Sin Da Kasashen Musulmi Za Su Kara Zurfafa Dangantakarsu
Published: 24th, June 2025 GMT
Majalisar ministocin harkokin waje ta kungiyar kasashen musulmi (OIC), ta gudanar da taronta na 51 daga ranar 21 zuwa 22 ga watan nan. Taron ya tabbatar da kokarin Sin na kare al’ummar musulmi tare da yaba wa ci gaban da aka samu na dangantaka tsakanin Sin da kasashen musulmi da kuma sa ran kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin kungiyar OIC da kasar Sin.
Da yake tsokaci kan hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Guo Jian kun, ya ce a ’yan shekarun nan, Sin da kasashen musulmi da ma kungiyar OIC, sun ci gaba da zurfafa aminci a tsakaninsu da fadada hadin gwiwarsu a bangarori daban-daban da karfafa musaya tsakanin al’ummominsu tare da samun kyawawan sakamako.
Ya ce Sin za ta ci gaba da hada hannu da kasashen da kungiyar OIC wajen raya dangantakar dake tsakaninsu. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
Cutar basir na daga cikin cututtukan da mutane da dama ke da mabanbantan ra’ayoyi akan ta.
A lokuta da dama za ka ji yadda mutane ke fadin dalilai daban daban da ke janyo cutar basir, yayin da wasu ke ganin yawan zama ne ke kawo ta, wasu kuwa gani suke yi zaki da maiko ne ke kawo ta.
Wannan shine abun da da yawa daga cikin mutane suka sani kan wannan cuta, sai dai masana kiwon lafiya na da nasu fahimtar daban kan wannan cuta.
NAJERIYA A YAU: Rashin aikin yi da hanyoyin magance su a Najeriya DAGA LARABA: Yadda ‘Yanbindiga Ke Amfani Da Hakar Zinare Wajen Mallakar MakamaiShirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai tattauna ne kan cutar basir da hanyoyin magance ta.
Domin sauke shirin, latsa nan