bangaren kuma kungiyar Tottenham na son kara yawan yan wasanta na tsakiya bayan ta kare a mataki na 16 a gasar Firimiya a kakar wasan da ta gabata, hakazalika babbar kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ta nuna sha’awarta ta sayen dan wasan mai shekaru 24, kadan ya rage Onyedika ya bar Brugge zuwa kungiyar Galatasaray ta Turkiyya a bazarar da ta gabata amma kuma sai ya ci gaba da zama a kungiyar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ƴan matan Najeriya Sun Lashe Gasar Kwallon Kwando Ta Afirka
Tawagar ƴan wasan kwando na matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon kwando ta Afirka karo biyar a jere, lamarin da ya sa ta kafar tarihin wannan bajinta a Afirka.
Tawagar D’Tigress ta samu nasara ne a wasan ƙarshe bayan doke Mali da ci 78-64 domin ɗaukar kofin gasar karo na bakwai a tarihi.
Ƴan wasan Najeriyar sun kankane gasar ƙwallon kwandon Afirka, inda suka yi nasara sau 29 a jere a duka wasan da suka buga ba tare da rashin nasara ba tun 2015.
Nasarar D’Tigress na zuwa ne kimanin mako guda bayan da tawagar Super Falcons ta ƴan wasan ƙwallon kafar matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon ƙafar matan Afirka, karo na 10 a tarihi.