Iyalan Kanawa da aka kashe a Uromi sun zargin gwamnati da yin watsi da su
Published: 24th, June 2025 GMT
Iyalan mafarauta 16 ’yan Jihar Kano da aka yi wa kisan gilla a garin Uromi da ke Jihar Edo sun yi zargin cewa gwamnati ta yi watsi da su.
Wasu daga cikin waɗanda suka tsallake rijiya da baya a harin da kuma iyalan waɗanda aka kashe, sun bayyana cewa alƙawarin kuɗin magani da tallafi da kuma diyya fa gwamnatocin jihohin Edo da Kano suka yi musu bai wuce fatar baki ba.
Ayarin farautan sun baro garin Fatakwal na Nijar Ribas ne, a hanyarsu ta komawa gida domin bikin Ƙaramar Sallah, amma wasu ’yan banga a Uromi suka tare su, suka yi musu kisan gilla.
Akasarin mafarautan sun fito ne daga yankin Toronkawa da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure ta Jihar Kano, tare da abokansu daga ƙananan hukumomin Garko da Kibiya da Rano.
Iran da Isra’ila sun amince da tsagaita wuta —Trump NAJERIYA A YAU: Dabarun Samun Kuɗaɗe Ta Hanyar Amfani Da Wayar Hannu’Yan kaɗan daga cikinsu ne suka sha da ƙyar a harin na Uromi na ranar 28 ga watan Maris, wanda ya sha tofin Allah-tsine daga ɓangarori daban-daban.
’Yan sanda sun bayyana cewa sun kama mutum 14 bisa zargin hannunsu a harin, a yayin da gwamnatocin jihohin Kano da kuma inda abin ya faru, suka yi alƙawarin ɗaukat matakan da suka dace na tallafi ga waɗanda abin ya shafa da iyalansu da kuma tabbatar da cewa an hukunta masu laifin.
A watan Afrilu Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya sanar da kafa kwamitin bincike na haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya kan lamarin.
Gwamna Okpebholo ya sanar da haka ne bayan mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdulsalam Gwarzo, ya jagoranci jami’an gwamnatin Kano suka yi takakkiya zuwa Edo bayan kisan da aka yi wa Kanawan.
Daga bisani Okpebholo ya kai ziyarar ta’aziyya Kano, inda ya yi alƙawarin biyan diyya ga iyalan mamatan da kuma majinyatan da harin ya shafa.
A nasa jawabin Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda ya jagoranci Okpebholo zuwa garin Toronkawa, ya jaddada cewa gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an biya cikakken diyya ga iyalan. Ya kuma yi musu alƙawarin tallafi na kuɗaɗe da kayan abinci.
Gwamnatocin Kano da Edo sun yi gumAminiya ta tuntuɓi Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano, Ibrahim Garba Waiya, wanda kuma mamba ne a kwamitin binciken, kan dalilin rashin cika alƙawuran da gwamnatin jihar ta yi wa mutanen da abin ya shafa, amma ya ƙi cewa komai.
Haka shi ma Kwamishinan Jihar Edo, Paul Ohonbamu da Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan jihar, Free Itua, ba su amsa kiranmu ba ko rubutattun tambayoyin da aka tura musu.
Wakilinmu ya tuntuɓi shugaban al’ummar Hausawa a Jihar Edo, Alhaji Badamasi Saleh, amma ya bayyana cewa ba shi da masaniya game da ko gwamnatin jihar ta biya diyyar da ta yi wa mutanen alƙawari.
Ba a cika mana alƙawari baA garin Toronkawa kuma, iyalai da ragowar mafarautan da harin ya shafa sun ce ba a cika alƙawarin ba.
Ɗaya daga cikin mafarautan da ya tsallake rijiya da baya, Ibrahim Isah, ya tabbatar da hakan, inda ya ƙara da cewa, “Yanzu da ƙyar nake iya kula da iyalina. Yarana ’yan ƙanana ne ballantana su tallafa min.
