Mali ta ƙulla yarjejeniyar nukiliya da Rasha
Published: 24th, June 2025 GMT
Shugaban Mali, Assimi Goita da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, sun rattaba hannu kan yarjejeniyar makamashin nukiliya a fadar Kremlin da ke birnin Moscow.
Wannan dai na cikin wasu yarjejeniyoyi da Mali da Rasha suka rattaba hannu waɗanda aka tsaro domin inganta alaƙar kasuwanci da tattalin arziki.
Shugaba Vladimir Putin ya shaida wa shugaban kasar ta Afirka ta Yamma da ke ziyara cewa akwai wasu fannoni na musamman da za a iya ƙara haɗin kai.
Putin ya karbi bakuncin Kanal Assimi Goita a fadar Kremlin, inda suka tattauna tsawon awanni biyu, kamar yadda kafafen yaɗa labaran gwamnati na Rasha suka bayyana.
Putin ya ce dangantakar Rasha da Mali tana samun “kyakkyawan ci-gaba” duk da cewa cinikayyar ɓangarorin biyu a halin yanzu tana da “ƙaranci,” kamar yadda rahoton Kremlin ya nuna.
Daga cikin abin da yarjejeniyar ta ƙunsa akwai haɗin kai domin samar da makamashin nukiliya, kamar yadda Rashar ta bayyana.
Goita dai yana ƙara ƙulla alaƙa da Rasha ne bayan juyin mulkin da ya jagoranta a shekarar 2021, sannan ya juya wa Faransa — wadda ta raini ƙasarsu baya.
Da yake jawabi a ranar Litinin, Putin ya ce sun inganta yarjejeniyar ne, sannan suka tattaunawa hanyoyin da za su ƙara ƙulla alaƙa a “ɓangarorin ma’adinai da makamashi da agaji.”
Goita ya yi godiya ga Rasha bisa irin “karamcin” da aka masa, sannan ya nanata shirin Mali na ɗabbaƙa yarjejeniyar, waɗanda ya ce sun ƙunshi ɓangarori da dama.
Alaƙar tsaro dai na cikin muhimman abubuwan da ke tsakanin Rasha da Mali.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda kwacen babur da waya ya maye gurbin garkuwa da mutane a Birnin Gwari
Bayan kulla yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin tubabbun ’yan bindiga da jama’ar gari a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, mazauna yankin sun ce yanzu matsalar tsaron ta dauki sabon salo.
A watan Oktoban 2024 ne dai aka kulla yarjejeniyar sulhun tsakanin bangarorin biyu.
Yarjejeniyar na zuwa ne bayan shafe sama da shekara 10 ana fama da rikicin da ya mayar da babbar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari daya daga cikin mafiya hatsari a Najeriya.
Bai kamata ake bai wa ɓarayi muƙamin ministoci ba — Sarki Sanusi II Ma’aikatan gwamnati na amfani da kudaden sata wajen gina rukunin gidaje – EFCCDaga shekara ta 2015, mazauna yankin sun sha fama da hare-hare da garkuwa da su, yayin da matafiya kuma ala tilas suka koma neman rakiyar sojoji kafin su iya wuce hanyar.
Yanzu dai yankin ya fara samun saukin matsalar, yayin da mazauna yankunan suka fara komawa gidajensu manoma kuma suka ci gaba da noma gonakinsu.
To sai dai da alama yanzu a maimakon garkuwa da mutanen, rahotanni na cewa a yanzu ’yan bindigar sun fara yawo a gonaki suna kwace babura, wayoyi, kudade da ma kayan aikin gona daga hannun manoman yankin.
Mazauna kauyen Kuyello da ma wasu kauyukan sun ce yanzu suna zaman dardar.
Wasu daga cikinsu sun kyale gonakin gaba daya, wasu kuma sun ce yanzu sukan bar wayoyinsu a gida saboda tsoron za a iya yi musu fashi.
“Yanzu ’yan bindiga sun daina garkuwa da mutane, amma sun koma yi mana kwace. Yanzu suna yawo a gari hankalinsu kwance ba sa tsoron kowa,“ in ji wani mazaunin garin na Kuyello.
Hakan dai ya sake jefa tsoro a kan ingancin zaman sulhun da aka ce an yi.
Mazauna yankin dai sun yi korafin cewa babu wani yunkuri da ake yi na dakile tubabbun ’yan bindigar daga kwacen da suke yi, lamarin da ya sa suka ce suna tsoron sake komawa gidan jiya.
Bayanai dai na cewa yanzu matafiya na bin hanyar ta Kaduna zuwa Birnin Gwari, wacce babbar mahada ce tsakanin kudanci da arewacin Najeriya, ba tare da wata barazana ba.