Aminiya:
2025-08-07@08:14:14 GMT

Bio ya maye gurbin Tinubu a matsayin sabon shugaban ECOWAS

Published: 23rd, June 2025 GMT

Shugaban Ƙasar Saliyo, Julius Maada Bio, ya zama sabon shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arziƙin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), inda ya karɓi ragamar shugabancin daga Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

An sanar da hakan ne a taron shugabannin ECOWAS karo na 67 da aka gudanar a Abuja.

An kashe matar aure, manomi ya jikkata a wani sabon hari a Kaduna ’Yan bindiga sun sace babban alƙali a Bayelsa 

Shugaba Tinubu, wanda ya yi wa’adin shugabancin ƙungiyar sau biyu tun daga shekarar 2023, ya bayyana cewa shugabancin ECOWAS babban abu ne a rayuwarsa.

Ya ce: “Yayin da nake miƙa ragamar shugabanci ga abokina kuma ɗan uwana, Shugaba Julius Maada Bio, ina mai gamsuwa da fatan alheri ga makomar Yammacin Afirka.”

Ya ƙara da cewa wajibi ne ƙasashen yankin su haɗa kai wajen tabbatar da zaman lafiya, ci gaban dimokuraɗiyya da kuma bunƙasa tattalin arziƙi.

“Mu ƙara inganta haɗin kai, mu mutunta ƙa’idojin diflomasiyya, sannan mu tabbatar da ci gaba wanda zai haɗa kowa da kowa musamman matasa, mata da waɗanda ke cikin mawuyacin hali,” in ji Tinubu.

A jawabinsa na karɓar shugabanci, Shugaba Bio ya gode wa Tinubu bisa jagoranci mai cike da hangen nesa da kyakkyawan fata.

Ya ce: “Shugabancinka a ECOWAS ya nuna jajircewa wajen ƙarfafa tattaunawar yankin, farfaɗo da tattalin arziƙi da wanzar da zaman lafiya.

“Na ji kaina a matsayin mai ɗaukar wannan nauyi domin ci gaba daga inda ka tsaya.”

Shugaba Bio ya bayyana cewa akwai buƙatar ECOWAS ta ƙara dagewa wajen kare dimokuraɗiyya, inganta tsaro da bunƙasa tattalin arziƙi.

“Dole mu sake fasalin ECOWAS ta yadda za ta zama mai gaskiya, inganci da amsa buƙatun al’ummarta,” in ji shi.

Ya kuma bayyana matsalolin da yankin ke fuskanta kamar ta’addanci, taɓarɓarewar siyasa da matsin tattalin arziki.

Ya ce: “Fagen dimokuraɗiyya yana fuskantar ƙalubale a sassa daban-daban na yankin. A wasu ƙasashe, tsarin mulki ya rikiɗe.

“Amma matasa na faɗin Yammacin Afirka na buƙatar ba kawai zaɓe ba, har ma da gaskiya, da ba su damar shiga cikin tafiyar da rayuwar ƙasa.”

Hakazalika, Bio ya ce zai yi jagoranci ECOWAS cikin gaskiya da fifita buƙatun al’umma tare da inganta haɗin kan yankin.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ECOWAS

এছাড়াও পড়ুন:

Yadda sabbin takunkuman Trump za su shafi tattalin arziƙin duniya

Shugaban Amurka, Donald Trump, yana shirin ƙara tsaurara wa Rasha takunkumi idan har ba a cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ba kafin ranar Juma’a, 8 ga watan Agusta.

Ko da yake Rasha ita ce ƙasar da aka fi ƙaƙaba wa takunkumi a duniya, har yanzu tana amfani da arziƙin man fetur da iskar gas da ta ke da su domin ɗaukar nauyin yaƙin da ta ke yi da Ukraine.

Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCC NAJERIYA A YAU: Mummunan Tasirin Rashin Bambance Zazzabin Lassa Kan Lafiyar Al’umma

Trump ya bayyana cewa zai sanya sabbin takunkuman da za su hana Rasha cin gajiyar kasuwanci da wasu ƙasashe.

Daga cikin matakan, akwai sanya haraji har kashi 100 a kan kayan da ake shigowa da su Amurka daga ƙasashen da ke kasuwanci da Rasha.

Rasha na samun kuɗaɗen shiga da yawa daga fitar da man fetur da iskar gas.

China, Indiya, da Turkiyya na daga cikin ƙasashen da suka fi sayen waɗannan kayayyaki daga Rasha.

Trump ya ce: “Ina amfani da kasuwanci a fannoni da dama, amma mafi amfani da shi, shi ne wajen kawo ƙarshen yaƙi.”

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Yadda sabbin takunkuman Trump za su shafi tattalin arziƙin duniya
  • Kasar Sin Ta Bayyana Adawa Da Ziyarar Boris Johnson A Taiwan
  • Tinubu Ya Umurci A Bada Kulawar Lafiya Kyauta Ga Tsofaffin Ma’aikata Masu Karamin Fansho
  • Tinubu ya taya ’yan matan Yobe da suka lashe gasa a Ingila murna
  • Shugaban ‘Yan Bindiga A Zamfara, Bello Turji, Ya Ajiye Makamai, Ya Saki Mutane 32
  • Xizang Ya Cimma Nasarorin Tattalin Arziki Da Zamantakewa Da Suka Kafa Tarihi Cikin Shekaru Fiye Da 60
  • Afirka ta Kudu ta zayyana matakan tallafi ga ‘yan kasuwa na cikin gida a matsayin martani ga harajin Trump
  • Rundunar PLA Ta Yi Sintiri A Yankin Tekun Kudancin Sin Cikin Shirin Ko Ta-Kwana
  • Gwamna Buni Ya Bukaci Sabon Sarkin Gudi Ya Jagoranci Zaman Lafiya, Hadin Kai, Da Ci Gaban Kasa
  • Ƴan matan Najeriya Sun Lashe Gasar Kwallon Kwando Ta Afirka