“An yi mana alƙawarin za a kula da mu a asibiti, amma daga aljihuna na kashe kuɗin jinya N40,000, duk da haka ban samu kulawar da ta dace ba.”
Ya ce duk da alƙawarin tallafin abinci da sauransu da Gwamnatin Kano ta yi musu, amma ba su gani a ƙasa. “Sun ce sun kawo mana kuɗi da abinci, amma dai ba mu komai ba.
“Mun je sakatariyar ƙaramar hukuma, aka ce ciyaman ya tafi Saudiyya, amma mataimakinsa ya ce suna aiki a kan lamarin,” a cewar Malaman Ibrahim ɗan shekara 45.
Malama Zahura Haruna, matan ɗaya daga cikin mafarautan da aka kashe, ta ce, “Rayuwa ta yi mana ƙunci, yanzu na zama nauyi ga surukaina, da ma shi ne mai ƙarfin gidan. Yanzu da maƙwabta muka dogara don samun abinci.”
A Ƙaramar Hukumar Kibiya kuma, Malam Bala Dutse, wanda aka kashe ɗansa Ahmadu a harin Ironsi, ya bayyana wa wakilinmu cewa ba su ji komai daga ɓangaren gwamnati ba, amma, “aƙalla ya kamata su fito su yi mana bayanin abin da suka tsara yi game da biyan diyyan.”
Wata mai takaba daga cikin matan mafarautan da aka kashe, Hauwa’u Isah, ta ce, “sun yi mana alƙawarin adalci, amma kullum sai ka ga abin kamar kalaman siyasa ne kawai.”
Amma Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar Kibiya, Nasiru Adam Abdulaziz, ya jaddada aniyar ƙaramar hukumar ta mama wa waɗanda abin ya shafa adalci.
Ya ce, “Waɗannan iyalan sun cancanta a yi musu bayani kuma ina da ƙwarin gwiwa cewa gwamnati za ta yi abin da ya dace.”
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: mafarauta Matafiya mafarautan da
এছাড়াও পড়ুন:
Mahara sun kashe ’yan sanda a shingen bincike a Kogi
’Yan bindiga sun kai hari shingen bincike na ’yan sanda a Jihar Kogi, inda suka kashe jami’ai da wani mutum.
Harin farko ya faru da misalin ƙarfe 10:30 na safe a ƙauyen Abugi da ke Ƙaramar Hukumar Lokoja.
Mata 400 sun amfana da kayan haihuwa a Gombe Bayan biyan N50m an sako ma’aurata da ’yarsu su da aka sace a KatsinaMaharan, sun kai harin ne a kan babur, inda suka buɗe wa ’yan sandan da ke bakin aiki wuce.
Wani matashi da ya zo wucewa ta wajen ya rasa ransa.
Bayan haka, maharan sun kwashe bindigogin jami’an sannan suka tsere.
Daga baya, da misalin ƙarfe 11 na safe, suka sake kai wani hari a shingen da ke kan hanyar Ilafin, Isanlu a Ƙaramar Hukumar Yagba ta Gabas, inda suka kashe wasu ’yan sanda biyu na rundunar MOPOL 70.
Mutanen yankin sun ce wannan hari ya jefa su cikin tsoro, suna ganin cewa maharan na neman bindigogi ne domin su ci gaba da kai hare-hare.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Yagba ta Gabas, Dokta Joshua Dare, ya yi Allah-wadai da hare-haren.
Ya bayyana harin a matsayin barazana ga zaman lafiya da tsaron jihar.
Ba wannan ne karo na farko da irin wannan hari ya auku ba.
A ranar 9 ga watan Satumba, an kashe jami’an tsaro guda biyar; ciki har da ’yan sanda uku da ’yan banga biyu, a wani hari kwanton ɓauna da aka kai musu a yankin Egbe da ke Ƙaramar Hukumar Yagba ta Yamma.
Gwamnatin Jihar Kogi, a baya-bayan nan ta zargi wasu matasa da taimaka wa ’yan bindiga a yankin, inda ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauke su a matsayin ’yan ta’adda.
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP William Aya, bai ce komai game da sabon harin ba, har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.