Nico Williams Ya Amince Da Komawa Barcelona Akan Kwantiragin Shekaru 6
Published: 20th, June 2025 GMT
Barcelona ta amince da yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan gaba na ƙungiyar Athletic Bilbao Nico Williams, amma kuma har yanzu akwai ƙalubalen da zasu fuskanta kafin ɗan wasan ya samu damar rattaba hannu a ƙungiyar ta Catalonia, ɗan wasan na ƙasar Sifaniya Williams, wanda ya zura ƙwallaye 31 a wasanni 167 da ya buga wa Bilbao, ya janyo hankalin ƙungiyoyin Arsenal da Bayern Munich a bana.
Amma ɗan wasan mai shekaru 22 ya amince da kwantiragin shekaru shida a Barcelona, wanda hakan zai sa ya hadu da abokinsa kuma abokin wasansa a matakin ƙasa Lamine Yamal a Nou Camp, Williams ya buƙaci Yamal da ya taimaka masa wajen zuwa Barcelona, bayan kakar da ya yi a Bilbao inda ya taimaka musu kai wa gasar zakarun Turai da kuma wasan kusa da na ƙarshe na gasar Europa duk a bana.
Yamal Ya Saka Hannu A Sabon Kwantiragin Shekaru 6 A Barcelona Diaz Ba Na Sayarwa Bane – Liverpool Ta Fadawa BarcelonaBarcelona ta yi yunƙurin ɗaukar ɗan wasan Liverpool Luis Diaz a farkon bazara amma sai Liverpool ta nuna cewa darajar ɗan ƙasar Colombian ta kai fam miliyan 80, hakan ya sa Barca ta janye daga cinikin, Williams yana da yarjejeniyar da ta kai Yuro miliyan 62 (£53m) a kwantiraginsa a San Mames, wanda Barcelona ta nuna cewa za ta iya biya.
Daraktan wasannin Barcelona Deco ya gana da Williams da wakilansa a Ibiza a farkon wannan makon, inda aka amince da yarjejeniya ta fatar baki, Williams ne ya fara zura ƙwallo a raga a wasan ƙarshe na kofin European Cup da suka doke Ingila da ci 2-1 a Berlin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: Barcelona a Barcelona
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Kano Ta Karɓi Rahoton Binciken Kwamishinan Sufuri Kan Belin Wanda Ake Zargi Da Safarar Kwayoyi
Gwamnatin Jihar Kano ta karɓi rahoton kwamitin bincike da aka kafa domin bincikar zargin da ake yi wa Kwamishinan Sufuri, Ibrahim Namadi, kan hannu da yake da shi a ceto wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Sulaiman Aminu Danwawu.
Shugaban kwamitin kuma mai bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Shari’a da Tsarin Mulki, Barrister Aminu Hussain, ne ya mika rahoton ga Sakataren Gwamnati na Jiha, Alhaji Umar Farouk Ibrahim.
Barrister Hussain ya bayyana cewa kwamitin ya gudanar da bincike bisa gaskiya da adalci, da kuma bin hujjoji, ba tare da son rai ba.
Ya bayyana cewa an gayyato Kwamishinan Sufuri domin karin bayani, inda ya kuma gabatar da rubutaccen jawabi ga kwamitin.
Sauran da aka tattauna da su sun hada da Abubakar Umar Sharada, Mataimaki na Musamman kan Wayar da Kan Jama’a, da kuma Musa Ado Tsamiya, Mataimaki na Musamman kan magudanan ruwa.
Don tabbatar da ingancin rahoton, kwamitin ya tuntubi hukumomin tsaro da shari’a kamar DSS, NDLEA da Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA). An kuma duba sahihan takardu da suka danganci lamarin tare da sharuddan doka da suka dace.
Barrister Hussain ya yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa kin tsoma baki da ya yi a lokacin gudanar da binciken, yana mai cewa hakan ya nuna irin shugabanci nagari da girmama tsarin doka.
Da yake karɓar rahoton, Sakataren Gwamnati ya nuna godiya kan yadda kwamitin ya gudanar da aikinsa bisa kwazo da kwarewa, duk da matsin lamba daga jama’a.
Ya jinjina musu kan jajircewa da tsayuwa akan gaskiya, tare da tabbatar da cewa za a mika rahoton ga Gwamna domin nazari da daukar matakin da ya dace.
Ya kara da cewa Gwamnatin Kano za ta duba cikakken rahoton tare da daukar matakan da suka dace bisa shawarar da kwamitin ya bayar.
Abdullahi Jalaluddeen