Leadership News Hausa:
2025-08-07@08:18:22 GMT

Rashford Na Fatan Buga Ƙwallo Tare Da Lamine Yamal A Barcelona

Published: 22nd, June 2025 GMT

Rashford Na Fatan Buga Ƙwallo Tare Da Lamine Yamal A Barcelona

Ɗan wasan gaban Manchester United Marcus Rashford ya ce zai so ya taka leda tare da matashin ɗan wasa Lamine Yamal a Barcelona, Rashford mai shekaru 27, wanda ya shafe rabin kakar wasan bara ya na zaman aro a Aston Villa, a halin yanzu yana atisayen ƙara kuzari a ƙasar Sifaniya kafin a fara wasannin share fage na kulob ɗin, yayin da ake ta raɗe raɗin makomarsa a United.

Lokacin da aka tambaye shi game da yiwuwar yin wasa tare da Yamal, Rashford ya ce: “E, tabbas, kowa yana so ya yi wasa tare da mafi kyawun dan wasa, don haka nima inada wannan burin kuma zamu gani, Yamal, mai shekaru 17, ya taka rawar gani sosai yayin da Barcelona ta lashe kofuna uku a bana, kuma ta kai wasan kusa da na karshe a gasar zakarun Turai, hakazalika ya kuma taka rawar gani a nasarar da kasar Sifen ta samu a Euro 2024.

Shin Rashin Nasara Ya Rage Damar Yamal Na Ballon d’Or? Nico Williams Ya Amince Da Komawa Barcelona Akan Kwantiragin Shekaru 6

Rashford ya ƙara da cewa “Ba kowa ne zai iya yin abinda Yamal yayi a cikin shekaru 16-17 ba, don haka lallai akwai wata baiwa dangane da matashin ɗan wasan, Yana da matuƙar fikira idan ka kalli yadda yake sarrafa kwallo a kafarshi” Inji Rashford, rahotanni a watan Afrilu sun nuna cewa Rashford yana jin cewa da wuya ya sake bugawa Manchester United wasa a karkashin Ruben Amorim.

A watan Disamba ne dan ƙasar Portugal ɗin ya fitar da shi daga cikin tawagar United, kafin ya shafe sauran kakar a Aston Villa a matsayin aro, Daraktan wasanni na Barcelona Deco a baya ya ce kulob din yana son Rashford da Luis Diaz na Liverpool, sai dai duk da sha’awar da kulob din na Catalan ya nuna, kudi na iya zama cikas idan suka yi yunkurin siyan Rashford.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Barcelona Rashford Yamal a Barcelona Rashford ya

এছাড়াও পড়ুন:

WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2025

Hukumar da ke shirya jarabawa kammala karatun sakandire a Afrika ta Yamma (WAEC), ta saki sakamakon jarabawar SSCE na shekarar 2025.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Litinin, 4 ga Agustan 2025, tana mai cewa dukkan ɗaliban da suka zauna jarabawar yanzu za su iya duba sakamakon nasu a shafinta na intanet.

Za a mayar da gidan yarin da ya haura shekara 100 zuwa gidan tarihi a Kano An sace jariri sabuwar haihuwa a asibitin Ekiti

“WAEC na farin cikin sanar da ɗalibai da suka rubuta jarabawar WASSCE a shekarar 2025 cewa an saki sakamakon a hukumance yau Litinin, 4 ga watan Agusta,” in ji sanarwar.

WAEC ta buƙaci ɗalibai da su shiga shafin duba sakamako na hukuma a (http://waecdirect.org) ko (http://waecdirect.org) domin duba sakamakon su ta amfani da bayanan jarabawa da lambobin tantance sakamako wato result checker pins.

A nasa bangaren, shugaban ofishin WAEC na Nijeriya, Amos Dangut, ya bayyana cewa an samu raguwar kashi 33.8 cikin ɗari na sakamako masu kyau idan aka kwatanta da na shekarar 2024.

Da yake zantawa da manema labarai a birnin Legas, Dangut ya ce kashi 72.12 cikin ɗari na ɗaliban da suka samu makin credit ko fiye aƙalla darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi — adadi ne da ya yi kasa da na bara da kusan kashi 34 cikin ɗari.

“A ƙididdigar da muka yi tsakanin sakamakon jarabawar 2024 da na 2025, mun lura cewa an samu raguwar kashi 33.8 cikin ɗari a yawan ɗaliban da suka samu makin credit ko fiye a aƙalla darussa biyar da suka haɗa da Turanci da Lissafi,” in ji shi.

Aminiya ta rawaito cewa wannan dai na zuwa ne bayan ɗalibai da iyaye da su kansu makarantun sakandare a faɗin ƙasar sun shafe makonni suna dakon fitowar sakamakon jarabawar na bana.

Jimillar ɗalibai 1,973,253 daga makarantu 23,554 da aka amince da su ne suka zauna jarabawar bana.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • An shafe wata 8 ana mulki babu mataimakin gwamna a Taraba
  • An shafe wata 8 ana mulki babu mataimakin gwamna a Tataba
  • Bello Turji Bai Yi Sulhu Da Kowa Ba – Guyawa Isa
  • Batun Ceto Wanda Ake Zargi Da Kwaya: Kwamishinan Kano Ya Yi Murabus
  • Shugaban IWGA: Birnin Chengdu Zai Karbi Bakuncin Gasar Wasanni Mafi Kyau A Tarihi
  • Gwamnatin Tarayya Ta Karrama ‘Yan Wasan Kwallon Kwando Na Mata
  • Rundunar PLA Ta Yi Sintiri A Yankin Tekun Kudancin Sin Cikin Shirin Ko Ta-Kwana
  • WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2025
  • Gwamnatin Kano Ta Karɓi Rahoton Binciken Kwamishinan Sufuri Kan Belin Wanda Ake Zargi Da Safarar Kwayoyi
  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Kauyukan Zamfara