Aminiya:
2025-08-10@17:50:53 GMT

Ba zan yi Tinubu ba a 2027 matukar ya canza Kashim Shettima – Sheik Jingir

Published: 26th, June 2025 GMT

Shugaban Majalisar Malamai na kungiyar Jama’atul Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheik Sani Yahaya Jingir, ya ce ba zai goyi bayan takarar Bola Tinubu ba a zaben 2027 matukar ya canza Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa.

Ya bayyana hakan ne yayin wani taron wa’azi a masallacinsa na ’Yan Taya da ke Jos, babban birnin jihar Filato.

Aminiya ta rawaito cewa a zaben 2023 da ya gabata dai Sheikh Jingir ya goyi bayan Tinubu sannan ya umarci magoya bayansa da su ma su yi haka a wancan lokacin.

Gwamnatin Kano ta ba da hutun sabuwar shekarar musulunci Za mu ci gaba da tattaunawa da Iran kan yarjejeniyar nukiliya — Trump

Jita-jitar da ake yadawa dai a kan cewa akwai yiwuwar Tinubu ya ajiye Kashim din a matsayin abokin takararsa a zabe mai zuwa ta dada kamari a ’yan kwanakin nan.

To sai dai da yake nasa tsokacin a kan batun, malamin addinin ya ce, “Na ji akwai wasu mutane marasa kishin kasa daga ciki da wajen APC da ke kokarin lalata alakar da ke tsakanin Tinubu da Kashim domin cimma mummunar manufarsu. To mu ba ma maraba da wannan Shugaba Tinubu.

“Ni da wasu na kusa da ni mun goyi bayan Tinubu da Kashim, kuma za mu sake goyon bayan takararku a tare. Duk wani yunkuri sabanin haka ba na tare da shi kuma ba zan goyi baya ba saboda a baya sun amince su yi aiki tare.

“Na goyi bayansu ba tare da sun ba ni ko sisi ba. duk da yake ina da kusanci da Atiku, amma na ce Tinubu da Kashim zan yi. Akwai jita-jitar da ke yawo cewa dangantaka ta yi tsami a tsakaninsu, amma ni ban yarda da, na fi tunanin aikin makiya ne,” in ji malamin.

Sheikh Jingir ya kuma yi kira ga Shugba Tinubu da kada ya saurari masu kiran nasa da ya ajiye Kashim ya canza shi da wani a 2027, inda ya bayyana wadannan mutanen a matsayin marasa son ci gaba.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno

Dakarun Sojin Najeriya sun kashe wani babban Kwamandan Boko Haram, mai suna Abu Nasr, wanda ya jagoranci kai hari garin Rann, da ke Ƙaramar Hukumar Kala Balge, a Jihar Borno.

A makon da ya gabata, dakarun rundunar Operation Hadin Kai, sun daƙile harin da Boko Haram suka kai garin Rann.

Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi aure Za a biya ma’aikata 445 garatutin sama da biliyan ɗaya a Kebbi

Sun kashe ’yan ta’adda da dama, duk da cewa sojoji biyu sun rasa rayukansu sakamakon harba roka da ‘yan ta’addan suka yi.

Rann na da iyaka da ƙasar Kamaru, kuma daga Maiduguri yana da nisa kusan kilomita 196.

Bayanan jami’an tsaro sun tabbatar cewa Abu Nasr, wanda ya jagoranci tawagarsa zuwa Rann daga Kamaru, ya mutu tare da wasu ’yan ta’addan.

An kuma samu nasarar ƙwato bindigogi, harsasai, bama-baman roka da sauran abubuwan fashewa.

Harin ya faru daga ranar Alhamis, 7 ga watan Agusta, zuwa safiyar Juma’a, 8 ga watan Agusta, 2025, tare da taimakon bayan jiragen sojojin sama.

A cewar jami’an tsaro, an gano gawarwakin ’yan ta’adda bakwai a wajen, kuma akwai yiwuwar sama da hakan sun rasu.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shirin Iskar Gas Na CNG Abin A Yaba Wa Shugaba Tinubu Ne -Shugaban IPMAN Na Ƙasa
  • Cacar Baki Ta Ɓarke Tsakanin el-Rufai Da APC Kan Tazarcen Tinubu A 2027
  • Sojoji sun kashe Kwamandan Boko Haram a Borno
  • Jarumar Kannywood Rahama Sadau ta yi aure
  • Soja ya soka wa ɗan sanda wuƙa har Lahira a Taraba
  • Sai Ƴan Siyasa Sun Haɗa Kansu Sannan Za Su Iya Tunkarar APC A 2027 – Lukman
  • Sojoji sun yi wa ’yan ta’adda ɓarin wuta a Borno
  • PDP ta gargaɗi ’ya’yanta kan goyon bayan Tinubu a zaɓen 2027
  • Tinubu zai kashe tiriliyan 1.5 wajen gina layin dogo na zamani a birnin Kano
  • Araqchi: Hari Kan Cibiyoyin Makamashin Nukiliyar Kasar Iran Ba Zai Taba Canza Matsayinta Ba