Aminiya:
2025-12-01@15:22:21 GMT

Mutum 2 sun mutu a ƙoƙarin ciro waya daga masai a Kano

Published: 23rd, June 2025 GMT

Wasu mutum biyu sun rasu a cikin masai a yayin da suke ƙoƙarin ciro wata ƙaramar waya da ta faɗa a ciki shaddar a yankin Ƙaramar Hukumar Albashi ta Jihar Kano.

Hukumar kashe gobara ta jihar ta ce mutanen biyu sun gamu da ajalinsu ne a ranar Asabar a unguwar Bazabe da ke ƙaramar hukumar.

Kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya sanar cewa a safiyar ranar Asabar ne aka sanar da ofishin kwana-kwana ta samu kiran gaggawa game da lamarin.

Ya bayyana cewa wani ɗan shekara 40 ya shiga masai domin ciro wayarsa da ta faɗa a ciki, amma sai ya maƙale a ciki.

A sakamakon wani mai suna Ibrahim ya shiga domin ciro shi, amma bayan ya yi nasarar sanya masa igiya, sai shi ma ya yanke jiki ya fadi a ciki.

Daga baya hukumar ta yi nasarar fito da su ta kai asibiti inda aka tabbatar cewa sun rasu.

Hukumar ta mika gawarwakinsu ga Babban Ofishin ’Yan Sanda da ke Ƙaramar Hukumar Albasu domin ci gaba bincike da sauran abubuwan da suka dace.

Daga ƙarshe Hukumar ta buƙaci jama’a da su daina jefa kansu a cikin haɗari su rika neman taimako daga ƙararru a duk lokacin da wani abu na gaggawa ya taso.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: waya

এছাড়াও পড়ুন:

Sarakuna sun goyi bayan Gwamnatin Gombe kan yaƙi da cin zarafin mata

Ma’aikatar Mata da Walwalar Jama’a ta Jihar Gombe ƙarƙashin Kwamishina, Asma’u Muhammad Iganus, ta ziyarci masarautun Nafada da Funakaye domin ƙaddamar da kwamitocin yaƙi da cin zarafi ga mata da yara.

A ziyarar ta farko a Masarautar Nafada, Kwamishiniyar ta ce alƙaluma sun nuna cewa cin zarafi ya kai kashi 87.46 a jihar.

Gwamnatin Kano ta nemi a binciki Ganduje kan zargin kalaman ta da hankali Yadda mutane suka yi cikar ƙwari don halartar jana’izar Sheikh Dahiru Bauchi

Ta ce ya ce ya zama dole a haɗa kai da sarakunan gargajiya don kawar da matsalar.

Sarkin Nafada, Alhaji Muhammad Dadum Hamza, ya yi tir da yawaitar laifukan aikata fyaɗe a yankin.

Ya bayyana cewa babu wani gurbi da mai laifin aikata fyaɗe zai samu mafaka.

Ya ce za su tabbatar da an hukunta duk wanda aka kama, tare da goyon bayan ƙarin hukuncin ɗaurin sama da shekaru 14 da doka ke yi a yanzu.

A Masarautar Funakaye, Sarkin Funakaye, Alhaji Yakubu Muhammad Kwairanga IV, ya nuna cikakken goyon bayansa ga matakin gwamnati.

Ya ce ba za a yi wa masu aikata fyaɗe sassauci ba, domin hukunci mai tsanani shi ne zai rage aikata laifin.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Funakaye, Alhaji Abdurrahman Shua’ibu Adam, ya tabbatar da cewa za su ci gaba da aiki tare da ma’aikatar domin kare mata da yara.

Kwamishiniyar, ta miƙa kundin Dokar VAPP ga masarautar Funakaye domin fara aiki da shi kai-tsaye.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • ’Yan sanda sun gano zinaren N23m bayan shekara 12 da ɓacewarsu a Borno
  • Jihar Jigawa Ta Mayar da Rarar Kudi Sama da Naira Miliyan 50 Ga Maniyyatan Aikin Hajjin 2026
  • Mutum 6 sun jikkata a rikici manoma da makiyaya a Jigawa
  • Sojoji sun ceto mutum 7 da ’yan bindiga suka sace a Kano
  • ’Yan bindiga sun kashe tsohuwa, sun sace mutum 3 a Kano
  • Iran ta bayyana halin da Falasdinawa ke ciki da rauni mufi da aka wa dan adam a doron kasa
  • An sake zabar Eto’o a matsayin Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Kamaru  
  • Kuɗin Cizo ya tilasta rufe fitacciyar sinima a Faransa
  • Sarakuna sun goyi bayan Gwamnatin Gombe kan yaƙi da cin zarafin mata
  • CAF ta ƙara yawan ’yan wasan ƙasashe zuwa 28 a gasar nahiyar Afrika