Matashi ya yi wa maraya ɗan shekara 10 kisan gilla a Zariya
Published: 23rd, June 2025 GMT
Ana zargin wani ɗan shekaru 18 da kashe wani maraya ɗan shekara 10 a yankin Ƙaramar Hukumar Zariya ta Jihar Kaduna.
’Yan sanda sun kama matashin ne kan zargin sa da yi wa ɗan yaron, wanda ɗan baffansa ne, ɗaurin goro tare da azabtar da shi saboda yaron ya ƙi amincewa ya yi lalata da shi.
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da ta gabata a unguwar Iyan Juma da ke Karamar Hukumar Zariya.
Mahaifiyar marigayin mai suna Asama’u Mohammed ta shaida wa Aminiya cewa, “Na dawo wajen aikatau kamar yadda na saba yi don na samo abin da zan ba su su ci tare da ’yan uwansa, sai ga yayansa ya shigo a guje ya ce ga Idris can a kwance cikin jini kuma fuskarsa a kumbure, wai sun yi faɗa da wani duk an ji mishi ciwo, nan da nan na yafa hijabi ni da ɗan uwar gidana muka tafi inda yake.”
Mahaifiyar Babban Editan jaridar Daily Trust ta rasu Koriya ta Arewa za ta taimaka da gyara tashoshin nukiliyan Iran —MasaniAminiya ta garzaya Babban Ofishin ’yan sanda da ke Ƙofar Fada cikin birnin Zariya domin ji daga bakin babban jima’i, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya shaida wa wakilinmu, cewa sun tattara bayanai yadda lamarin ya kasance kuma sun tura zuwa babban ofishinsu da ke Kaduna
Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna DSP Mansur Hassan ya tabbatar wa wakilin namu da faruwar lamarin, da kama wanda da ake zargi.
Ya ƙara da cewa bayan sun kammala bincike za su tora zuwa kuto.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
An kama ɗan sandan bogi a Kano
Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta sanar da cafke wani mutum da ke yi mata sojan-gona yana yaudarar jama’a domin karɓar musu kuɗi.
An cafke wanda ake zargin ne a ranar Lahadi, 21 ga Satumbar 2025 a yankin Kofar Dawanau, sanye da kayan ’yan sanda, wanda bayanai suka ce ya daɗe yana aika-aikar.
An yi wa sojoji ɗaurin rai da rai kan sayar wa ’yan ta’adda makamai a Borno Sanata Natasha ta koma Majalisar DattawaSanawar da rundunar ta fitar ta bayyana cewe an kama shi ne bayan da jama’a suka shigar da ƙorafe-ƙorafe da dama game da ayyukan wasu da ke yin kutse da shigar ’yan sanda domin damfarar jama’a.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce “binciken farko ya tabbatar cewa wanda ake zargin ba ɗan sanda ba ne, kuma ba shi da alaƙa da rundunar kwata-kwata.”
A wata hira da rundunar ta yi da mutumin wanda mazaunin Kofar Waika ne, ya ce sha’awar aikin ce ta sanya yake yi wa ’yan sandan sojan gona, inda yake bayar da hannu a kan titi domin samun na ɓatarwa.
Ya shaida cewa shaye-shayen da yake yi bai wuce na sigari da tabar wiwi ba, inda ya nemi a yi masa afuwa duk da ya nanata cewa duk duniya babu aikin da yake sha’awa kamar aikin ’yan sanda tare da neman a taimaka a dauke shi aikin.
Kazalika, ya bayyana cewa muradin ganin ya zama ɗan ya sanya shi sake aikata wannan laifi na sojan-gona duk da an taɓa kama shi da laifin a baya.
Tuni dai rundunar ta bayyana cewa za a gurfanar da shi a gaban kotu domin fuskantar hukunci bayan kammala bincike.
Kwamishinan ‘Yan Sandan jihar, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai ko ƙorafe-ƙorafe idan sun san wani abu game da wanda ake zargi ko makamantansa.