Mahara sun kashe ’yan ɗaurin aure 12 daga Zariya a Filato
Published: 21st, June 2025 GMT
An yi wa wasu matafiya ɗaurin aure 12 kisan gilla bayan wasu mutane sun kai musu hari a yankin Mangu ta Jihar Filato sun kai musu hari.
Rahotanni sun bayyana cewa mutum 11 daga cikin matafiya suna samun kulawa a asibiti, bayan raunukan da suka samu a harin da aka kai musu a yankin Ƙaramar Hukumar Mangu a ranar Juma’a.                
      
				
Aminiya ta samu labarin cewar an kai wa matafiya hari ne da misalin ƙarfe 8 na dare, a lokacin da su mutum 31, ciki har da mata da ƙananan yara, a cikin wata bas mallakin Jami’ar Ahmadu Bello (ABU) ta Zariya.
Ayarin ’yan daurin auren da aka kai wa harin sun fito ne daga yankin Basawa da ke Zariya a Jihar Kaduna, lokacin da maharan suka tare su a kusa da yankin Ƙaramar Hukumar Qu’an Pan, suka kashe mutum 12, ciki har da direban motar, wanda ma’aikacin jami’ar ne.
Najeriya ta tura sojoji domin samar da zaman lafiya a Gambia Yadda Iran ta lalata cibiyar kimiyya mafi muhimmanci a Isra’ilaBabban Limamin Masallacin Juma’a na Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), da ke Mangu, Sheikh Suleiman Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin, da cewa an ajiye gawarwakin a Babban Asibitin Mangu.
Sheikh Suleiman Haruna, ya ce, “Matafiya 31 ne a motar. Mun samu gawarwakin mutum takwas, amma mun roƙi jami’an tsaro su taimaka wajen kawo ragowar gawarwaki huɗu da suka rage.
“Muna tare da Shugaban Ƙaramar Hukumar Mangu kuma yana iya bakin ƙoƙarinsa a kan lamarin.”
Wani wanda ya tsallake rijiya da baya a harin, Ibrahim Umar, ya ce, “Mun kusa kaiwa Qu’an Pan bikin ɗaurin auren ɗan uwanmu, amma muka yi ɓatan kai saboda ba mu san hanyar ba.
“Mun tsaya tambayar wasu mutane kwatance, kafin mu farga har sun yi mana ƙawanya sun zagaye motar ta kowace kusurwa, suna ihu cewa a kashe mu, mu Hausawa ne.
“Daga nan suka fara duka suna kawo mana hari da muggan makamai. Direban suka fara kashewa kafin sauranmu, suka ƙona motar da gawarwakin mutane a ciki. Yanzu muna asibiti ana jinyar mu.”
Wakilimmu ya tuntuɓi kakakin ’yan sanda na Jihar Filato, DSP Alfred Altau, kuma jami’in ya shaida masa cewa yana sane da lamarin, amma sai nan gaba zai fitar da sanarwa a hukumance bayan tantance haƙiƙanin abin da ya faru.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ɗaurin Aure mahara Matafiya
এছাড়াও পড়ুন:
Al’ummar Kauru Sun Koka Game Da Karuwar Hare-hare Da Ke Barazana Ga Gonaki Da Rayuka
Daga Yusuf Zubairu Kauru
Al’ummar Karamar Hukumar Kauru ta Jihar Kaduna sun shiga halin kaka-ni-ka-yi duba da yadda rayukansu ke kasancewa cikin hadari yayin da suke gonakinsu.
A wata tattaunawa ta wayar tarho, wani jagoran matasa, Junaidu Ishaq, ya bayyana cewa kusan shekaru biyar ke nan da hare-haren ’yan bindiga ke ta faruwa akai-akai, wanda ya bar al’umma cikin fargaba da ƙuncin rayuwa.
Ya ce manoma suna shiga gonakinsu ne cike da fargaba domin komi na iya faruwa yayin da suke aiki a gonakin.
Mazauna yankin sun bayyana cewa Kauru, wadda aka fi sani da yawan gonaki da ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da abinci a jihar Kaduna, yanzu manoma ba sa iya shiga gonakinsu cikin kwanciyar hankali saboda yadda ‘yan bindiga ke yawan kai musu hare-hare.
A koda yaushe iyayen yara suna fargaba kada ‘ya’yansu su yi nesa da su, yayin da iyalai da dama da ke fama da ƙangin talauci ke kara shiga cikin matsanancin hali.
Sun yi kira gwamnati da hukumomin tsaro su yi gaggawar kai ɗauki wanda zai bai wa manoman karkara kwarin gwiwa, waɗanda su ne ginshiƙin samar da abinci a yankin.
Mazaunan sun yi gargadin cewa idan ba a ɗauki mataki cikin gaggawa ba, hare-haren na iya haifar da ƙaruwar matsalar rashin abinci da yawaitar ƙaura daga yankin.
“Idan zuwa gona zai sa mutumya rasa ransa, to lalle akwai babban matsala,” in ji wani manomi a yankin.
Sun yi fatan cewa za a dawo da zaman lafiya a yankin, yadda ƙasar da Allah Ya albarkace su da ita za ta ci gaba da ciyar da al’ummar Kauru ba wurin binne su ba.