Tun da ka yi karatu a Italiya, yaya kake kwatanta ci gaban Kano, da na wasu biranen zamani da ka sani?

Wannan tambaya ce mai amfani. Birane irin su Milan da Florence da Turin, suna da dogon tarihi a fannin ci gaban birane amma abin da ke bambanta Kano a yanzu shi ne saurin aiki da kuma hangen nesa, kuma wannan gwamnati tana da tsari a fagen.

A matsayina na mai tsara gine-gine, zan iya saurin gano kyakkyawan shiri idan na gan shi. Kuma abin da ke faruwa a Kano ya na da kyau sosai. Ana gabatar da abubuwa masu alaƙa da biranen zamani, wato wuraren shakatawa da sanya fitilun titi da magudanan ruwa da kuma kula da tsarin taswirar gine-gine. Haƙiƙa wannan wata alama ce da take nuna gwamnati ta ƙuduri kawo ci gaba a zahiri.

Wasu suna cewa shekaru biyu ba su isa a auna nasarar gwamnati ba. Mene ne ra’ayinka gane da hakan?

A wannan magana, ban yarda da ita ba. Shekaru biyu ƙarƙashin Injiniya Abba Kabir Yusuf, sun haifar da abubuwan da wasu shugabanni ba su iya yi ba a cikin shekaru takwas da suka yi suna mulki ba. Duk abinda aka gina kan tubali nagari, ba sai an jira dogon lokaci ba za a fara ganin tasirinsa, abin da kawai ake buƙata shi ne jagoranci nagari. Kuma hakan muna da shi a yanzu. Ayyukan da ya yi cikin shekaru biyu ya cancanci a rubuta su cikin tarihi.

Wasu na cewa irin waɗannan shugabanni su na da buƙatar a ba su dama su ci gaba da mulki fiye da iyakar wa’adin da kundin tsarin mulki ya tanada. Me za ka ce akan haka?

Wannan gaɓa ce mai mahimmanci, wanda lokaci ya yi da ya kamata mu sauya yadda muke kallon shugabanci. Idan muna da shugaba mai hangen nesa da bayar da sakamako, kuma wanda ke tafiyar da mulki kan buƙatun al’umma kamar Injiniya Abba Kabir Yusuf, me zai hana a ɗora da ci gaban da yake kawo wa? Da alama kamar muna hukunta nasara ne idan muka taƙaita irin wannan shugaba zuwa wa’adi biyu wato “4+4”. Irin waɗannan shugabanni misali ne ba kawai ga Nijeriya ba, har ma ga nahiyar Afirka da duniya baki ɗaya. Idan akwai buƙatar sauya tsarin mulki don bayar da damar ci gaba da irin wannan jagoranci, to ya dace mu fara tattaunawa a kan haka, don ci gaba bai kamata a katse shi ba saboda al’ada.

A ƙarshe wane saƙo za ka bai wa jama’ar Kano da matasa ‘yan kasuwa irinka?

Ga jama’ar Kano, wannan lokacinmu ne da za mu tallafa wa wannan jagoranci mai hangen nesa ta hanyar bayar da gudummawa wajen ɗaukar nauyin ci gaban da ke faruwa a garuruwan mu. Ga matasa ‘yan kasuwa kuma ku duba Kano yanzu. Dama tana bayyana a ɓangarori daban-daban daga gine-gine, da fasahar zamani (IT), da masana’antu, har ma da yawon buɗe ido. Lokaci ne da ya dace mu fara tunani mai zurfi, tare da shirin ƙara jajircewa don bayar da gudummawa wajen gina sabuwar Kano.

Gwamna na cika shekaru biyu a mulki, mene ne saƙonka na ƙarshe?

A ƙarshe, ina mika gaisuwa ta musamman ga mai girma gwamna, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa cikarsa shekaru biyu kan karagar shugabanci nagari. Haƙiƙa ya nuna mana yadda salon jagoranci nagari ya ke, tare da yadda ake fifita muradun jama’a a tsarin shugabanci, muna miƙa saƙon gaisuwa tare da nuna alfahari da shi.

Gwamnan Kano, Abba K. Yusuf tare da Arch. Ali Hassan yayin wani taro a fadar gwamnatin Kano.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Arch Ali Hassan Tsara Birane shekaru biyu

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Ɓullar Cutar Mpox A Jihar

Ya ce Kano na cikin hatsari saboda cunkoson jama’a da kuma zirga-zirgar mutane daga wurare daban-daban.

KNCDC ta gudanar da cikakken bincike a Ungogo, inda aka duba unguwar da marar lafiyan yake da kuma asibitocin da ya ziyarta.

Duk wanda aka bincika yana cikin ƙoshin lafiya kuma babu wanda ya kamu da cutar.

Farfesa Abbas ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a don hana yaɗuwar cututtuka.

Ya nemi kafafen watsa labarai su ci gaba da yaɗa bayanan lafiya ga al’umma.

Ya kuma buƙaci jama’a su kasance masu lura, inda ya tabbatar da cewa Kano tana da tsarin sa ido da shiri don shawo kan kowace irin cuta nan gaba.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tarihi da rayuwar Sheikh Abdulaziz Al-Sheikh (1943-2025)
  • Wa’adin Mulki Ɗaya Kacal Za Ka Yi — ADC Ga Tinubu
  • An Kama Ɗansandan Bogi A Kano
  • Xi Jinping Zai Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 70 Da Kafuwar Yankin Xinjiang Na Uygur Mai Cin Gashin Kansa
  • Gwamnatin Kano Ta Tabbatar Da Ɓullar Cutar Mpox A Jihar
  • Taron Canada: Haɗin Gwiwa Afirka Ke Buƙata Ba Agaji Ba – Gwamnan Zamfara 
  • Kasar Sin Za Ta Shirya Taron Mata Na Duniya A Beijing Yayin Cika Shekaru 30 Da Taron Mata Na 1995
  • Sarkin Ruman Katsina ya rasu
  • Gwamnan Gombe ya bai wa maharba kyautar motoci da babura don bunƙasa tsaro
  • Babu Wanda Ya Jawo Ra’ayina  Zuwa Masana’antar Kannywood —Umar Hassan (2)