Ƙasar Iran ta bayyana shirinta na shiga tattaunawar sasantawa “idan aka tsagaita hare-hare”, kamar yadda ministan harkokin wajen ƙasar ya bayyana bayan ganawa da takwarorinsa daga Faransa, Burtaniya da Jamus.  

Yayin da ministocin Turai suka nuna sha’awar ci gaba da tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran, Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna shakku kan yiwuwar nasara, yana mai cewa Iran tana son magana kai tsaye da Amurka.

Hakan ya faru ne a lokacin da rikici tsakanin Iran da Isra’ila ke ci gaba, inda Isra’ila ta kai hari kan wasu wurare a Tehran, kuma Iran ta mayar da martani da harin makamai.

Fadar White House ta bayyana cewa Trump zai yanke shawara cikin makonni biyu kan ko Amurka za ta ɗauki mataki kai tsaye a rikicin.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Iran Isra ila Turai

এছাড়াও পড়ুন:

Amurka Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Zuwa Ƙasarta Domin Haihuwa

Gargaɗin ya yi daidai da irin wannan sanarwar da ofisoshin jakadancin Amurka a Jamaica da Uganda suka fitar kwanan nan, a wani ɓangare na yaƙi da dabi’ar karya ƙa’ida shige da fice. 

A cikin watan Janairun 2025, hukumomin Amurka sun sake jaddada aniyarsu na ƙarfafa ikon kula da iyakoki kan yin amfani da damar zama dan ƙasa ta haihuwa.

A farkon wannan shekara, shugaban ƙasar ɗonald Trump ya sake nanata matsayinsa na cewa yaran da aka haifa a Amurka ga baƙin haure ba su da takardun zama ƴan ƙasa kai tsaye.

A bisa dokar da aka yi wa kwaskwarima na Amurka kan shaidar zama dan ƙasa, ta fayyace cewa duk wani jaririn da aka haifa sai an duba matakin damar zaman iyayensa a ƙasar kafin a amince da shaidar zamansa dan ƙasar ko akasin hakan, inda jami’an suka ce ba za a amincewa da wadanda suka shiga ƙasar kawai don an ba su biza ba.  

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An Zargin Akantan jihar Nasarawa Da Shiga Harkokin Siyasa
  • Mu daina zagin malaman addini idan muna son zaman lafiya — Uba Sani
  • Ministan Harkokin Wajen Kasar Iran Ya Jinjinawa Al’ummar Iran Kan Namijin Kokarinsu
  • Kasar Iran Ko Da Zata Sake Tattaunawa Da Amurka Zata Kasance Dauke Da Makamai Cikin Shirin
  • Rahotonni Sun Bayyana Cewa; Agajin Jin kai Da Ake Wurga Ta Sama A Gaza Tamkar Digon Ruwa Ne
  • Son Zai Bar Tottenham Zuwa Amurka Bayan Shafe Shekaru 10 A Ingila
  • Manoma Sun Caccaki Tinubu Kan Ƙarfafa Shigo Da Shinkafa Da Masara Daga Ƙasashen Waje
  • Amurka Ta Gargaɗi Ƴan Nijeriya Kan Zuwa Ƙasarta Domin Haihuwa
  • Kungiyar Hamas Ta Bayyana Cewa Ba za ta Ajiye Makamanta ba Sai Bayan samar Da Kasar falasdinu
  • Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji