Kasar Sin Na Fatan Isra’ila Da Iran Za Su Tsagaita Bude Wuta Nan Bada Jimawa Ba
Published: 25th, June 2025 GMT
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya bayyana matukar damuwar da Sin ke da ita dangane yanayin da yankin Gabas ta Tsakiya ke ciki, tare da bayyana fatan ganin an tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Iran nan bada jimawa ba.
Guo Jiakun ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai na yau Talata, lokacin da yake tsokaci game da rahotannin dake cewa shugaban Amurka Donald Trump, ya sanar da cewa an cimma cikakkiyar yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Isra’ila da Iran.
Kakakin ya kuma nanata cewa shaidu sun riga sun nuna cewa, matakan soji ba za su kawo zaman lafiya mai dorewa ba, kuma yarjejeniya da tattaunawa su ne kadai hanyoyin warware rikice-rikice.
Ya kara da cewa, Sin na kira ga bangarori masu ruwa da tsaki su bi tafarkin da ya dace na warware matsalar a siyasance nan bada jimawa ba. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Mallaki Kusan Tashoshin Fasahar 5G Miliyan 4.65
Yawan tashoshin fasahar sadarwa ta 5G a kasar Sin ya kai kusan miliyan 4.65 a karshen watan Agusta, kamar yadda alkaluman mahukunta suka nuna a yau Talata.
A cewar ma’aikatar masana’antu da fasahar sadarwa ta kasar Sin, adadin ya kai kashi 36.3 na adadin tashoshin sadarwar wayar hannu a fadin kasar baki daya.
A halin yanzu, ana samun karuwar masu wayar salula a kasar Sin da ke rungumar amfani da fasahohin sadarwa na 5G.
Alkaluman da aka fitar zuwa karshen watan Agusta sun nuna cewa, yawan masu amfani da wayar salula na manyan kamfanonin sadarwa uku da kuma kamfanin China Broadnet ya kai kimanin biliyan 1.82. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp