Zamfara Ta Zama Jiha Ta Farko Da Ta Ƙaddamar da Tsarin Ilimin Fasahar Zamani
Published: 20th, June 2025 GMT
A nasa jawabin, Gwamna Lawal ya bayyana tsarin a matsayin wani kwakkwaran taswirar zamani da za a sa a gaba tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na ganin an aiwatar da shi sosai.
Ya ci gaba da cewa, “A yau mun samu wani gagarumin ci gaba a tafiyarmu ta haɗin gwiwa a jihar Zamfara ta hanyar inganta fasahar zamani, ƙirƙire-ƙirƙire, da hanyoyin samun bayanai da fasahar sadarwa.
“Tsarin Ilimin Fasahar Zamani nna Zamfara wani tsari ne da zai amfani buƙatun al’umma na dogon lokaci don samar wa mutanenmu ƙarfin aiki da haɓaka ƙwarewarsu a cikin duniyar fasahar zamani.
“Kamar yadda muka sani, ilimin fasahar zamani yana da muhimmanci don samar da ayyukan yi da samar da ingantacciyar tsarin aiki. Ba zai yiwu mu rungume hannu mu bar jihar a baya ba a zamani ilimin fasahar zamani.
“Wannan tsarin yana da nufin samar da ilimi a bangaren fasahar zamani kan abubuwan da suma shafi – kwamfuta, ayyukan gwamnati, da kasuwanci. Tsarin yana dubi ga jihar da kowane ɗalibi zai ƙware sosai a fannin fasahar zamani, kowane ma’aikacin gwamnati zai samu fasahar zamani don gudanar da aikin sa, kuma manyan ‘yan kasuwa da ƙanana suna da ƙwarewar faɗaɗa kasuwancinsu. Mun fara shirin aiwatar da wannan hangen nesa.
“Jihar Zamfara ta haɗa gwiwa da Kamfanin Oracle domin horar da matasa 3,000 a shirin ‘Cloud 2 Computing, Artificial Intelligence, Data Science, and Database Management’. Tare da makarantar Oracle, manyan makarantunmu za su samu tallafi don yaye ɗalibai masu ƙwarewa a harkar masana’antu.
“An fara aiki a Cibiyar Fasahar Sadarwa ta Zamfara (ZIIT) da ke Gusau, wannan cibiya za ta kasance cibiyar ƙwararru ta yanki, da ke ba da ilimin kwamfuta da kuma samar da ƙirƙire-ƙirƙire a cikin gida. Muna da burin ganin mun ɗinke barakar fasahar zamani da kuma sanya Zamfara a matsayin cibiyar ilimin kwamfuta a Arewacin Nijeriya.”
Tun da farko, a jawabinsa na maraba sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Malam Abubakar Nakwada, ya bayyana ƙudirin gwamnatin jihar na ganin jihar Zamfara ta kasance kan gaba wajen kawo sauyi a bangaren fasahar zamani a Arewacin Nijeriya.
Da take isar da saƙon fatan alheri, Sanata Ikra Aliyu Bilbis (Sanata mai wakiltar Zamfara ta tsakiya), Shugabar Kwamitin Fasahar Zamani da Tattalin Arziki na Majalisar Dattawa, ta yaba wa Zamfara kan yadda take kan gaba a lokacin da ci gaban ƙasa ya ta’allaka kan fasahar zamani. Sanatar ta ba da gudunmawar kwamfutoci 300 ga ZITDA don tallafa wa tsarin fasahar zamani a duk faɗin jihar.
A jawabinsa dangane da Tsarin Ilimin Fasahar Zamani na Zamfara (ZDLF), Dokta Habib Gajam, Babban Sakatare na Hukumar Bunƙasa Fasahar Watsa Labarai ta Zamfara (ZITDA), ya bayyana tsarin a matsayin wata dabarar da ta shafi mutane da aka tsara.
Muhimman cibiyoyi na fasahar zamani na Gwamnatin Tarayya da aka wakilta a taron masu ruwa da tsakin sun haɗa da Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC), Galaxy Backbone, Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA), Cibiyar Kuka da Tauraron Ɗan Adam, da Hukumar Kare Bayanai ta Nijeriya (NDPC).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: ilimin fasahar zamani Fasahar Zamani jihar Zamfara
এছাড়াও পড়ুন:
Wani Dan Siyasa Ya Shirya Addu’o’i Na Musamman Domin Samun Zaman Lafiya A Zamfara
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta tarayya Kabiru Amadu (wanda aka fi sani da Mai Palace) ya shirya taron addu’a na musamman ga jihar Zamfara da Najeriya baki daya, domin neman zaman lafiya da cigaba mai dorewa.
Taron addu’o’in wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a na Tudun Wada da ke Gusau, ya hada malaman addinin Musulunci, da sarakunan gargajiya, da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, da kuma daruruwan al’ummar jihar baki daya, duk sun ba da hadin kai wajen ganin an samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.
A nasa jawabin, Kabiru Mai Palace, ya bayyana taron a matsayin wani shiri na ruhi da nufin neman taimakon Allah wajen magance matsalar rashin tsaro da zamantakewar al’umma da ke addabar Zamfara da sauran sassan kasar nan.
Ya kara da cewa, idan aka ajiye siyasa a gefe, kowane dan majalisa daga jihar Zamfara yana yin kokari na gaske don ganin an magance rikicin.
Manyan Malaman addinin Musulunci daga sassa daban-daban na jihar ne suka jagoranci addu’o’i na musamman, da karatuttukan Alkur’ani mai girma, tare da gabatar da addu’o’in neman zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban Zamfara da Najeriya baki daya.
Sun kuma yi addu’ar Allah ya baiwa shugabanni a dukkan matakai da hikima da jagoranci.
Babban Limamin Masallacin Juma’a na Tudun Wada, wanda ya jagoranci zaman addu’ar, ya bayyana muhimmancin Ikhlasi, Adalci, da kokarin hadin gwiwa wajen ganin an samu dawwamammen zaman lafiya.
Sauran sun bukaci al’umma da su rungumi afuwa, hakuri, da hadin kai, tare da jaddada cewa zaman lafiya da tsaro yana farawa ne daga jama’a da kansu.
Mahalarta taron sun nuna jin dadinsu ga Alhaji Kabiru Amadu bisa kaddamar da taron addu’ar, inda suka bayyana shi a matsayin wanda ya dace kuma a yaba masa.
Shima da yake jawabi a wajen taron, mai martaba Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad ya yi kira ga sauran ‘yan majalisar tarayya da su yi koyi da irin wannan kokari da Mai Palace ya yi, yana mai cewa sa hannun Allah shi ne ginshikin magance matsalar tsaro a jihar.
An kammala taron addu’o’in ne da yin kira ga al’umma baki daya da su bayar da gudunmawarsu wajen ganin an dawo da zaman lafiya da zaman lafiya da adalci a jihar Zamfara da Najeriya baki daya.
AMINU DALHATU